← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 166

Sashe 44

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Batuul na gama shirin makaranta tazo yiwa Aunty sallama zata wuce, bayan ta gaidata ne tace "Aunty yau in na tashi daga school zanje gidansu Farida", dagowa Anty ta da sauri tana kallonta tace, "mey zakije yi a gidan?", da mamaki Batuul ta dubi Aunty dan bata tab'a hanata zuwa ba, asalima ita ke sata zuwa ko bata son zuwa, cewa tayi "wajen Farida zanje, nace mata zanzo jiya banje ba shine zani yau" a takaice Anty tace "No ki bar zuwan , some other time kya je, ki dawo gida in kin gama lectures kawae", jiki a sanyaye Batuul tace "toh Aunty na tafi", "Allah ya dawo dake lafiya", a hka ta fita dakin, tana fita k'iran Abdallah ya shigo wayanta, sai da ya kusa katsewa tukunna ta 膹auka, a hankali tace "Hello", wani k'ayataccen murmushi ya saki yace "Habibty hope ba tada ki nayi ba, naji voice 膹inki so low", ce mishi tayi "No am okay, yanxu ma school zanshiga, tun 膹azu na tashi", yace "okay okay durlyn, i will meet you there cux nayi missing cute face 膹inki", ce mishi tayi "toh, sai kazo", ta shige mota ta wuce school. [8/22, 2:04 PM] .: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐 32 By phartiemarhk Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR* Gaba 膹aya ji yayi kanshi yayi mishi nauyi, idonshi ya canja kala ya zama ja har wani gumi ne ya tsatsafo mishi a goshinshi, ya girgiza kai yana ci shiga gaba da ambaton innalillahi wa inna illaihir raji'un, sai da yaji bugun zuciyanshi ya 膹an daidaita tukunna ka kalli Ammah dake hararansa har lkcn ya marairaice murya yace "Ammah ki min rai ki aura min wata daban amma ba Batuul ba, yarinya ce fa karama, kuma kila ma baxa ta rasa saurayin da take so.....," wani irin kallo Ammah ke mishi, hkn yasa ya sunkuyar da kai ya kasa k'arasa maganar, Ammah tace "ko ma dae jaririya ce, ita din muka yi niyyan hada ka da, don nasan xata fi mana babban macen da ka aura, in kuma nuna mana xaka yi ba mu isa ba bismillah, ae dama ka saba daga sanda kayi aure" Runtse ido yyi a hnkli yace "Wane ni Ammah, in'sha Allah yanda ku ka ce hkn xa ayi." jin ya fa膹i haka yasa Ammah sakin fuska ta juya ta kalli Abui tace "dama nasan 膹ana zaimin biyayya, tashi kaje, Allah shi maka albarka, bbu 6ata lkci xa ayi komae don ka koma bakin aikin ka", shafa kanshi tayi tace " Allah maka albarka" da k'yar ya samu ya mik'e daga tsugunen da yake, yayi musu sallama ya fita daga falon, abubuwa ne suka mishi yawa a kanshi, shi ta ina zai fara sanarda Ajiddeh ma aure iyayensa xa su masa, kuma ma matar ba wata bace illa Batuul, yarinyar da bata wuce sha takwas ba tsabar a ja masa raini, me zaiyi da Batuul yarinyar cikinsa? shi if he can clearly remember ma ai Massa ke sonta tun kamin ya bar gari, tunawa da yayi da Massa ne ya sashi saurin ciro wayarshi daga cikin aljihu ya lalubo number shi Massan, dialing biyu ya 膹aga, "dama ana jinka a gari", abunda Massa ya fara fa膹a kenan, share tambayar da Massa ke mishi yayi yace "Kana inane?, inaso mu ha膹u", ya tsaya jin mey Massan zaice mishi, cewa yayi na fita yanxu bana gida but i will b back in an hour", yace "Aii then, zanje gida yanxu before ka dawo zan shiga in gaida Yaa Mera, sai ka dawo 膹in, i need to discuss some issue with you", da haka suka katse wayan, suna gamawa ya mur膹a k'ofan 膹akinshi ya shiga ya 膹auko key 膹in mota ya fito waje, direct hanyan gidansu Massa ya 膹auka, cikin y'an minutes ya isa gidan yayi parking bayan an bu膹e mishi gate ya shiga, Side 膹in Yaa Mera yayi, tayi mamakin ganinshi, dan rabonshi da gidan tun aurenshi da Ajiddeh da yazo yi mata sallama, mamaki shimfi膹e fuskanta tace "Wata sabon gani Babana kaine a gidan nan yau, ashe ka shigo gari", k'arasowa yayi gabanta ya zauna yace " *Yaa Nda dubdo, aaah u' b猫lan amma tusen g猫i*, "ina wuni Yaa, ehhh na shigo amma banma da膹e ba", ya k'arashe maganan da murmushi a fuskanshi, hira sukayi sosai da Yaa har tana ce mishi matarshi dai ba 'a ganinta, har sun manta kamanninta,suna nan zaune Massa ya shigo da sallama, tun daga can ya tsaya k'are ma Abutturab dake gaban Yaa Mera kallo, ba makawa Abu ne sai dai ya 膹an rame, ko meye dalili oho yaci gaba da shigowa abunshi cikin 膹akin, hannu ya mik'awa Abutturab tareda cewa "Man an dena ganinka, rabona dakai fa tunda naje wajenka kamin kazo gida, that is two months after your wedding, i tot baza ka shigo bama sai aure na ai", Yaa Mera ce tace "Abunda na gama fa膹a mishi kenan, nace gashi matar bata haihu ba bare mu muje can suna tunda su sunqi su zo gunmu", sauk'ar da kanshi yayi k'asa dan shima abin nan da yayi na damunshi, gashi nan har yana son zame mishi matsala, Massa ne yasa dariya yace "Kaji ko, ashe su Yaa zaman jiran jikansu suke, sai kayi k'ok'ari ku samo musu kai da Ajiddeh, kaga sai suji da膹in bin naku can garinku mai da膹i da baku son bari", wani kallo ya sakarwa Massa da ya sashi k'ara yin dariya yace "toh ba gaskiya bane", mik'ewa Yaa Mera tayi ta shige daga ciki su kuma suka wuce chamber 膹in Massa, suna shiga 膹akin ya zauna a 膹aya daga cikin kujerun 膹akin tareda mik'e k'afafuwanshi, Massa ya dubeshi yana bu膹e fridge zai 膹auko ruwa yace "wai gajiya kayi ne haka na ganka so slow, ko kuma duk cikin canjawan da kayi ne", wani irin glare ya wurgawa Massa ya tashi daga kwancen da yake ya zauna, k'arasowa Kujeran Massan yayi shima ya zauna tareda mik'awa Abutturab ruwa, karb'a yayi bayan yasha ya rufe ya ajiye bottle 膹in daga gefenshi ya fara msgana kamar haka "Musty, kwanankin baya lokacin biki na kamar naga you showed interest akan yarinyar nan, har yanxu kuna tare ne?", yayi tambayar yana kallonshi, gaba 膹aya kan Massa ya 膹aure dan shi baisan ma wace yarinyar yake tambaya ba, cewa yayi "wacce yarinyar wai, dan ni ban gane wacce kake nufi ba", ce mishi yayi yarinyar nan k'arama mana, yarinyar Aunty", tsaki Massa yaja yace "kaji ka da wani zance, Aunty 膹aya muke da mai k'aramar yarinya, specify inji", shiru yayi ya kasa furta sunan nata, da k'yar ya iya bu膹e bakinshi yace "Batuul", "ohhh dama wai Batuul kake nufi kake ta wannan abin, wait!, dont tell me bakasan zancen aurena ba", da mamaki Abutturab ya dubeshi yace "kayi aurene?", kai ya girgiza yace "No banyi ba but nan da two weeks za ayi", kan Abutturab ne ya 膹aure, yaushe Massa zaiyi aure har bai sani ba, kuma wa zai aura inba Batuul ba, yes ba Batuul bace tunda har su Ammah sukace ya aureta, da sauri ya juya ya dubi Massan da ya zuba mishi ido ganin yadda yake abu kamar ba shi ba yace "Tell me wacece zaka aura inba Batuul ba, kuma ya akayi haka bayan at that time kace min sonta kakeyi", murmushi Massa yayi yace "Toh kai duk mey ya kawo zancen nan, kai da kace mey zanyi da yarinyar tayi k'arama shiyasa na rabu da ita", kai Abutturab ya girgiza yace "c'mon jokes apart, ba wasa nake ba, mesa ka rabu da ita kuma wa zaka aura?", Massa ne yace "Rahama mana zan aura, y'ar Sultan, Batuul tun lokacin ta nuna bata sona shiyasa ma ban kai abun wajensu Ammah ba, but naso in aureta, she will make a good wi.....", wani tsaki Abutturab yaja yace "hold it, okay?", gaba 膹aya ranshi ya b'ace, sai da ya 膹an nutsu tukunna yace "Mustapha am in a problem, kuma babu mai iya fiddani sai kai, kasan auren nan da nayi shekara kenan, kuma su Ammah suna ganin shine ya hanani zuwa inda suke, and ni inason Ajiddeh, like banima da ra'ayin mata biyu, i cant cope, toh 膹azu su Ammah suka tareni da zancen sai na k'ara aure, da nace suyi hak'uri, amma ganin ransu ya b'aci yasa nace na yadda, toh shine da na tambayesu wa suke so in aura, dan ni i have no one in mind shine sukace min wai Batuul", yadda ya k'ira sunan nata kamar ba daga bakinshi sunan ya fito ba yayi maza ya 膹auke idonshi daga kan Massa , dariya Massa yasa harda kyakyatawa ya kwanta akan kujeran, sai da ya gaji dan kanshi ya gama dariyan tukunna ya mik'e ya zauna, Abutturab ko kallonshi baiyi ba har ya gama dariyanshi, sai da yayi shiru tukunna yace mishi "ka maidani 膹an iska ma ko, inyi maka serious magana shine kake dariya", ya k'ara tamke fuska ya tashi zai bar 膹akin, da sauri Massa ya sha gabanshi yace "No baza muyi haka ba, mu koma ka fa膹amin how am i of help dan ni gaba 膹aya zancen ne yazo min a bazata, kaga kuma tunda bazanyi kuka ba ai sai inyi dariya", ya fa膹a yana k'ara smiling, wani siririn tsaki yaja ya koma ya zauna a kujerar da ya tashi, sai da dukkansu biyu suka zauna Massa yace "ina jinka, mey kakeso inyi maka?", shiru yayi ya kasa magana dan baisan ya Massa zai 膹auki zancen ba barema da yace aurenshi nan da sati biyu, iska ya furzar daga bakinshi sannan yace "Inaso kaje kacewa su Ammah kai ke son Batuul, zaka aureta", a razane ya juyo jin abinda Abun ya fa膹i yace "Are you really okay, duk yadda akayi Ajiddeh har brain 膹inka ta tab'a, toh in naje nace musu inasonta sai inyi yaya da ita bayan inada mata", kai ya girgiza yace mishi "ai dama kana sonta, kuma kasha fa膹amin kai baza ka zauna da mata 膹aya ba, and as crowned prince kaga zaka k'ara wata, kaga tunda sooner or later zakayi, y not do it now", kai ya girgiza yace "No way, thats not happening with me, bazanje inyi abunda ban shirya yinshi ba besides ai Batuul 膹in na fa膹a maka da kanta tace min bata sona, kaga there is no way zan auri
Chapter 44 · 0% Book details