Sashe 75
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Abuturrab na fitowa ya shiga Duddubawa ko zai ga motar driver amma wayam, da mamaki ya ciro waya ya k'irashi, yana d'agawa yace "I didn't say you should leave, where are you guys", a daburce driver yace "Sir Ma'am insisted we should leave, and am by d office now, av already dropped her", rai a b'ace ya katse k'iran ba tare da ya jira driver ya k'arasa magana ba, he wanted giving her money, kuma inma ta gama lecture ya za ayi tasan anzo d'aukanta, d'an tsaki yaja ya fad'a motarsa, awa biyu sukayi suka fito daga class d'in, gumi sosai takeyi tsabar azaban ciwo amma ta daure dan bataso su Aisha su sani, Aisha ce ta fara yi musu sallama ta wuce yau da yayarta zasu tafi, bayan minti kamar Sha biyar Samantha ma ta wuce, sai lokacin tayi tunanin bata fad'awa driver ya dawo lokacin ya d'auketa ba ya fad'o mata, waje ta nema ta zauna ta kifa kanta kan gwiwa ta fashe da kuka, sunan Aunty kawai take k'ira, ita Yanzu ya zatayi ga ciwon ciki da zai hanata takawa ta tafi da k'afa tunda ba nisa sosai, gashi bata da kud'i bare tayi karambanin hawa Bus ko Taxi tunda ba lallai ma ta gane ba, kuma batada number Yaa Abu bare ta k'irashi tace ta gama lectures azo a d'auketa, to in ma tana da shi iya kiransa xata yi, kuka sosai takeyi kamar wacce ake zanewa, tafi awa d'aya zaune a wajen, kamar daga sama taga mota yaja ya tsaya gabanta, a hankali ta d'ago rinannun idanuwanta dai dai lokacin da ya fito daga motan, tsayawa yyi ya hade rae yana kallonta, sunkuyar da kai tayi ta mike a hnkli tana jan kafa ta xaga xuwa seat din gaba, tana shiga motar shi ma ya shiga ya rufe, ya juya yana kallonta fuskarsa daure sae dae fa har da borin kunyan daxu da safe yace "How dare yhu xan ba driver na order ki sa ya ketare? Kin yi employing driver ne garin nn?" D'ago kai tayi tana kallonsa, sae a snn ya lura da idonta da yyi ja, kana ganinta kasan kuka tayi, d'an kyabe baki yyi ya tada motar ya ja ya nufi gida, jinginar da kanta tayi jikin kujeran motar ta lumshe ido tana jin ynda ciwon cikinta ke karuwa ba kadan ba, yana gama parking a garage ya bude motar ya fita ba tare da ya bi ta kanta ba, da kyar ta bude motar ta fito, bata jira ya kulle motar ba ta nufi cikin gida, bin ta yyi da kallo yana mamakin halinta, komai kuka kmr wata 'yar goye, tsaki yyi ya rufe motar ya nufi cikin gidan shi ma. Bbu kowa falon Batuul ta haura sama da sauri ta shige dakinta ta sa key ta fada kan gado ta cusa kanta cikin pillow ta dinga rusa kuka kamar ranta zae fita, juye juye ta shiga yi ta sauko k'asa ganin kwanciyar ma ya gagareta, kan kace me duk ta fita hayyacinta. Abuturrab kam bedroom dinsa ya shiga, ya nufi toilet yyi wanka, xaune ya samu Ajiddeh dakin da ya fito, ta mike tace "Babe wllh na mance ban gaya maka ba, lotions dina sun kare, gashi akwae wani turare don nake son siya, xan kuma sake kayan make up" wani kallo ya shiga mata yace "Wae ke wace irin mace ce Ajiddeh, how on earth mijin ki xae dawo daga aiki bbu sannu da xuwa, baki bari ya huta ba, baki kawo masa ko ruwa ba ki xo kina masa lissafe lissafen banxa, to bani da kudin siyan komae ynxu" sakin baki Ajiddeh tayi tana kallonsa, sae kuma ta ja tsaki tana hararansa cike da fitina tace "Toh idan ban maka lissafe lissafe ba Aliyu wa xan ma, ko ina da su xan xo ince maka bbu, ubana xan kira ince yyi min bayan kana da halin min" kayansa ya sa ya fice daga dakin ya bar ta nan tsaye, downstairs ya sauka ya kwanta dogon kujera ya lumshe ido, to ita kuma wancan kukan me take a sch, tsaki yyi ya mike xaune ya jinginar da kansa jikin kujera, shi kam kawae wahala aka hadasa da, mikewa yyi ya koma sama ya nufi dakin Batuul, kwance ya sameta kasan dakin tana juye juye tana kuka, tsayawa kallonta yyi da mamaki, shi dae ya shiga uku, karasawa dakin yyi ya durkusa gabanta ya dagota yana kallonta yace "Wae ke kina da hankali kuwa?" Kuka take tana yarfe hannu tana neman kwace kanta daga rikon da yyi mata, jawota yyi jikinsa don xuwa ynxu ta d'aga masa hankali yace "Wae wats wrong with yhu, me ya faru ki gaya min? Talk to me plss, What happen" rufe fuskarta tayi jikinsa tana kuka, ya dago kanta yana kallonta yace "Fateema!" Da kyar tace "Cikina ke man ciwo" yace "Ciki kuma? What did yhu eat at sch" girgixa masa kai tayi ta runtse ido tace "Nothing!" Sae kuma ta fashe da kuka, duk ta rikitasa yace "Wait yana maki haka a gida ne, wani irin magani ake siya maki?" Boye fuskarta tayi jikinsa taki cewa komae sae kuka don ita kadae tasan axaban da take ji, murda kofar dakin aka yi, ae da sauri ya turata ya mike ya koma baya, Ajiddeh ta shigo ta tsaya daga bakin kofar fuskar nan nata daure tana kallonsu, kame kame ya shiga yi yace "Kinga babe wae cikinta ke ciwo kuma taki fadin cause din, nd nd... Wat are we going to do to her then, ko mu tafi clinic?" Ajiddeh ta yatsine fuska tace "Cikinta ke ciwo ko kuma tana Al'ada?" Kallon Ajiddeh ya tsaya yi kafin ya juya ya kalli Batuul da tayi k'asa da kai tana hawaye, Ajiddeh ta watsa mata harara tace "Ko ba jini bane?" Ae Batuul k'asa dagowa tayi, Ajiddeh ta ja tsaki ta fice daga dakin, kallonta Abuturrab ya tsaya yi, ta ki bari su hada ido.
[8/22, 2:24 PM] .: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐
52
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
[8/22, 2:24 PM] .: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐
52
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*