← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 166

Sashe 81

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Har suka isa makarantar, Abuturrab bae ce ma Batuul komae ba ita ma window kawae take kallo abun ta, sae da yyi parking sannan ta dauki jakarta dake kafarta xata fita yace "Ki na da hankali kuwa, wa ya baki izinin fita" komawa tayi ta xauna ta jinginar da kanta jikin kujerar da take xaune, kallonta kawae yake, ita kam bata ma san yana yi ba, ya wani daure fuska yace "Kin yi breakfast ma kuwa" ba tare da ta kallesa ba tace "Na sha tea" a d'an tsawa ce yace "Hey look at me!" Juyawa tayi tana kallonsa yace "Yaushe na fara wasa da ke xaki wani dinga dauke min kai ina magana" tagumi tayi tana kallonsa ko kifta wa bata yi, dariya ta basa ganin yanda ta tsuke baki, yace "Ayt, naga alama don kin ga na fara bi ta kan ki ne ynxu, ina kare ki gun matata shi yasa kike son ki raina ni koh?" Ita dae bata ce komae ba kuma bata fasa kallonsa ba, kayan jikinta ya kalla da d'an karamin bakin gyalen da tayi rolling a kai yace "Wae ma kina matar aure xaki dinga irin wannan shigar kina xuwa makaranta kina da hankali kuwa" kallonsa take har lkcn kuma bata ce komae ba, kafin ya kara cewa komae ta kalli agogon wrist dinta tace "Its almost time for lecture" tana fadin hka ta dauki jakarta ta bude motar ta fice, bin ta yyi da kallo cike da mamakin ta, bae san lkcn da yyi murmushi yana shafa kansa ba, kamar wanda ya tuna abu ya bude motar ya fita ya kulle sannan ya bi bayanta, tafiya take kamar me tausayin kasa tana rataye da jakarta, ko kai ka ganta sae ta burge ka don a nutse take tafiyar, kamar ance ta waiga taga yana biye da ita a baya, ae bata san lkcn da ta tsaya ba gabanta na faduwa sosai, ya karaso ya xaga gabanta yana facing dinta, sunkuyar da kai tayi, yana mata wani irin kallo yace "Are yhu stupid? Yhu walked me out ina maki magana?" K'in cewa komae tayi, ya gyada kai yace "Gud nasan maganin ki?" Kudi ya ciro aljihunsa ya mika mata ba musu ta risina ta karba murya can kasa tace "Thank yhu" wayarsa ya mika mata fuskarsa daure yace "driver xae kira ki" ta karba tace "Toh" tafiya yayi ya bar ta nan tsaye ta bi sa da kallo snn ta ci gaba da tafiyarta ita ma, sae taji for the first Abuturrab ya burgeta, "Upon all, he is kind at heart kmr yanda farida ta gaya mata, he always care and show concern" murmushi tayi ta karasa Dept da sauri ganin few minute ya rage a fara lecture.

Karfe sha biyu saura suka fito daga lecture, Batuul tace "Lets get something to eat frnd am hungry" Aisha tace "It's ok, same with me here" suna tafe ne bbu me cewa komae cikinsu har suka iso wani guri da Shaheed ke xaune da abokansa kusan su biyar, biyu bakake kmr sa uku kuma turawa, hiran su kawae suke shi kuma yana duba wani textbook dake hannunsa" Batuul ta hade rae ganin yanda suke kallonsu tun kan ma su karaso, suna Karasowa wani dake xaune gefen Shaheed yace "Hey Aysha!" Aysha ta tsaya tana murmushi tace "Hei Usman how you, how's lecture?" Usman yace "Alhmdllh, dat gal! Is she ur frnd? So haughty of her!" Sae a sannan Shaheed ya d'aga kai yana kallonsu, Batuul ya bi da kallo don ko tsayawa bata yi ba ta ci gaba da tafiyarta, ya lumshe ido ya bude ya ci gaba da karatunsa, Aysha tayi dariya tace "No, no, not at all, she's not! just dat ba ku saba bane, Well! We'll chat later Usman, bye for now" yace "Ayt! Take care of ur self bae" dariya tayi ta bi bayan Batuul da sauri. Xaune ta sameta waiter dake aiki a wajen yana tsaye kusa da ita yana tambayar me xae kawo mata, tace "Just caramel bun and frapuccino" mutumin ya juya yana kallon Aysha yace "yhu ma'am?" Tace "Same also!" Juyawa yayi ya tafi kawo masu. Aysha tace "Shine kika tafi kika bar ni koh?" Batuul ta kalleta murmushi dauke fuskarta tace "Yea naga yhu were busy ne" Aysha tace "Ayt, amma ko gaisawa ne ki dinga yi da mutane don ku saba mana" Batuul bata ce komae ba sae juya wayar Abuturrab dake hannunta take, Aysha ta ce "Kawo in sa maki digit dina, it's gud ace mun yi exchanging" mika mata wayar Batuul tayi ta karba ta kunna, "Woaww is this ur sister on the screen, kai she's so beautiful wallahi, ya aka yi ke baki yi hasken ta ba" hade rae Batuul tayi ba tare da tasan ta ma yi hakan ba, don ko lura da hoton screen din ma bata yi ba kawae ta fito da wayar daga jaka ne don ta duba agogo, Aysha bata damu da shirun da Batuul tayi mata ba tayi ta koda kyan Ajiddeh, daga karshe ta sa mata nmbrta tayi mata saving ta mika mata, Batuul na karban wayar ta maida jakarta snn ta maida hankalinta kan abincin da aka dire masu gabansu, ta riga Aysha gamawa snn ta fiddo wayar don hoton ya tsaya mata a rai haka kawae, kare ma hoton kallo kawae take, bata san lkcn da ta ja tsaki ba Aysha ta kalleta tace "Ya dae" yake tayi tace "Naga time ya wuce ne, baxa kiyi sllh ba?" Aysha tace "No bana yi" Batuul bata ce komae ba ta shiga gallery duk tayi mark din hotunan Ajiddeh dake wayar har na screen din ta watsa su a kwandon delete. Tana gama hakan ta ja tsaki ta fiddo kudi jakarta tace "Tambayar mana bill Aysha" ita ta biya kudin duk yanda Aysha ta so biya bata yrda ba, suka mike don komawa Dept.
Chapter 81 · 0% Book details