← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 166

Sashe 61

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tunda suka 膹au hanyan airport take kuka ba k'akk'autawa dan tasan farin cikinta ragagge ne tunda har ta yadda tabi Abu wani garin da babu kowa nata, tausayin kanta take sosai tana kuka, sai da tabi y'an uwanta 膹aya bayan 膹aya tayi hugging 膹insu tana kuka su din ma kukan suke, har ta iso kan Farida dake kukan itama ta rungumeta, da k'yar suka sake juna don itama kukan da take ya hanata yin magana, ta kasa yin komai sai gya膹a kanta da takeyi, cikin hanzari ta sake Farida xata bi Sadiq da ya kasa ci gaba da kallon emotional scene din ya juya xae bar wajen, Abuturrab ya fixgota jikinshi, sosai ta shiga yin kukan kmr ana tunxura ta, dai dai saitin kunnenta ya sunkuyo a hnkli yace "control, its a public place baza mu tafi kina kuka kamar wacce na sato ba", kwanciya tayi jikinshi tayi lamo tana ajiyar xuciya, yana jin yadda heartbeat 膹inta ke up and down, hannunshi 膹aya ya 膹aura bayanta, 膹ayan kuma yayiwa su Sadiq alamun suja su Ahmad su tafi, hakan kuwa akayi, takai minti biyar kwance jikinshi, can da ta tsagaita kukan ta fara dawowa normal ta 膹ago kanta, jinta jikinshi yasa ta kallon fuskanshi taga shima ita yake kallo, da sauri ta matsa baya ta juya bayanta ganin ko su Farida na nan, taga wayam babu kowa wajen, kallonshi tayi da idonta da yacicciko tace "Yaa Abu dan Allah mu koma kar mu tafi plss", wani irin kallo ya bita dashi yaja akwatin dake gabanshi yace "When you are done ina ciki", babu yadda ta iya haka tabi bayanshi a sanyaye tana share hawayen dake sakko mata, a departures waiting room ya xauna yana jiran jin announcement din departure'n su sanin few minutes ya rage, ya juya yana kallonta ganin a tsaye take, a hnkli ta xauna nesa da shi kanta a kasa, tabe baki yyi ya kauda kai, bayan kusan minti takwas akayi announcing cewar passengers din Abuja to UK su fara boarding ynxu jirgi xae tashi, mikewa yyi yana kallonta, wasu sabbin hawayen ne ke sauko mata duk jikinta yyi sanyi ta kasa tashi, har ya fara tafiya yana jan trolley dinsa ya tsaya, juyawa yyi yana kallonta ganinta xaune yasa ya dawo yana kallonta bbu yabo bbu fallasa yace " Ko in daga ki ne" a hnkli ta mike tana rufe bakinta da mayafi kar ta saki ihun da taji na shirin fitowa, sauke idonsa yyi daga kallonta ta kama hannunta ya shiga tafiya tana binsa har suka isa inda jirgin British Airline (B.A) yake tsaye, yana rike da hannunta suka shiga jirgin, a first class ya samar masu empty seats, a hnkli ta xauna ta jinginar da kanta jikin kujerar tare da lumshe ido, ya saka trolleyn hannunsa daga sama inda ake ajiye luggages, snn shi ma ya xauna, announcement aka shiga yi na cewa "Passengers on board shud pls fasten their seat belts, British Airline flight is about taking off" Abuturrab yyi fasten din seat belt dinsa yana kallonta, gani yyi ko motsi bata yi ba, ranan da suka yi boarding same plane daga Maiduguri xuwa Abuja ya tuna, yyi shiru yana kallonta, a hnkli ya kai hannunsa ya mata fasten din belt din da kansa, ta bude rinannun idonta tana kallonsa, lkci daya ya hade rai, da sauri ta sunkuyar da kanta, wayarsa ya fiddo ya maida shi flight mode ya jona earpiece ya sa a kunne ya lumshe ido, jirginsu na tashi ta fashe da wani kukan tausayin rayuwarta, bude ido yyi yana kallonta sae dae bae ce komae ba, tayi mai isarta bayan wani lkci tayi shiru ta kwantar da kai jikin kujeranta lkci daya bacci ya dauketa, sae a snn ya cire earpiece din kunnensa ya rike kansa dake sara masa xuciyarsa a dagule, from Where is he going to start this long explanation to his Ajiddeh, just ta ina xae fara ce mata iyayensa ne suka makala masa Batuul, ya xata dauki xancen, will shi even believe him, tunanin hkn ya sa ciwon kansa ya tsananta, jinginar da Batuul tayi jikinsa tana bacci ya dawo da shi duniyar tunanin da ya tafi, juyawa yyi yana kallonta ya ga bacci ssae take, ya fuzar da iska tare da lumshe ido ya jawota jikinsa don gyara mata kwanciya, muryar wata hostess din jirgin ya sa shi bude idonsa, tana tsaye dai dai kujeran da suke plate holder din seats dinsu ta jawo ta dora ruwa a kai a karamin disposable cup, murmushi dauke fuskarta tace "Sir what would yhu like to have?" Yace "Just coffee" kallon Batuul tayi xata yi magana yace "She's OK" juyawa tayi ba a dau lkci ba ta dawo da cup din coffee ya karba yace "Thank you" d'an bow din masa tayi tana murmushi tace "Yhu are welcome Sir" daga hka ta juya ta bar wajen. Karfe sha biyu saura na dare Batuul ta bude idonta ganinta jikinsa yasa ta kallesa, idonsa lumshe yake alamar ya fara bacci, a hnkli ta xame jikinta ta xauna da kyau, ta shiga rera kuka tunawa da tayi shknn fa ta rabu da Anty, bude ido yyi yana kallonta, ya gyara xamansa a fusace yace "God! What again? Ke wae baki gajiya da kuka ne, am tired of this pls, aiki kawae su Ammah suka hada ni da I knw" jin ta kara sautin kukan yasa ba tare da yyi wani tunani ba ya jawo ta jikinsa murya can kasa yace "are yhu hungry" kin cewa komae tayi, ya watsa mata wani kallo yace "Kina jina dae koh?" Girgixa masa kai tayi, ya hade rai yace "Gud! Go back to sleep ynxun nn" rufe idonta tayi, tayi lamo jikinsa sae dae yana jin ynda xuciyarta ke bugawa. Har asuba daga ita har shi basu rintsa ba, da ta bude ido xae tambayeta ko tana jin yunwa ta girgixa kai ta kuma rufe idon, Karfe bakwae na safiyar washegari jirgin British Airline ya sauka airport a UK, nn fa Abuturrab ya ji duniyar gaba daya tayi masa xafi, da ya tuna Ajiddeh sae gabansa ya fadi ba kadan ba, da kyar ya mike yana kallon Batuul da idanuwanta suka rine ssae, hade rae yyi lkci daya ta mike kanta a kasa, ya fiddo trolley dinsa ya shiga tafiya, bin bayansa tayi hawaye cike idonta har suka sauko daga jirgin, duk da ta sha xuwa kasashen turawa da Baba har ma da Anty Hafsat yau komawa tayi kmr bakauyiya a haraban airport din, don sae shishshige masa take, ba komae kuma ya janyo hkn ba sae don duk a tsorace take, ba kuma wae turawan suka bata tsoro ba sae don tunawa da tayi da Ajiddeh. 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

43

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Amma na ganin tafiyarsu ta koma cikin gida itama tana jimamin rashin Batuul da zatayi, 膹akin Abui ta wuce ta sameshi zaune yana kallo da glass idonshi, daga gefenshi ta zauna tace "Barka da zama Abui", yace "Yawwa Ammah, naga har kin fara missing yaran naki", murmushi tayi mishi tace "Ai ni tausayin yarinyar nan ke cikani, sosai nake tausayinta danma dai tana da nutsuwa", juyawa tayi ta kalli Abui with full attention tace "Abui amma hankalina gaba 膹aya yaqi kwanciya, matar Abu nake jiyewa Batuul dashi kanshi Abun, ko wancan karan ni nasan Abu ba yin kanshi bane zaman da yayi ba tareda dawowa gida ba har na shekara 膹aya", with full concentration Abui yake kallonta har saida tayi shiru yace "Ehhh shiyasa this time da mukaje Maiduguri kamin a 膹aura aurenshi sosai nasa aka mishi addu'a, sauk'an Alqur'ani kuma kullum sai anyi har yau 膹innan Allah ya rabasu da sharrin masharranta", wani ajiyar zuciya Ammah ta sauk'e tace "Alhamdulillah", ta gyara zamanta tana fuskanta Abui tace "Nima tun lokacin da Ashiekh yace a dage da addu'a ban daina ba, yanxu naga komai ya fara daidaita, dan banga alamun abinda akayi mishin har yanxu yana jikinshi ba, sai dai mu sake dagewa Allah ya sake rufa asiri, wannan karan har Batuul 膹in sai da na sa ana yiwa sauk'an Qur'ani da addu'a, daga baya ma zan sake tura mata maganin kariya dan yanxu lokaci ya k'ure shiyasa ban basu ba" Abui yace "Allah ya sake karewa, tare suka amsa da "Amin", mik'ewa tayi tana kallon Abui tace "Abui abincin fa baka ci ba gashi har takwas ya wuce", murmushi 膹auke fuskanshi yayi mata alama da tazo ta zauna gefenshi, ba musu ta dawo ta zauna gefenshi tana kallonshi yace "naga kina ta hidiman yaranki bakizo bani abinci ba shiyasa nima banci ba", murmushi tayi dan tasan tsokanarta yake ta 膹an kalleshi tace "Toh su ba yara bane, kai ai kullum inayi maka kuma daga yau su tafiya zasuyi", k'ok'arin tashi take daga wajen tana cewa "Abui bari in kawo maka tea toh tunda baza kaci abincin ba", jawota yayi jikinshi yace "No am okay, kiyi zamanki nima bana jin yunwa, i ate late in d evening shiyasa banci abincin ba, kuma tea 膹inma i dont feel like taking it", batace komai ba ta sake shigewa jikinshi daga nan sukaci gaba da hiransu,
Chapter 61 · 0% Book details