Sashe 101
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lumshe ido yayi bayan ta fita daga d'akin, tunani kawai yakeyi na yadda zai sanar da Ajiddeh Batuul matarsa ce, sai yanzu yake ganin rashin kyautuwar fad'a mata da bai yi ba tun farko, yasan da ya fad'a tun lokacin da duk wani rikici ya kau by now, amma gaba d'aya kanshi a k'ulle yake as of then, yana ce komai zaizo da sauk'i amma yadda yake jin Batuul a ranshi, bazai iya yin nisa da ita ba, not for a second, d'an siririn tsaki yaja ya mik'e ya koma gaban desktop d'inshi yana duba ayyukan da baiyi ba yau a office, kamar wanda aka tsikara ya mik'e ya fita daga d'akin ya shiga d'akin Batuul, har ta canja doguwar rigar dake jikinta ta saka wani d'an bingel d'in gown pink ta baje gashinta kan pillow dan yasha iska, tana kwance ta d'aura Laptop d'inta saman cikinta tana danne danne, wani irin ajiyar zuciya ya sauk'e ganin she is fine, a hankali ta juyo da kanta ganin shine ta maida kallonta ga abinda takeyi, tura k'ofan d'akin yayi ya shigo ya maida ya rufe, daga bakin gadon ya zauna yana kallonta, ya kai wajen 3mins amma ko sau d'aya bata juyo ta kalleshi ba, hannu yasa ya d'auke laptop d'in, sai a lokacin ta d'aga ido ta kalleshi, idanunsu na locking cikin na juna tayi maza ta sadda kanta k'asa ta juya mishi baya, hannu yasa cak ya d'agota yana kallonta yace "are you okay?", kai ta gyad'a mishi ta sulale zata koma ta kwanta ya rik'ota yace "then why are you like this, aman ne har yanzu?", har lokacin batace mishi komai ba sai gyad'a mishi kai da tayi, hannu yasa ya d'ago hab'arta yace "talk to me and stop nodding, wani abun ke damunki?", ganin idonta ya fara ciccikowa yasa yace "stop that, don't you dare drop a tear, tell me mey ke damunki", kamar cewa yayi ta fara kuka ta fashe mishi da wani matsanancin kuka, har cikin ranshi yakejin kukan nata, rintse ido yayi ya janyota jikinshi ya rungumeta, patting bayanta ya shiga yi har saida ya samu tayi shiru, sai ajiyar zuciya take sauk'ewa, a hankali ya d'agota yasa hannu ya share mata d'an guntun hawayen dake fuskanta ya had'e rai yace "Look at me", bata d'ago ba sai da ya sake maimaitawa jin yayi maganar in a serious tone ya sata d'agowa tana ajiyar zuciya yace "Fatima kinada hankali kuwa, keh abin kuka baya miki kad'an, ko don kinga ina k'yaleki kullum sai kinyi kuka, gari baya wayewa ya wuce bakiyi kuka ba, tell me what your exact problem is", ajiyar zuciya ta sauk'e ta zumb'uro mishi baki tace "ni ai ba kullum nakeyi ba sai in kaine ka.....", tsareta yayi da ido yace "ehhn, sai in nine nayi mey?", sadda kanta tayi k'asa tace "You always talk abt your wife, kullum sai kace min your wife your wife, I know she is your wife, but ai ba sai ka dinga tunamin ba", baisan lokacin da dariya ya k'wace mishi ba, dariya ya dinga har sai da abin ya bata haushi, haushin kanta ma taji da ta fad'a mishi hakan, takaicin dariyan da yake yasa taja bargo tayi kwanciyarta, sai da yayi mai isarshi sannan ya d'agota har lokacin yana murmushi, kwace jikinta ta shiga yi zata kwanta amma yaqi saketa, fuskarta ya kamo da duka hannayenshi yana kallon idonta da duk ya cicciko yace "Toh ni yau duk yaushe na ambaci my wife", baki ta zumb'uro mishi tace "ko d'azu ma ba ka....", sai kuma tayi shiru, saketa yayi sannan yace "indai wannan ke saki kuka baza ki sake ji ba, you won't hear that from me okay?, ya hade rai ya ci gaba "but promise me kema baki sake yin kukan, kinga Farida will b coming so banso tazo taga kina wannan koke koken tayi tunanin wani abun ake maki", kamar wata y'ar yarinya ta gyad'a mishi Kai, ajiyar zuciya ya sauk'e ganin yayi convincing d'inta kan kukan nata, yanzu saura Farida, itama sai yayiwa tufkar hanci tun wuri, hannunta ya kamo yace "inason shan kunu, can you make some now?", kai ta gyad'a mishi yayi d'an murmurshi yace "Thank you", tsuke baki tayi zata tashi daga kan gadon yayi saurin janyota yace "Did you just pout?", da sauri ta kad'a mishi kai tace "baka ganiba, ni ba pouting nayi ba", murmushi yayi ya janyota jikinshi sosai ya d'anyi brushing lips d'inshi kan nata yayi mata light kiss, lips d'inta na d'aya daga cikin abinda bazai Iya resisting ba akan Batuul, suke tempting d'inshi yayi abubuwan da ma bai shirya yinsu ba, mik'ewa yayi itama ya mik'ar da ita, kallonta yayi yace "muje?", a hankali tace mishi "Ehh", Hijab d'inta ta d'auka zata saka ya riqe yace "Do you really need to put on this?", kai ta gyad'a mishi kawai taci gaba da saka Hijabinta, ita tayi gaba ya biyota a baya, turus ta tsaya bakin k'ofa ganin mutanen da suka hauro wa sama, kallon mamaki suka tsaya yi mata, wani irin bugawa Ajiddeh taji k'irjinta nayi ganin ya fito daga d'akin Batuul, tun bayan dawowanta bata tab'a tunanin har lokacin yana shiga d'akin ba, baki ta bud'e zatayi magana Jainaba tayi saurin rik'o mata hannu, murmushi ta k'irk'iro tace "Aliyu ashe ana ganinku a gari", shima d'in murmushi yayi yace "ai sai in ba a nemi ganinmu ba Aunty, Ya hanya?" Ya tambaya yana k'arasa fitowa daga d'akin, murmushin nan dai taci gaba dayi tace "Alhamdulillah, hanya mun baroshi, mun sameku lafiya?", kai ya gyad'a yace "Alhamdulillah, ya jikin Mummy, kwanaki bata ji dad'i ba, I wanted going with her", ya nuna Ajiddeh da zuciyarta ke tafasa "but abubuwa held me hear", dariya tasa tace "Ai ba komai ma, ai zuwan Ajiddeh ma yayi,taji sauk'i yanzu sai dai Allah ya kiyaye gaba", "Amin" yace sannan ya juya yana kallon Batuul da ta tsaya daga bayanshi kamar wata munafika yace "baki iya gaisuwa bane kika tsaya kallon mutane?", ido ta d'aga ta kalleshi sannan ta kalli Aunty Jainaba da ta bita da wani shu'umin kallo tana jira ta gaida ta, juyawa tayi ta shige d'aki ta banko musu k'ofa, gaba d'ayansu freezing sukayi ganin abinda Batuul d'in tayi, tsabar mamaki kasa magana Abu yayi, Ajiddeh ce a fusace tayi k'ofar d'akin zata bankad'a Jainaba ta rik'ota, "shegiya karamar matsiyaciya har kin isa ki wulak'anta min y'an uwa, toh koma uban wa ya d'aure miki gindi, ko kuma aka zugoki kizo ki min iskanci ko, toh dama hak'uri nakeyi nake k'yaleki, yau sai kin bar min gida y'ar abu kazan uba", Aunty Jainaba ce ta janyota da k'arfi ta d'an kanne mata ido sannan tace "Haba Ajiddeh, bakya ganin yarinya ce, kema ai kinsan hankali ba isanta yayi ba, yarinta ne ke damunta", wani irin kallo ta jefawa Aliyu da ya kasa cewa komai sai kallonsu yakeyi, a masifance tace "ai dama nasan kai ke d'aure mata tana min abinda taga dama, gashi ka janyo min raini da bai tsaya iya kaina ba, har kan y'an uwana ya koma, toh Allah zamanta ya k'are gidan nan ko kuma ni in bar muku gidan sai kuyi xaman auren da ita", Aunty Jainaba ce ta d'anyi magana a tsawace tace "keh wai wace irin yarinyace Jiddah, haka ake yiwa miji magana dama, wuce mu shige tunda bakida hankali wawiya kawae", taja ta sukayi gaba, wani irin iska mai d'umi ya furzar daga bakinshi yasa yatsunshi cikin gashin kanshi ya bajesu, juyawa yayi ya bud'e d'akin Batuul tana tsaye tana waya da alama da Farida suke wayan, a hankali ta juyo ta dubeshi, sai da y'an hanjin cikinta suka kad'a ganin irin kallon da yake tunkarota dashi, dakewa tayi da k'yar ta bud'e baki tace "Hey hold on, I will call you ltr", bata cire wayan a kunnenta ba taji ya fizge ya jefar kan gado tareda fizgota gabanshi, yana mata wani irin kallo yace "What's d meaning of what you just did, kinada hankali ma kuwa?", babu abinda k'irjinta keyi sai heaving kamar zai fito amma ta dake tace "ni kuma mey nayi?", fizgota ya sakeyi jikinshi yana mata wani irin kallo yace "you are asking, i will slap you yanzun nan in baki min magana ba, meye dalilinki na tafiya ba tareda kin gaidata ba, are you stupid?", k'wace kanta daga rik'on da yayi mata tayi zata matsa daga gabanshi ya kuma fizgota a tsawace yace "kehh! na fara wasa da ke koh, I will right away slap you, bakida hankali ne", hannunshi tacire daga rik'on da yayi mata tace "wai ni mey nayi ne na rashin hankali, dan ban gaishesu ba?, dole ne sai na gaishesu? Naga ai dama ba dole bane gaida kishiya, ita yaushe ta tab'a gaidani? Let me be plss", ta k'arashe maganan tana rolling eyes d'inta cike da masifa, kafeta da ido yayi cike da mamaki, baisan lokacin da gasp yayi escaping lips d'inshi ba jin abinda take ce masa, ci gaba tayi da cewa "kuma ni daga yau na dena gaisheta tunda itama bata gaishenin take ba", daga haka ta juya fuu zata tafi ya fizgota, kankamesa tayi jikinta na rawa tana kiran Anty, murmushi ne ya subce masa jin yadda k'irjinta ke heaving, kana ganinta kasan a tsorace take, yace "Huh kishiya?, waye kishiyar taki, ko kuma kinji nayi declaring d'inki matata ne da har kike fad'in baki gaida kishiyarki?", hawaye ya cika idonta tace "Ai ko bakayi declaring d'ina ba nidai bazan sake gaishesu ba, period", jefata kan gado yayi yace "Fine, duk ranan da ta koreki daga gidanta sai kisan inda kika nufa", da haka ya fita ya barta a d'akin, mikewa tayi a fusace ta sa key a kofarta, k'ofar d'akinshi ya tura ya shiga, nan ya tarar da Ajiddeh da Aunty nata zaune tana mata magana can kasa, d'an tsaki yaja ya koma da baya dan baisan ranar hankalin Ajiddeh ba, duk d'akunan dake gidan nan ta rasa wanda zata shigo da bak'i sai nashi, key d'in mota kawai ya d'auka ya fice daga gidan, bai dawo sai bayan Sallah Isha, direct d'akinshi ya wuce amma har lokacin suna ciki, sai ma dad'a littering d'in d'akin da sukayi da kayayyakinsu, ganin shi ne