← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 166

Sashe 3

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gaban gate din wani mansion ta tsai da motar tare da yin horn, masu gadine su biyu suka fito cikin hanzari suka bude musu gate din suna yi musu sannu da zuwa, karasawa tayi cikin gidan har ta isa inda ake parking, kamin ta tsaida motan Yusra tayi sauri ta bude kofan ta fita Hafix ma ya bita a baya, cikin hadin baki Aunty da Batuul suka ambaci "Inna lillahi wa inna illaihi rajiun"Fa'iza ta fito itama a guje ta bi bayansu tana fadin bakuji ciwo bako su kuma suna ta kyalkyala dariya Yusra tana fadin ai na rigaka shima Hafix yana ya rigata, suna karasawa bakin wani sliding door mai girma na glass suka tsaya dan baza su iya danna kararrawar ba yayi musu nisa sai Fa'iza ce da ta karaso ta danna musu kararrrawar suka tsaya jiran 脿 bude musu kofar, 脿 dannawa na biyu ne aka bude musu kofa daidai lokacin Aunty da Batuul suka karaso suka Shiga ciki, parlour ne mara tarkace amma yana da kyau, wallpaper ne baqi mai flowers fari da grey zagaye da dakin , daga tsakiya akwai farin kujera mai L shape da throw pillows akai ,karamin round Table daga gaban kujeran, office chair daga gefe sai Babban TV da ya kusa cinye bango dan girmanshi 脿 manne da bangon.

Kanshine mai dadi na sandal wood ke fitowa daga parlour hade da iskan Ac mai dadi da sanyi ,bayan sun karasa daga ciki sun wuce wani bene mai rails silver suka isa wani dinning area shima cr茅am ne da Brown mai dauke da dogon dining Table da kwanuka na alfarma sai chandelier daga tsakiya

Bayan sun shiga sun zauna ne yarinyar da ta bude musu kofa tace "sannunku da zuwa Aunty " cikin hausar ta da ba dai dai ba " Aunty tace mata sannu Janet, Su Ahmad Sun fita ne naga motan da suka fita dashi 脿 parke "
"Janet tace 脿 ah Aunty sun dawo tun dazu Sun hau dakinsune, su da babane dukkansu Sun dawo shima ya tafi sama" " Batuul ce ta juyo bayan ta ajiye wayar da take dannawa tace Tabawa fa ko har yanxu aiki take ba 脿 samu tayi wanka ba, Janet tace 脿 ah Aunty taje dakine zatayi wanka, tace okay

Tafiya sukeyi suna ta gaisawa da dimbin jama'ar da suka halarci sallah Massa ya dubi Abutturab ''Man yaushe zaku koma Abuja ne ?
Abutturab ya furzar da iska daga bakinshi sannan yace " Yeah i want to leave in the next four days dan inada appointment da Minister amma nasan su Abui sai next week cuz su sai Sun gama sallah anan. I cant wait that long"
"Massa yace okay nima sai next week din zan shigo ", suna tafiya har suka iso inda su Abui suke, Abui ne ya Juyo ya dubesu tare da cewa mutumin da suke tsaye tare, "ai gasu nan ma", mutumin ne ya fadada murmushinshi tare da fadin "Masha Allah" ya miqa musu hannu suka gaisa, yacewa Abui "Its been long i met them , almost 19 yrs nasan bazasu tunani bama, anyway ya kuke ? Ana karatu ko kuma an gama ? Ko kuma aure za Ayine ya fadi maganar tare da dariya ? " , take fuskan Abuturrab ya canza dan baya so ana mishi maganan aure in Abui na kusa , yanxun nan zai tada maganar har sai ya dinga magiya tar茅 da bashi hakuri

Abui ne ya bawa mutumin ansa tare da fadin "ai aure kam sunqi shi, Shi Aliyu(Abutturab) architect ne dan yanxu ma yana da contact da minister Abuja, Mustapha(Massa) kuma Doctor ne tunda yayi karatu 脿 Germany sukayi retaining dinshi, but munaso ya dawo dan baza mu barshi cikin turawa ba", mutumin yace "gaskiya kam, Allah ya taimaka. " *Alai*(Alhaji) Ahmad Kyaree zan wuce yanxu dan nasan su Madam suna jira, tare mukazo dasu kuma ga ruwan da akeyi, zan kawosu before ku koma in sha Allah " , Abui yace okay 脿 gaidamin su, ace musu muma muna nan zuwa.

Tunda mutumin ya fara magana Abutturab bai dago kanshi ba har sai da mutumin ya fara maganan aure, a snn ne ya dago kanshi ya k'arewa mutumin kallo har yaso gano inda ya sanshi amma ya kasa, sai cewa Abui yayi bayan mutumin ya karasa barin wajen, " Abui is he an old friend"?

"Yeah 脿 good one too inji Abui ", tare da basu labarin tare da ce musu su tafi kamin ruwan ya kara yawa "

Ta miqe kenan tana cewa Aunty zata haura dakinta tayi wanka ta canxa kaya dan Sun jike ta hango Babanta na saukowa daga bene, da gudu taje ta rungumeshi, "tace Baa yanxu nakeso inje wajenka, ya d'an janyeta daga jikinshi yana tambayarta

"Batuul ya kayanki 脿 jike" ? "Tace Baa ai anyi ruwa 脿 waje ku tun dazu kuka dawo ko ? Ya sake ce mata "Batuul yanxu sallahn Allah shine kika saka baqin kayan nan kikaje har masallaci dashi ? Batuul ta danyi kasa da ido ta zumburo karamin bakinta kamin tace "Baa sabone fa kuma designer ne na Haut茅 脠lan kai ka siyomin mafa " , yace mata "toh naji maza Je ki cire su kar kiyi mura, tayi murmushi tace yanxu zan dawo ai, ta haura sama shi kuma ya karasa saukowa kasa .

Har ta wuce wani daki 脿 sama sai kuma ta dawo daga baya, cikin sand'a ta bude kofar dakin, a hankali take turawa, sai da ya fara karane ta bude shi gaba daya tana fadin Taraan, yara ne maza a dakin su biyar, kowa da game controller a hannunshi suna ta ihu,typical dakine na maza da akayi littering gwangwanaye drinks, kayansu da suka cire daga k'asa, gadajen 脿 hargitse sai plates din abinci da spoons.Yan manyan guda biyu da baza su wuce 13-15 yrs ba sanye suke da wandunan shadda sai fararen vest 脿 jikinsu hannunsu kuma maqale da agogo, sai mai bi musu shi kuma sanye yake da compl猫te kaftan dinshi brown harda hula akanshi ya tsaya akan sofa yana ihun ni zanyi winning, dayan kuma sanye yake da three quarter da T-shirt shima yana riqe da game controller, karamin cikinsu ne snn duk yafisu haske yana daga gefe riqe da Ipad 脿 hannunshi yana ta aikin dannawa, Suna ganinta suka yadda abubuwan dake hannunsu, Manya ukun na ihun Aunty ta dawo kanana biyun kuma suna cewa Mama ta dawo, a guje suka fito kowa na rige rigen ya riga dan uwanshi fita daga dakin, Da sauri Baatul ta matsa daga bakin kofa dan kar su bigeta tana ta dariya ta juya ta bar kofar dakin ta karasa nata dakin ta murda kofan ta shiga.
[8/22, 1:30 PM] .: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

5

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Tana shiga daki ta nufi inda towels dinta ke rataye, ta janyo daya sannan ta cire kayan jikinta da suka jiqe, ta daura towel din a kirjinta, ta nufi toilet din dake dakin nata, bayan minti goma ta fito tana kanshin shower gel da sabulun Makari,da towel a jikinta daya kuma a daure a kanta kamar turban, gashin goshinta ya kwanta lub lub, fuskanta ya kara haske da kyau, ta karaso gaban mirror dake cike da turararruka da yan kayan kwalliya da na shafa , ta jawo stool din mirror ta zauna sannan ta dauko man Makari, a hankali ta riqa shafa man kamar baza ta gama ba, bayan ta gama ne ta karasa gaban closet din kayanta, ta bude ta dauko peplum blouse da skirt din atamfa baqi mai pattern din purple ta saka 脿 jikinta, kayan ba karamin kyau yayiwa jikinta ba, komawa gaban madubin tayi ta shafa powder a fuskarta sannan ta saka kwalli a idonta, ta shafa nude lipstick a bakinta , ta bude costume box dinta dake kan madubin daga gefe ta dauko dankunne da sarka silver masu duwatsu a jiki, sai abun hannu da zobe shima silver, sannan ta fesa turare, ta kalli kanta a madubin tare da murmushi sannan ta koma ta zauna a kan gadonta tare da d'aukan wayanta,

bayan ta d'an daddana wayan ne ta kara 脿 kunne tare da fadin "Hello Riri, shine kikace min a Ramat Square zakuyi sallah, kuma bakije ba,
Daga daya bangare aka amsa ana dariya tare da fadin

"Yo babe nan naje mana, i wanted calling you inji inda kike sai sai da na duba wayana naga ban fito dashi ba, You know anytime Yaa Abu na gida toh komai nawa doesnt seems to be ryt"

"Batuul tace babu wani Yaa Abu, anytime kika samu matsala sai kice shine, toh duk ranar da zan ganshi sai na fada mishi

"Riri tayi dariya,tace mata dan baki sanshi bane ai, koh face dinshi idan kika gani zakiga ko smiling bayayi, brows dinshi kullum a hade, bayayiwa mutane ma magana wai surutu na saka mishi ciwon kai, kuma ko bashi zaiyi ba wai baza ayi a kusa dashi ba,

"Batuul tace all these apart, ni zanzo yau dan Baa yace nan da kwana hudu zamu koma dan yana da aiki sosai kuma gobe da jibi zamuje wajen su Yayya da sauran Family

"Riri tace yawwa bae of earth,daman ina ta tunanin yadda zan ganki, I missed you soo much wlhy, kizo yanxu i have have So many things for you alone, Batuul tayi dariya tace
"You are not serious, ai sai na fadawa Baba tukunna, sai yayi approving zuwana

"Riri ce ta marairaice murya hade da cewa nasan Baba zai barki sai dai in kece bakison zuwa, pls kizo, am bored over here, kuma kinsan Yaa Abun in yana nan ba a yawo "

"Batuul ce ta cemata ni ba ruwana and i told you zan fada mishi whenever i meet him"

"Ai bazaki iya ba nasanki, I wish zaki zo yana nan shima yaga wanda ya fishi rashin magana,ai mantawa ma nayi halinku daya nake fada miki

"Ni dai yanxu a bar maganan, yanxu zanje in fadawa su Aunty zanzo wajenki ,

"Aii sai kinxo"
Chapter 3 · 0% Book details