Sashe 154
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Binsu yayi a baya zuwa d'akin da aka shigar da Batuul d'in, daidai bakin k'ofa wata nurse tace "We are sorry Sir, but you can't get in", wani irin kallo ya jefeta dashi da yake mata nuni da bakida hankali ko, da sauri ta sauk'e idonta k'asa tana cewa "am sorry sir", hannu yasa ya matsar da ita gefe ya tura k'ofar shiga d'akin, kan gado ya tarar da Batuul kwance har an bata maternity wear, sun fito da duk wani abu da ake buk'ata, da sauri ya k'arasa gadon da take kwancen, ido kawai ta rintse tana ambaton sunan Allah dan yau hawayen ma nemanshi take ta rasa, dukda azabar da take sha hakan bai hanata jin d'umin hannunshi cikin nata ba, a wahalce ta bud'e idanunta ta sauk'e cikin nashi, ido ya lumshe ya bud'e, bayason ganin wannan yanayi da take ciki, a hankali tace "Yaa Abu Aunty", kamar wacce ta watsa ruwa haka sweat duk ya jik'ata, hannunta dake cikin nashi ya riqe ya kai bakinshi tareda kissing yace "You will be fine Babyna, we will make it together, am here kinji?", ido ta lumshe tana kad'a kai cikeda azaba tace "inaso inga Aunty, plss call her for me kaji Yaa Abu, inaso in ganta", ta fad'a tana sake cije leb'e, gaba d'aya ta gama rikitashi, shima so yake kawai yaga hawaye ya zubo mishi ko zaiji dad'i da wannan irin ciwon da yake jimata, daidai fuskarta ya sunkuyo yace "Glitter you will b okay, Aunty will be here anytime,Ammah zata fad'awa Aunty, am upright sure, she will b here shortly, sannu kinji?", daidai lokacin da doctor da nurses d'in suka k'araso cikin shirin aikinsu, ganin Abu zaune Doctor yasa yace "Good Afternoon Mr Kyaree, we are sorry but we need you to stay outside to carry out our work efficiently", fiyeda kallon da yayiwa Nurse d'in d'azu yayiwa Doctor dukda sabon dake tsakaninsu amma yau mantawa yayi da hakan, gaba d'aya ranshi ya gama b'aci, matarshi in such a pain maimakon yayi attending to her yake kawo masa shirmen banza wai ya fita, a fusace yace "Get yourself composed Doctor and attend to my wife, She is my wife, we are in this together, I ain't moving an inch from here", ya sake maimatawa sternly snn yace "And if anything happens to her?, am gonna shut d whole hospital down, you will all pay for it", yayi maganan idonshi na kad'awa, "Damn it, Doctorrr", ya fad'a kamar zai make doctor, ganin dagaske yake kuma zai b'ata musu lokaci yasa kawai suka fad'a aikinsu cikeda k'warewa, duk wani kuka na Batuul yau nemanshi tayi ta rasa, Addu'o'in da Abu keyi yana tofa mata duk wanda ta kama shi takeyi, da taji azaba lokacin take tuna Aunty, take zata fara Rabbir Ham huma kama rabbayani Sagira, duk wani motsi da Batuul zatayi har cikin ranshi Abu ke jinshi, sosai ya tausaya mata ganin irin wahalan da take sha, a lokacin ya sake ganin kima da daraja irin ta mata had'e da tausayinsu, in basu ba wazai iya enduring irin wannan ciwon, addu'a yayiwa duk wata mace wacce aka haifa da wacce ta haifa, a hankali ya fara tofa mata "wa tilka hujjatuna atainaha Ibraheema ata qaumihi, narfa'u darajatin man nasha, inna rabbaka hakeemun aleem", a zuci ta dunga maimaita aabinda taji yana fad'i, a hankali taji ciwon na raguwa, ba a cika one hour ba ta sumb'ulo y'ar Babynta k'arama mai kyau itama, Hamdala Abu yayi yana kai hannu zai tab'a Babyn Doctor yace Mishi "No pls, not now", yatsina fuska yayi ya janye hannunshi, tareda shi suka taimaka aka gyara aka kimtsa Batuul da Baby, bayan an fito da Babyn yana zaune bakin gadon da Batuul ke kwance yana mata sannu suka mik'o musu Babyn, da Bismillah yasa hannu ya karb'eta daga wajen nurse, gaba d'aya komai na jikinta farine, babu komai nata a waje sai d'an k'aramin face d'inta, wani irin k'auna da nutsuwa da baisan daga inda yake sauk'o mishi ba yakeji jin d'umin Babyn jikinshi, murmushi ne ya kufce Mishi ganin komai na fuskan Babyn irin nashi, lips d'inta ne Kad'ai irin na Batuul hatta heart shape d'in bottom lip d'in nata irin na Batuul ne, a hankali ya matso da Babyn kusa da Fuskan Batuul yace "Fatima our child, our Baby, kyautar da Allah yayi mana Fatima, look at her please, she is too cute for me", murmushi kawai Batuul tayi dan bata jin k'arfin jikin nata sosai, daidai kunnen Babyn ya sunkuya tareda k'ira mata Sallah, ya karanto "inni sammaituha (A'eesha) wa inni u'ixuha bika wa xurriyatiha minash shaaid'anir rajim" yayi mata addu'o'i sosai tareda yi mata Hud'uba da Suna A'eesha, Dabinon Ajwan da dama yana cikin kayansu yasa aka mik'o mishi da ruwan Zamzam ya tauna ya d'iga mata tareda ruwan Zamzam d'in, kamar wacce tasan abinda akeyi ta yatsina fuskarta tana lashe baki, dariya yayi ya sunkuya yayi kissing goshinta snn ya matsa jikin Batuul d'in yace "Glitter?", a hankali ta d'ago lumsassun idanunta ta dubeshi, yace "kin bani kyautar da duk duniya babu mai bani irinta, you have given me the best gift I would ever ask off, I will forever be grateful, Allah ya barmin keh Glitter kici gaba da bani wasu Babies d'in, just tell me anything you want, ko meye shi indai akwai shi a nan duniyan, I promise to get it for you, you have given me the best gift of life, I promise you, just ask me duk abinda kikeso zanyi miki shi, just tell me jinni", a hankali ta bud'e idanunta da suke a lumshe, kallonshi takeyi da murmudhi d'auke kan fuskarta tana tunanin abinda takeson cewan, tasan duk murna ne ya cikashi amma da wuya ta samu abinda takeson, a hankali ta bud'e baki tace "You Promise?", kallonta yayi for seconds kamin ya kad'a mata kai, zai yi magana doctors da nurses d'in suka zo za a canja mata d'aki, tana kwanace suka turata zuwa wani d'akin, badan ta saba da ireirensu ba da zatace d'aki ne kawai ba na asibiti sbd girma da kuma kyansu, saida Nurses d'in suka gama duk wani necessary abu da ya kamata suyi mata itada Babyn snn suka kwantar da Babyn gaban Batuul suka fita suna mata sannu, kallonsu yayi with so much adoration yana yiwa Allah godiya da kyautan nan da Allah yayi mishi, Batuul is one part of him da baya tunanin zai iya rayuwa babu ita, hannunshi yasa ya kamo na Batuul d'in yana d'an murzawa a hankali yace "Fatima you are the best thing that ever happened to me kinsan da haka ko?", a hankali ta kad'a mishi kai yaci "I know I love, ban san amfanin kud'ina ba if I can't give you abinda kike nema, komeye shi kike so indai bai sab'awa addini back just mention the anything, zanyi miki shi Glitter", ya fad'a yana sassauta muryarshi tareda sak'ale yatsunsu waje d'aya, a hankali ta bud'e baki tace "Yaa Abu ka dawo Ajiddeh gidanka, zamanta haka ya isa batareda sanin makomarta ba, banasone ka shiga hakkinta, na fad'a maka nikam na yafe mata wlhy, nobody is above mistake, kuma everything happens for a reason, maybe for us to realise each others worth, how much we mean to each other, Yaa Abu plssssss", ta k'arasa maganan tana lumshe ido , shi kad'ai yasan irin impact d'in da Batuul ta yiwa rayuwanshi, mesa baza ta fad'i wani abin ba sai wannan, har ga Allah ko jiya da Abui ya sake mishi zancen Ajiddeh聽 ce mishi yayi zai rabu da ita, zai sallameta, duk da ya yafe mata shima amma ya kasa samun wajen da zai ajiye abinda ta aikata ya manta dashi, baya tunanin zai iya d'aukan wani abin da zai sami family d'inshi ya qyale maishi nan gaba, amma its about Batuul yanzu, she is worth more than that, He can sacrifice that atom of happiness da ya rage mishi for her to be happy, tana son ya maida Ajiddeh d'akinta, kuma alk'awari yayi mata akan ta fad'i abinda takeso, how can he just deny her , a hankali ya sauk'ar da idonshi kan fuskan Batuul ya shafi gefen fuskarta da d'aya hannun nashi yace "will that make you happy?", kai ta kad'a mishi, murmushi yayi mata yace "Anything for you Fatima, just know I will always love you", murmushin ta mishi amma jin yanayin da yake聽 sab'ule hannunshi cikin nata yasa murmushin dake fuskarta bajewa, duk da rashin k'arfin da takeji hakan bai hanata damqe hannunshi ba, kallonta yayi, ganin hawaye idonta yasashi zama da wuri yana girgiza mata kai, cikin siririyar muryarta tace "Are you sad, angry about what I requested for?, ka bari na fasa if you are not okay with .....", bai bari ta k'arasa ba ya d'aura dogayen yatsunshi kan lips d'inta yace "Shhhh, am happy with whatever that makes you happy, okay?", kai ta kad'a mishi yayi murmushi yace "Good girl, get some rest", ya fad'a yana d'aga mata girarshi d'aya, murmushin tayi mishi itama tareda lumshe ido, ido ya tsura musu itada y'ar Babyn dake gabanshi yana kallonsu yana dad'a yiwa Allah godiya da ya bashi wad'annan precious kyautan a rayuwanshi, yana nan zaune yana kallonsu aka turo k'ofar d'akin, Abui ne sai Ammah, Farida sai Sadiq, lokacin doctors suka sanar dasu da Batuul ta sauk'a lafiya zasu iya shiga su kanta, tsabar murna Farida har rawa jikinta keyi sbd d'okin zuwa taga niece d'inta, y'ar yayanta y'ar Bestyn ta that turn out to be a sister, Abui ne ya fara d'aukan Babyn da murmushi a fuskanshi yana tuna lokacin da ya fara riqe Abu for the first, yace "This is how I held Aliyu , kamar jiya fa gashi yanzu Allah ya bani tsawon rai nayi witnessing haihuwar y'arshi, Allah yayi muku albarka baki d'ayanku", ya fad'a tareda kissing goshin yarinyar, duk suka amsa da "Amin", Ammah ce ta karb'eta daga hannun hannun Abui murmushi d'auke fuskanta snn ta kalli Batuul dake kwance tana bacci tace "Allasarki Bitti, yadda kukaga wannan jaririyar haka Fatima take lokacin da aka haifota, tun ranan Allah ya dasa min sonta a raina kamar ni na haifeta, ashe itace zata fara samar min jika, Allah ya k'ara miki