← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 166

Sashe 102

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

yasa Aunty Jainaba jin kunya tace "Laah Aliyu ashe har ka dawo, gashi mun b'ata maka d'aki", Ajiddeh kam ko kallonshi batayi ba, Murmushi yayi wa Aunty Jainaba yace "Nah its okay, ba komai, I will use another room", da haka ya fice ya jawo musu k'ofa, d'akin Batuul ya koma ya murda kofar yaji a rufe, komawa yayi ya dauko spare key sannan ya dawo ya bude ya tura kofan a hankali, as usual yana k'anshin da ya saba, kayanta ya tarar da ita tana gyarawa, kallo d'aya ta mishi ta d'auke kanta taci gaba da abinda takeyi fuskarta daure, k'arsawa yayi ciki ya kamo hannunta ya jata, tirjewa tayi a waje d'aya tana kallonshi tace "Lafiya, ko ka mance hanyar dakin matar taka ne?", ita kanta mamakin sabon halin nan nata takeyi, shi ma haka ya tsaya kallonta cike da mamaki, ta juya ta ci gaba da abinda take yi, ganin zata b'ata mishi lokaci yasa ya d'agata cak "baki ta bud'e zata sa mishi ihu ya sa yatsa ya bige mata d'an baki yace "shout and I will drop you down d stairs, dare me ki ga", gaba d'aya kanta ne taji yana juyawa kamar d'azu ga tashin zuciya, wani k'arfi ne yazo mata ta sauk'a daga hannunshi tace "zan tafi da kaina, ba sai ka d'auke ni ba", ta fad'a tana murgud'a mishi baki, shi mamakin sabon halin nan nata kawai yakeyi har ta fito daga cikin d'akin shima ya biyota rik'eda hijab d'inta, ganin Hijab a hannunshi yasa ta ce mishi "wai ina zamu?", baice mata koma ya rik'ota ya sa mata Hijab d'in ya jata sukayi waje, mota ya bude ya saka ta ciki sannan ya xaga shi ma ya shiga ya tada motar suka bar compound din, eatry ya nufa da ita ya siyo masu abinci suka dawo gida, yana gama parking ta fice daga motar ya bi ta da kallo yana murmushi, fitowa yayi shi ma ya kwashi ledojin abincin ya rufe motar ya bi bayanta, dakinta ta shige ta fada kan gado jin yanda xuciyarta ke tashi, ya hauro sama shi ma, yayi knocking dakinsa da su Ajiddeh suke, Ajiddeh ta leko fuskarta daure ya mika mata leda daya, wani matsiyacin kallo tayi masa tace "Ae nayi xaton da yunwa xaka bar 'yar uwar tawa" daga haka ta maida kofa ta rufe ta bar sa nan tsaye, girgixa kai yayi cike da takaici ya juya ya nufi dakin Batuul, ajiye ledan hannunsa yayi ya karasa kusa da gado ganinta kwance ya xauna daga gefenta yana kallonta yace "Tashi ki ci abinci" ba tare da ta kallesa ba tace "Am OK ka kai ma matar ka" dariya ta basa ba kadan ba yace "Uhnn! Ae sai da na fara kai mata kafin in kawo maki" tace "Nawan ma ka hada mata ta cinye" dariya yayi ya dago ta yace "Ashe kema haka kika iya masifa, wannan ba halin Anty bane" kwace kanta tayi tace "Ni ka kyaleni" yace "Sakko ki ci abinci toh" tace "Ban ci" sakko da ita yayi kasa ya jawo ledan yace "Look am not joking fah" bude kofa aka yi daga waje, yyi saurin mikewa yana kallonta yace "Kafin in dawo ki tabbata kin cinye" daga haka ya juya ya nufi kofa ya fita, mikewa tayi da kyar ta koma ta kwanta don duk ta rasa me ke mata dadi ga tashin xuciyar da yasa ta gaba, tana kwanciya bacci ya dauketa. Shi kam Abuturrab duk ya kagu Ajiddeh ta koma gun 'yar uwarta ya je yaga ko Batuul ta ci abincin don xuwa tayi ta sa shi gaba a palo, har sha biyu bai ga alaman xata tafi ba yace "Kin bar Anty ita kadae" tace "Ehh ita tace in tafi gun mijina bacci xata yi" bai kuma ce mata komai ba, har dai ya mike daga karshe yace "Am going to bed yanxu" ta mike tana mitsika ido, ya kashe kayan kallon parlour'n da wuta ya nufi sama ya bar ta, ta bi bayansa, kwanciyarsa yayi a bedroom ya juya mata baya ta shige jikinsa, ko ta kanta bae bi ba ya lumshe ido kamar me bacci, yana jin alaman tayi bacci ya xame jikinsa daga nata ya mike daga gadon ya fita daga dakin, dakin Batuul ya shiga, ya karasa yana kallonta, kwata kwata bai ji dadin rashin cin abincin da bata yi ba, ya xauna gefenta ya cire duvet din da ta lulluba da a hankali, ya ji jikinta da d'an xafi, ya jima yana kallonta sannan ya lumshe ido yayi pecking lips dinta ya mayar mata duvet din jikinta ya mike ya dauke ledan abinci yasa a fridge ya fita daga dakin ya koma nasa.馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐
Chapter 102 · 0% Book details