Sashe 165
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
aka fara mata a hannu kamin a fara yiwa Ammah, taso ayi mata na k'afa amma a al'adar kanuri yara ko y'an mata basa yin lallen k'afa sai dai matan aure, sam Batuul tak'i yadda da ayi mata shi, sai wajen sha d'aya sukayi musu sallama akan gobe zasu dawo suci gaba da ziyara har gidansu Shehuri, har parking lot suka rakosu, Twinkle kamar a barta ta kwana dan ta sake da Ammah kuma ta bata chocolates masu dad'i, ana fitowa Twinkle ta hango wata mota tace itakam Sam a ciki zasu tafi gida, babu yadda suka iya haka Sadiq ya koma ya d'auko musu key d'in motar, Batuul kam na ganin motar saida gabanta ya fad'i, shekara biyar yanzu amma tana iya tuna komai about motar, Sadiq na kawo key d'in suka shiga, sai tsokanan Twinkle yakeyi da turanci, ta had'e rai tace "My Mommah said I should not speak Nasara again", Sadiq ya kwashe da dariya yace "And you just did", tayi maza ta riqe baki tace "Sorry Mommah", Batuul kam shiru tayi tana ta tunane tunane zaune cikin motar, har suka d'au hanya bata ce komai ba sai Twinkle da Abu ke hiransu, Pidgin motar Twinkle ta bud'e tana saka hannu ciki, wani d'an kwali ta ciro a ninke cikin pidgin d'in sai k'anshi yakeyi, Abu tana nunawa tace "Daddy see what I found", Hannu ya mik'o daga baya ya amshi d'ankwalin yana kallo da ido, ido Batuul ta wara ganin d'an kwalin, takan manta da kayanta koda bata rabu dasu ba, in har ba ganinshi tayi ba mancewa takeyi dasu, Ammah wannan tana ganinshi ta tuna komai da ya faru da ita a ranan da ta sakashi, ranan da ta fara had'uwa da Abutturab, ranan ta fara shiga motarsa, ranan komai na rayuwarta ya canja, a hankali taji bugun da zuciyarta keyi ya fara daidaita, hannun Abu masu d'umi taji cikin nata, ajiyar zuciya ta sauk'e tana jin wani abu na ratsa duka sassan jikinta, ido ta lumshe ta bud'e snn ta kalleshi tace "You still remember?", murmushi yayi yana kawo hannun nata daidai bakinshi yayi kissing snn yace "Ban tab'a mantawa ba Fatima, Ban tab'a mantawa da rana d'aya da nayi spending tare dake ba, they are my most treasured moments and memory I always keep to reminisce, ranan da kika saka kayan nan ranan na fara had'uwa dake, ranan da sonki ya zama a part of my breathing,ranan na fara d'aukanki a motata, ranan nasan komai nawa ya canja, hankalina bai sake kwanciya ba saida na mallakeki a matsayin matata, son da nake miki is something da ban san ya akayi na fara shi ba kuma bansan ya zan gama shi ba, abu d'aya nasan ina fata yanzu, to be with you till my last breath Fatima, I can't imagine life without you yanzu because inasonki dayawa, I love you a lot", murmushi tayi idonta na cika da kwalla ta kwanto ta jikinshi tace "I love you more Yaa Abu, I will be with you In sha Allah", "In sha Allah" shima yace yana sake kissing hannun nata, Twinkle dake wasa da iPad can baya bata san ma mey ake ciki ba, kamin su k'arasa gida har tayi bacci.