← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 166

Sashe 121

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ammah kam na hawa sama bayan fitansu Abui d'akinta ta wuce kai, Batuul na kwance abinta tana bacci kamar ba itace d'azu ke kukan ba, amma da gani baccin baya mata dad'i, daga gefenta ta zauna tana kallon yanda ta k'ara haske tayi kyau ta rame, hannu ta d'aura saman goshinta taji babu wani zafi, kallon Batuul d'in kawai takeyi tana jin yadda tausayinta ke ratsata, yarinya k'arama da ita amma saida aka samu wani Mara imanin yayi mata wani abin, duniya babu kyau, babu ruwanka da rayuwar mutum amma idonshi yana kan naka rayuwar, in banda rashin adalci da rashin tausayi meye ma Batuul da har za ayi mata asiri, babu komai da izinin Allah sai aikinsu ya lalace, a hankali ta furta "sannu Fatima, Allah ya baki lafiya", sannan ta mik'e ta bud'e closet d'inta ta ciro wani d'an kwalba mai d'auke da ruwan Zamzam ta dawo bakin gadon ta bud'eshi ta tsiyaya kad'an a hannunta ta shafawa Batuul d'in a fuska, wani irin numfashi taja jin ruwan a jikinta, juyawa tayi ta gyara kwanciyarta daga haka taci gaba da baccinta, intercom Ammah ta d'auka ta k'ira d'aya daga cikin masu aikinta, babu b'ata lokaci d'aya daga cikinsu tazo, "inaso ki wanko min Baby cucumber, ki tabbatar ya wanku da vinegar snn ki tafasa fresh milk sai ki jefa cinnamon da cardamom kad'an kada a saka sugar, ki Juyo min a flask, bada dad'ewa ba, snn a d'ora soup d'in offal's", yarinyar dake sanye da uniform d'in cooks tace "okay Ma, za ayi wani abin ne kuma?", Ammah tace "No for now dai babu, ba kun d'ora lunch ba?", yarinyar ta kad'a kai tace "Ehh Ma", Ammah tace "toh shikenan kije ku gama wannan, and be fast", da sauri yarinyar ta amsa ta fice abinta,

Ajiddeh na zaune d'akin Abu duk abin duniya ya taru yayi mata yawa, ta rasa mey ma zatayi taji dad'i, har ga Allah ba son Batuul takeyi ba bare ma a matsayin kishiya amma batason ta zama silar mutuwarta, ko ba kishi musulmace kuma ta san hukuncin kisa kan musulmi, ita inda yadda za ayi kawai ayi koma meye a rabata da gidan amma banda kisan kai, ko haukatata ne ayi, gabanta na fad'uwa take kallon wayan da ta saka silent na ringing, tun d'azu ake k'ira amma ta kasa d'auka, da k'yar ta sa hannu tayi sliding ta kara wayar a kunnenta, tun kamin tayi magana taji muryar Mum na cewa "Dan ubanki tunda yarinyar kanwar uwarkice dole kiqi d'aukan wayata, wlhy Ajiddeh kina jina, kada ki kuskura raina ya b'aci kanki, wani abu ya shiga kanki ne shegiyar yarinya inace akanki nayi sa'ar haihuwa ashe wahalar banza nasha, toh tun wuri kisan abunda kikeyi tun kamin inyi maganinki" Kamar wacce za a jiyo maganan da takeyi tace "Mum mey yayi zafi toh hka, naji kiyi duk yadda kike so amma fa babu ruwana inta mutu, I just want to be happy, yanzu haka mun dawo Nigeria kan ciwon nata muna gidansu Aliyu yanzu haka", kirji Mum ta dafe tace "Naga ta kaina ni Zuwaira, yanzu dan uwarki Ajiddeh kina garin nan shine baki fad'a mana ko kizo gida ba, gidansu miji yafi miki dad'i ko, ina zansa kaina yau dan takaici ni Zuwaira, anya kanki d'aya kuwa Hauwa, lokaci d'aya ki juye ki zama wata sakarya sallamamiya, Wato Bilkisun asirce min keh tayi ko, Ta Allah ba tata ba, duk sai nayi maganinsu daga ita har y'ay'an nata, kuma ki tabbata kinzo gida yau", shiru Ajiddeh tayi tama rasa mey zatace, "Toh" kawai ta iya cewa ta katse wayan, tashi tayi ta fito daga d'akin tayi hanyan d'akin Ammah, saida tayi sallama snn tajiyo muryan Ammah na cewa "Bismillah shigo", tura k'ofan d'akin tayi ta shigah Ammah na zaune kan abin Sallah ta idar da Sallah kenan, waje Ajiddeh ta samu ta zauna tana kallon Batuul dake kwance, takai 5mins kamin ta iya bud'e baki tace "Ammah ya jikin nata?", Ammah ta kalli Batuul dake kwance snn tace "Bacci takeyi tun d'azun, kuma da izinin Allah zataji sauk'i", daga haka basu sake cewa komai d'akin shiru, Farida ce tayi sallama ta shigo, da mamaki ta tsaya kallon Ajiddeh, rabonta da ganinta a d'akin tun satin bikinsu da Yaa Abu, tab'e baki tayi ta k'arasa shigowa, daga gefen Batuul d'in ta zauna tana kallonta da tausayi tace "Ammah ya jikin nata?, ta farka tun bayan fitana?", kai kawai Ammah ta gyad'a mata alamar A'a, Hannu tasa ta kamo na Batuul tace "Allasarki bestfriend , you will get well soon kinji, In sha Allah", tacewa Ammah, "Ammah mu tafi asibiti mana, turawan nan duk ba aikin kirki sukayi ba, a kaita wajen Dr Zakaa tunda gynaecologist ne zai iya duba matsalarta, tunda cikinta take cewa kullum", Har saida Farida tayi shiru kamar baza tace komai ba can tace "Ai ciwon nata bana asibiti bane, Abui sun tafi tahowa da Ashiekh Zai mata addu'a ya gane mana matsalar", k'ululu cikin Ajiddeh yayi k'ara, gani kawai takeyi Ammah tasan abinda ke faruwa, har zufa taji yana tsattsafo mata, Farida tace "Subhanallah, Ammah Jinns ne suka tab'ata?", Ammah tace "tashi kije ki kitchen ki dubamin ko sun gama aikin da na sakasu, kice su hanzarta, banaso ta farka babu komai a kusa", "Toh", Farida tace tasa kai ta fice,
Chapter 121 · 0% Book details