← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 166

Sashe 66

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abuturrab kam na daki kan system wayarsa ta hau kara, dauka yyi ganin Ammah yasa shi saurin d'agawa da sallama, Ammah tace "Abu kun isa lafiya, shine ba kira?" Yyi k'asa da kai yace "Kiyi hkuri Amnah ynxu nake da niyar kiran ki, gajiya ne yasa hka", Ammah tace "Shknn Babana, ina Ajiddehn, kun sameta lafiya", yace "Alhamdulillah Ammah she is doing good", tace "toh Abu, bazan gaji da yi maka Nasiha ba, ka kula dasu ka zauna tsakaninka da Allah dasu, Allah zai tayaka rik'on indai niyyanka is pure, sannan Fatima yarinyace k'arama, hankali bai gama game ta ba, in ka cuceta akan matarka, toh Allah sai yayi mata sakayya, kaji tsoron Allah Abu, kuma makaranta Abui yasa Sadiq ya turo maka, in ka duba kaje kayi mata necessary abubuwan da duk ya kamata" sai da yaji tayi shiru tukunna yace "In sha Allah Ammah nagode, Allah ya k'ara nisan kwana", ta amsa da "Amin, Allah yayi muku albarka, bata wayan inyi magana da ita", yace "Ammah tana 膹akinta, sai dai in kai mata", tace kai mata ina jira", yace " Toh xan kira ki" daga hka ya katse wayar ya fita yayi hanyan 膹akinta, ganin bata ciki yasa ya sakko falo, tsayawa yyi daga stairs hango Ajiddeh da yyi tsaye kofar kitchen din don yasan ba arxiki ya kai ta ba, Karasowa yyi Ajiddeh na hango sa tayi tsit daga cin fuskar da take ma Batuul cike da faduwar gaba, shiga kitchen din yyi yana kallon Batuul dake durkushe har lkcn a kitchen din tana kuka, Ajiddeh ta juya ta bar bakin kofar da sauri ya bi ta da kallo, murmushi yyi yana kallon Batuul dake kuka kmr xata shide yace "Yhu see! Kinga abinda nake guje maki knn, kika rufe ido kika ce sae ni, don hka yhu have to endure duk me xa ki fuskanta daga matata tunda kika ce kin ji kin gani...." kallonshi tayi da idonta da yyi jajir ta mike da kyar ta fice daga kitchen din hawaye na bin kuncinta, murmushi ya shiga yi yana jujjuya wayar hannunsa, wayar ya fara ring, sae a snn ya tuna abinda ya sakko da shi, xaro ido yyi ya bar kitchen din da sayri ya hau sama ya nufi dakinta, kwance ya sameta tana kuka ssae, ya karasa gadon ya xauna yana kallonta yace "Wae kukan me kike ma mutane hka daga an gaya maki gskya" kin cewa komae tayi, ya kalli wayar hannunsa jin ya katse, yasan Ammah ba hakura xata yi ba, sake bugowa tayi, ya ajiye wayar ya dago Batuul ya daura hannu kan kafadarta ya runtse ido yace "Alryt! Kiyi hkuri" ko kallonsa bata yi ba kuma bata daina kukan da take ba, a tsawace yace "Nace kiyi hkuri" ae sae ta kuma fashewa da kuka, rungumeta yyi ba tare da yyi wani tunani ba, yana patting bayanta a hnkli kmr me rada yace "Am.. am srry" ita kanta ta rasa dalilin da yasa ta tsaida kukan nata sae ajiyar xuciya da take saukewa, tana jikinsa ya jawo wayar da har ya katse, sae ga shi Ammah ta kuma kira, d'agawa Ammah tayi cikin fada tace "Walakanci ne hka Abuu?" Yace "Kiyi hkuri Ammah tana bayi ne, gata" kara wayar yyi a kunnenta yana rungume da ita, jin muryan Ammah yasa hawaye sake gangarowa a hnkli cikin sanyin murya tace "Ammah ina wuni", Ammah tace "Lafiya lau Bitti, ya gajiya, duk gajiyan ne naji muryar ki hka", kallon fuskarta Abuturrab ke yi kawae, tana sharen hawayenta tace "Alhamdulillah Ammah, babu gajiya ya su Abui da Farida", Ammah tace "suna lafiya Bitti, babu dai matsala ko", kai ta 膹aga tana kallon Abu da suna ha膹a ido ya kuma mannata jikinsa, jiki a sanyaye tace "Ehh Ammah babu komai", Ammah tace "haka nake son ji dama, kiyi hak'uri sosai kinji Bitti, sai kiga komai yazo miki da sauk'i, makarantarki ma soon zaki fara zuwa kinji, ki manta da komai kiyi abunda ya kaiki, as i told you, don't hesitate in telling me your problems kinji, koh na meye", kai ta gya膹a kamar Ammahn na ganinta hawaye na xubo mata tace "Toh Ammah zanyi nagode", tace "Yawwa Bitti", daga haka ta mik'awa Abu wayan, ji tayi yace "Yeah gobe Monday zamuje a gama processing komai, sai Anjima Ammah mun gode", ita kam Batuul bata 膹ago ta kalleshi ba sae kkrin janye jikinta daga nasa da ta shiga yi amma ya ki saketa, cikin kakkausar murya yace "Wae ma kukan mey kike yi ma mutane daga an fada maki gskya,", sake fashe mishi tayi da sabon kukan takaici, lumshe ido yyi yana murmushi, lkci daya ya bude ido ya dafa kafa膹unta yace "okay naga alamar kina son hada ni da Ammah ne, today shud b the last time da xa ki min kuka a gidana, its not going to b good for you idan na sake ganin kin yi hka, ba gidan ku bne nn, tunda kika zab'i aurena yhu have to endure everything yhu will come across" Shiru Batuul tayi tana saurarensa, duk taji yace ita ta xabi aurensa sae ranta ya baci, ido yabi fuskanta dake jik'e da hawaye, 膹an k'aramin lips 膹inta ya koma ja, yace "clean your face and hear me out", a hankali tasa hannnu tana goge hawayen, sai da ta gama yace "nasan dai kinsan zancen komawanki makaranta, gobe zakije a fara komai, it doesnt mean komawanki makaranta zaisa kiyi min yawo a gida ba, am not tolerating that, sannan babu ruwanki da matata inba girmamawa ba i cant take duk wani raini da zakiyi mata, ban yadda ki rainata ba, sannan ban yadda da tarkacen k'awaye ba, not in my house, abinda ya kaiki shi zakiyi ki dawo, inma zakiyi toh ya tsaya daga can makaranta, in kuma baki yadda da all i said ba, try me and see what will happen", har sai da taji yayi shiru tukunna ta janye daga rikon da yyi ma kafadunta tace "ai dama nasan you are always against my happiness, you snatched it all away from me, kuma da kake cewa kar in raina matarka ai nima duk sunanmu 膹aya da ita, am also your wife kammar yadda kace an lik'a maka ni, and as it is, zan 膹auki komai daga wajenka but not from her ka ja mata kunne bbu ruwanta da ni, kar ta kuma involving iyayena a abunta yawo kuma ba halina bane, k'awaye kuma, nobody can live in isolation, ba kowa na sani ba,", cikin k'arfin hali tayi duka wannan maganganun dan idonta rufe tayi duka wannan maganan, chest 膹inta sai heaving yake, tsaf ya gama kalleta yana kallon yadda zuciyanta ke bugawa, dariya ta kusa bashi, a hankali ta bu膹e idonta, cikin hanzari ta tashi zata gudu dan sai yanzu maganganun da tayi suke dawo mata, hannu yasa ya fincikota jikinshi, a tsorace tace "Ni ja kyaleni xan hada ja da Ammah" sake janyota yayi jikinshi daidai kunnenta ya sunkuyo yace "fine if thats what you actually said, just try me and see", jin sauk'ar numfashinshi a wuyanta yasa duk tsigar jikinta tashi, kan gadon ya jefata ya juya xae fita daga 膹akin, daidai bakin k'ofa yana fitowa suka ci karo da Ajiddeh ta shiga masa wani kallo, bai ce mata komai ba yayi tafiyarshi, da ido tabi k'ofan 膹akin sannan tabi bayanshi da ido, hankali tashe tayi hanyan 膹akinshi itama, ae ko baxa ta yi tolerating wnn ba.
[8/22, 2:13 PM] .: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

46

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

A hargitse ta tura k'ofan 膹akin, yana kwance kan gado ya lumshe ido kamar ba shine ya shigo yanxun ba, dai dai kanshi tazo ta tsaya tana huci, ranta b'ace har wani gumi takeyi ta shiga yi masa magana, "Aliyu nifa bazan yadda da wannan abinda kuka tsira ba, wlhy ni bazan yadda da zamanta ba a cikin gidan nan, inma kai baza ka iya fa膹awa iyayenta baka son zamanta gidanka ba sai ka kama mata hostel 膹in da kanka kawae, amma ba dai tayi ta zama min a gida ba dan dama nasan munafirci ya kawota", sai da yaji tayi shiru tukunna ya bu膹e lumsassun idanunshi dake rikitata yace "tunda gidanki ne sai ki koreta", ido ta wara tana kallonshi hawaye na bin kuncinta, cikin rashin damuwa da hawayen nata yaci gaba da cewa "tsabar rashin hankali da rashin sanin ciwon kai shine ki kaje kika tsareta a kitchen kina gaya mata maganganu koh, toh duk kika yrda ta raina ki baxa ki ji da dadi ba kuma bbu ruwana baxan kuma ce mata don me ba ", hankalinta ne ya k'ara tashi wai yau ita Abu ke k'ira mara hankali akan wata can y'ar iskar, wlhy Allah sai tasan yadda tayi da Batuul, sai ta wulak'anta ta fiyeda tunaninta, k'wafa tayi ta juya a fusace ta banko mishi k'ofar 膹akin a xuciyarta tana cewa xaka rashin hankali kuwa, tabe baki yyi ya sake lumshe idanunshi ya gyara kwanciya yana shak'ar k'amshin Batuul da ya mannne mishi a kaya da yayi hugging 膹inta.
Chapter 66 · 0% Book details