← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 166

Sashe 113

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Har jirginsu Aunty Jainaba ya sauk'a Nigeria hankalinta yaqi kwanciya kan abinda Ajiddeh ta fad'a mata, inko gaskiya ne ai da sun kad'e dan kishiya ba abar so bace ko cikin mafarki, bazai ma yiwu bane, Aliyu ya raina musu hankali, amma koma menene zasuyi maganinshi maci amana kawai, so take kawai ta isa gida ta fesawa Mummy lbrn cin amanan da d'an matsiyatan nan yayi musu, Dan ba Ajiddeh kad'ai yayiwa ba, ko jiran driver batayi ba ta tari Taxi tayi hanyar gida, suna isa tacewa driver taxi ya jirata a kawo mishi kud'inshi ta shige cikin gida jikinta sai b'ari yakeyi kamar ita aka yiwa kishiyar, a hakimce ta tadda Mum d'in Ajiddeh zaune a parlour, da mamaki Mum ke duban Jainaba da ta fad'o cikin d'akin ko sallama babu tace "Keh kuma daga ina haka kamar ana tunkud'oki, mey ya faru kika dawo da wuri haka keda zakiyi har sati biyu", waje ta nema ta zauna jiki na b'ari, Mummy ta gyara zama tace "Keh ko lafiya haka, Ya Ajiddehn take?", gumin da takeyi ta goge snn ta shiga korowa Mummy bayanin duk abinda ya faru tun zuwanta har zuwa zancen cikin dake jikin Batuul da kuma abinda Ajiddeh ta fad'a mata kan cewa Batuul matar Aliyu ce, wani irin zabura Mummy tayi daga kan kujerar da take zaune ta dafe k'irji tana rafka salati tareda cire d'ankwalin kanta da ya bayyana gashin kanta mai tsawo da shek'i tana fifita dashi dan wani irin zafi takeji duk da Acn dake aiki, tace "Jainaba bana son zancen banza, wane Aliyun ne yayi aure?, ba dai na Hawwa ta ba, ina ba Aliyun Ajiddeh bane ya k'ara aure" Jainaba dake zaune ta mik'e tace "Shi d'in ne kuma ma dan wulak'anci irin nasa har ciki ke gareta yanzun, wannan tsinanniyar yarinyar wai itace matarsa duk ba a sani ba", Cikin d"aki Mummy ta shiga sai gata rik'e da gyale da jaka tana ta sababi tace "Ni Bilkisu zata wulak'anta, duk burin da naci kan Ajiddeh? Su da zaman lafiya saida su ga wasu nayi, shima munafikin Aliyun shine harda dukar min y'a ko?, toh duk sai sunci ubansu gabaki d'ayansu dan sai nasa sunyi kuka da idanunsu munafukai kawai, wannan ciki sai ya zama sanadin rushewar farin cikinsu baki d'ayansu, sai na nuna musu kan kishiya babu abinda bamayi, munfi k'arfin zama da ita koda tadda ta mukayi bare kuma an kawo mana ita a munafurce" ta fad'a tareda wani d'an guntun murmushin takaici ta kalli Jainaba da ta koma ta zube kan kujera tsabar gajiya tace "Yaya ina kuma zamu? Ni wlhy duk na gaji, in na huta sai mu tafi", ta watsa mata wani irin kallo tace "bakida hankali inaga, ace miki anyiwa Ajiddeh kishiya keh har lokacin hutu ke gareki?, ai in kinga mun huta to sai naga na d'agawa Bilkisu hankali itada Zuri'arta baki d'aya naga sun wulak'anta sun d'and'ani bakin cikin da suka jefa y'ata snn zaki samu damar hutawa, kan y'ay'ana biyun nan babu abinda bazanyiwa mutane ba, bare ma Ajiddeh wacce tafi komai soyuwa a gareni, duk burina yana kanta, sun jawowa kansu, maza ki tashi muje", Rai b'ace Jainaba ta mik'e da k'yar dan duk jikinta ciwo yake mata ga gajiya suka fita waje, Sadi driver na ganin Mummy ya washe baki tareda k'arasowa wajenta yace "Hajiya fita zamuyi kenan?", tace "Ehhh maza d'auko mota, Kuje zamu yanzun nan", Jainaba batace komai ba sai bin Mummy da takeyi a baya kamar wata doluwa, saida ya fita da motar bayan sun shiga sun zauna ta dubi Mummy tace "wai gun wa zamu a Kuje?" Mummy ta kad'a kai tace "wajen wani Malamin zamu mana, wannan ma yafi kowa iya aiki danshi baima San Allah ba, Matsafine sosai na bugawa ma a Jarida snn shi ba kowa yakewa aiki ba sai in kanada connection, kin dai San y'an cikin k'auyen garin Abujan nan da basu San wani Addini ba, toh gunshi zamu, Hajiya Ramatu ta dad'e da cemin zata kaini gunshi ban samu munje ba sai kwanaki ne dana rakata kuma naga aikinta ya kammalu in no time kinga har ta samu ta auri wannan Ambassador, matanshi kuma sun shiga gari yanzu daga ita sai y'ay'anta da ta kawo suke zama a can, y'ay'an mijin nata ma ta koresu kuma mijin bai isa cewa komai ba , yanzunma can d'in zamu, dan ni na tabbata banida mak'iyi kamar wanda zai tab'amin y'ay'a", a bakin gate suka tadda driver d'in taxi shida Mangal yanata mishi zuba, Sadi Aunty Jainaba tacewa ya bada kud'in motar ya ciro ya mik'a suka d'au hanyar Kuje, saida suka shiga can cikin k'auyen snn tacewa Sadi sun kawo, nan yayi parking suka fito suka isa y'ar bukkar hatsabibin bokan nasu mai suna Namurje

Hawaye kawai Farida keyi dan ita Sam bata shirya tafiya ba yanzu, Abu kam driving yakeyi hankali kwance ko kallonta baiyi ba, a hankali ta bud'e baki tace "toh Yaa Abu kaga bari in k'ira Ammah in fad'a mata ina zuwa kar taga nayi dawowan baza....", wani irin kallo da ya wurga mata yasa ta saurin sunkuyar da Kai, bata sake d'agowa ba saida taji yaja ya tsaya da motar, jiki a sanyaye ta d'ago kai tanace airport suka zo, duk ranta ba dad'i batayi sallama da Batuul ba, ganin ba airport bane yasata sauk'e ajiyar zuciya tareda murmushi, fita yayi daga motan yayi gaba itakam tana nan zaune dan baice ta fito ba, saida yaje bakin k'ofar shiga yaganta zaune cikin mota ya daka mata harara yace "kin fito cikin motar nan ko sai nazo na fidda ki mara kunya", ba shiri ta fito tana zumb'uro mishi baki tabi bayanshi, numfashinta ne ya kusa d'aukewa ganin irin tsaruwar gidan, tasha ganin gidaje masu kyau ko designs d'in Yaa Abu amma wannan daban yake, ya tafi da ita ba kad'an ba, binshi kawai takeyi har suka k'arasa hawa sama ya bud'e wani d'aki ya shige ciki, bayanshi tabi itama ta shiga, Batuul ta hango kwance kan gado tana bacci hankalinta kwance, batasan lokacin da ta fasa wani ihu tana fad'in "Sweetheart ashe kina nan shine kika barni so lonely inata Nemanki....", tana yi tana nufar gadon da niyyar hawa, da hanzari ya fizgota yana mata mugun kallo yace "bakida hankali ko? Tashinta zakiyi daga baccin", ta zumb'uro mishi baki tace "toh aini ban sani ba" , yaja tsaki ya jefar da ita ya koma gaban computer da alama tunda ya fita baccinta takeyi hankali kwance, d'an murmushi yayi ya dawo bakin gadon tareda hawa yana kallon kyakyawar fuskarta, hannu yasa ya gyara mata gashinta da ya bazar tun d'azu snn ya gyara mata duvet, a hankali ta bud'e lumsassun idanunta dake cike da bacci ta sauk'esu kanshi, murmushinta mai kyau tayi mishi ta sake maida idanun ta rufesu, shima har lokacin murmushin ne a fuskanshi, Farida ikon Allah ta tsaya gani, a hankali ya sunkuya yayi kissing goshinta snn ya sauk'o daga kan gadon, Farida ya gani duk ta wara ido tana kallon Abunda yake, harara ya sakar mata yace "kallon na lafiya ne, mara kunya kawai saura ki tada ta, kuma if you try something stupid sai nayi maganinki dan yanzun ma ba k'yaleki nayi ba" daga haka ya fita, itakam yana fita ta murgud'a bakinta tace "masifaffe" tayi windown d'akin tana kallon yadda tsarin gidan mai kyau yake
Chapter 113 · 0% Book details