← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 166

Sashe 73

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

A dinning d'in ta ganshi zaune yayi serving kanshi breakfast din da ta yi yana ci, Ajiddeh na daga gefenshi tana ta kumbure kumbure, tana ganin Batuul ta watso mata wani mugun harara, ko kallonta Batuul batayi ba ta karaso cikin falon ba tare da tace musu komai ba ta wuce, har ta kai bakin kofa idon shi na akanta, sai da yaga fitanta snn ya maido da hankalinshi kan Ajiddeh da ta zuba mishi ido rai a b'ace tana kallon yadda yake kallon Batuul, yasan driver bazai tafi ba sai ya jirashi ya fito dan yana son bata wayanshi in ta tashi a k'ira a d'auketa kuma ya bata kud'i, yi yayi kamar bai San kallon da take mishi ba yace "so you ain't eating har yanzu, kilan zaki dafa ne ko kuma sai na tafi zaki faraci ta shigo ta ganki kinaci kije kina amai koh", ya karashe maganan yana murmushi, sake hade rai tayi tace "kaga nifa wulakancinka ne banaso Aliyu, koh jiya a gabanta ka dinga min dariya, ko ta rainani ai kai ka jamin, bare ma bata isa tayi hkn a gidana ba", bai ce mata komai ba yaci gaba da cin abincinsa yana murmushi, sai had'iyar miyau take tana kallon yadda yake cin abincin, duk yadda akayi abincin nada dadi ganin yadda yake ci sannan ga k'anshi duk ya gama bad'e ta a gun, kallonshi tayi rai a b'ace tace "magana fa nayi maka amma kaqi kulani sai tunkud'a abinci kakeyi kamar wanda bai tab'a ci ba", kallonta yayi da idanunwanshi dake piercing zuciyarta yace "ko kin taba dafa irin wannan ne a gidannan da kike cewa inaci kamar ban tab'a ba", baki ta turo tace "nifa duk ba wannan ba, ai abinci ga ka gashi, baby ni abinda na tambaya tun jiya, I urgently need it, gashi har ka shirya bakace komai ba fa", cike da shagwaba ta kare maganar, shi kam har ta gama maganan bai ce mata komai ba, da alama santin chips d'in Batuul yasashi kasa magana, ran Ajiddeh ne ya fara b'aci, tashi tayi a fusace zata tafi ya riko hannunta da sauri, ya dawo da ita ya zaunar kan dinning chair din, kallonta yayi da murmushi a fuskanshi yace "keh bakisan in mutum na cin abinci bai son damuwa ba, da kinci abincin kema nasan all your worries will b cleared away" wani irin kallo ta mishi yace mata "tunda bakici je d'auko min cheque d'ina a sama", da murna ta mike ta haura sama, bata jima ba ta sauko rike da cheque book dinshi a hannunta, har saida ya gama cin abincin tukunna ya janyo ya rubuta mata amount din da take bukata, murna ta dinga yi kamar mey, har bakin kofa ta rakoshi tareda yi mishi peck a kumatu sannan yayi mata sallama ya tafi.
Chapter 73 · 0% Book details