← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 166

Sashe 130

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Mum a can gida duk hankalinta a tashe ta rasa da wanne zata fara, mijin Jainaba dake shirin tozartasu ko kuma Ajiddeh dake kunsa mata bakin ciki tana son jawo mata attack, ga wata munafika da Dad ya dawo gida da wai accident sukayi amma yanzu ita duk ba ta tasu takeyi ba, so take ta fara magance Jainaba da Ajiddeh tukunna inyaso asan abin yi kan buzuwar da ya kawo mata gida, bayan sun gama waya da Ajiddeh ta jefa wayarta cikin Jaka ta fito ta sami driver ta fad'a mishi inda zai kaita, gidan su Abu tace mishi tanaso, umarni yabi har saida sukazo gidan ta fita tace ya jirata ba jimawa zatayi ba, baki ta sake tana karewa gidan kallo, duk kallonta da manyan gidaje hadaddu wannan daban yake, a ranta kuwa cewa tayi "Shine waccan sallamamiyar take son janyo mata asara, irin wannan daula sai sun kwashi rabonsu ai", har ta shigo cikin gidan sake sake takeyi cikin ranta, Da Ammah suka fara cin karo, rikicewa tayi ganin Ammah amma ta dake ta kirkiro murmushi tace "Hajiya Bilki kin ganni da sammako ko, wlhy abubuwane nayi dayawa gashi Ajiddeh tace min satinsu d'aya yar uwarta bataji dad'i ba shine nazo dubata, in banyi sammakon bane bazan samu time ba", Ammah tsabar mamaki kasa magana tayi, mamaki fal ranta kuma hankalinta sam bai kwanta da zuwan Mum ba, dakewa tayi tace "Alhamdulillah mai jikin ma ta fara jin sauki, Allah bada lada", Mum ta tab'e baki tace "ko ba sauki ba, saukinta d'aya ai mutuwa", amma a fili tayi murmushi tace "Allasarki baiwar Allah, tasha wuya Allah yasa kaffara ne", Mum dai ce mata tayi "Amin", snn tace "Hauwa na sama ko, kamin kiga mai jinyar", Mum tace "Ahh toh shikenan, ba jimawa zanyi ba", Mum ta kira d'aya daga cikin masu aikin gidan tace ta kaita d'akin da Abu yake snn tace a kai musu refreshments can sama, saida sukayi gaba tayi inda aka kwantar da Batuul take bacci, lokacin babu Sadiq da Farida da kuma masu yi mata sauk'an sun fita, Asheikh ta tarar yana magana yace" Hajiya keh muke jira dama, Alhamdulillah yarinya ta samu lafiya kuma kamar yanda muka fad'i sihiri akayi mata snn Allah cikin ikonshi ya bayyana mana wad'anda sukayishi", dafe k'irji Ammah tayi tace "Innalillahi wa inna illaihi raji'un", Abui ya kad'a yace "La hawla wala quwata illa billahi aliyul azim, Subhanallah", Abu dai kai kawai ya d'ago yana jiran jin karashen bayani, Ammah tace "Allah ya kyauta, yarinyar nan bana tunanin tana da matsala da mutane", Asheikh ya d'anyi murmushi yace "Ai yanzu ba sai kayiwa mutum komai ba zaiso ganin bayanka", Ammah ta sauk'e ajiyar zuciya tace "Allah ya kyauta", Abu duk ya k'osa yaji wad'anda suka sa Batuul cikin wahala, har wani zafi ranshi keyi dan shi kad'ai yasan abinda zaiyi musu, sai yasa sun d'and'ani azaba fiyeda yadda suka sa Batuul ko su din su wayene kuwa yace "Asheikh munaji, zamu iya sanin sunayensu?", Asheikh yace "Ehh kaga wannan abinda ta amayo shi ya nuna mana ko su waye su, dama shi irin wannan sihiri mugune, sosai yake lahanta mutun dan bama sihirine na haka ba, yarbawa sunfi yinshi , ba kowa ke iya juresa ba, in har aka yiwa mutum shi toh indai maishi ya mutu, ko ba dade ko ba jima sai ya koma kan wanda yayi shi, inko bai mutu ba, a irin haka duk abinda ya fito jikinsu toh da sunayensu zai fito kamar yadda nata yayi", Abu dake tsaye kai kawai ya dafe dan ya fara losing cool d'inshi, baya tunanin inyaji sunayensu zasu k'ara minti talatin ba a prison ba, cikin tunanishi kamar daga sama yaji ana ambaton, "Zuwaira, Jainaba da Ajiddeh", da sauri ya d'ago dan gaskata abinda yakeji, wani irin nauyi yaji kanshi yayi mishi kamar an d'aura mishi dutse, bai ankara ba sai ji yayi hawaye na bin kuncinshi, kai ya shiga girgizawa yana matsawa da baya, if his memory still serves him right sunan matarsa Ajiddeh yaji daga bakin sheikh itada iyayenta, jirine yaji yana neman d'ibanshi da sauri ya samu bango ya dafa, Ammah da ta tsaya itama da mamaki tayi hanzarin rik'oshi ganin zai fad'i, banda ance Azzanu zambin, zato zunubine amma hankalinta Sam bai kwanta dasu Ajiddeh ba, ido ya lumshe ido ya bud'e hawayen na ci gaba da zubowa yace "Ammah kinji?, kinji wai Su Mum d'in Ajiddeh su sukeson kashe min Fatima, Ammah mey tayi musu zasu kasheta, mey tayi musu?", rungumeshi Ammah tayi tace "Shhhh Babana, Allah yayi da sauran kwananta a duniya, babu abinda zai sameta", kuka ya fasheda kamar wani karamin yana rungume da ita.
[12/1, 15:42] 80k: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

87

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Chapter 130 · 0% Book details