Sashe 22
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
K'arfe shida na yamma Aunty ta dawo gida lokacin har Batuul sundawo, a palo ta zauna ta k'irawo wayan Batuul tace mata ta dawo, sauk'owa tayi mata sannu da zuwa, zama tayi daga gefenta tace "Aunty ya gidan bikin", ce mata tayi "lafiya Batuul, masha Allah , gobe zasuje Maiduguri 膹aurin aure, har Baba ma zaije, amma shi sai ranan 膹aurin auren, jibi kenan", baki Batuul ta tab'e tace Allah ya basu zaman lafiya", "Amin" tace sannan tace mata tace "yaushe kuka dawo ne", "tun three thirty suka sauk'eni a gida ita kuma Farida ta wuce gida", ta sake cewa "Aunty maganan admission 膹in nawa kunyi da Baban, time yana wucewa", Aunty ce tace "ni na manta ma Batuul amma yau zamuyi maganan in sha Allah , Allah dai yasa kar in manta, "Amin ta amsa da sannan suka mik'e a tare sukaje yin sallah dan an fara k'ira, Batuul na 膹aki bayan ta idar da sallah ta zauna tana game a Macbook 膹inta, Yusra ce ta shigo tace mata "Yaa Batuul, Mama tana k'iranki tana 膹akinta", cemata tayi "kice ina zuwa", ta juya ta fita, tana fita ta 膹auke Macbook 膹in akan cinyarta ta mayar gefe, mik'ewa tayi tabi bayan Yusra, da sallama ta shiga ta tarar Aunty tana duba abu a closet 膹in kayanta, k'arasawa tayi cikin 膹akin tare da sallama ta zauna aka makeken gadon 膹akin, cewa tayi "Aunty gani", sai da gama dubo kayan da take nema sannan tace wa Batuul "kije ki shirya zamu tafi wushe wushen Aliyu, k'arfe 8 zamu fita, kije maza ki shirya", da sauri Batuul ta 膹ago kanta tana kallon Aunty, ganin Aunty ko noticing kallon da take mata ma batayi ba yasa ta cewa "Aunty wushe wushe kuma, nifa bazan je ba , tun 膹azu ma na fa膹awa Farida, kuma ma ban shirya bafa", ba tare da Aunty ta kalleta ba tace "ki tashi kije shirya, jama'a sai tambayana ina kike akeyi, wasu ma cewa suke ni ke hanaki fitowa bayan halinki ne na k'in jama'a yake hanaki shiga taro, ki tashi kije ki shirya" tana fa膹a mata tana warware laffayan da ta 膹auko, baki Batuul ta zumb'uro ranta a b'ace ta mik'e ta fita, 膹akinta ta isa ta zauna akan gado gaba 膹aya ranta a dagule, toh ita wane kaya ma zata sa , bayan angon ma ba son mutane yake ba shine za ace wani sai anje bikinshi, mik'ewa tayi ta shiga toilet ta watsa ruwa ta fito, zama tayi shafe jikinta da mai sannan ta isa closet 膹in kayanta ta ciro abaya 膹aya a hanga na Al layl mai kyau da purple crystals a jiki ta sa, gashinta ta taje ta k'ara parking 膹inshi sannan ta shafa powder ta saka kwalli a idonta da chappete a bakinta, turarenta masu k'anshi ta fesa ta sauk'o k'asa tana jiran Aunty, Aunty na sauk'o zata cewa 膹aya daga cikin masu aikin ya k'ira mata Batuul ta ganta zaune a palo, ce mata tayi "Batuul bana son iskanci, kina jina, ince kije ki shirya shine zakije ki wani sako min doguwar bak'ar riga, dama naga ranki bai so ba shiyasa dole ki b'ata min rai ko?, toh ki wuce kije ki canza su kuma karki b'ata min lokaci, mik'ewa Batuul tayi tace "Aunty bansan kayan da zan saka bane", "duk kayanki kice min kin rasa na sawa, ba wushe wushe bane, ai kina da dongashua da zaki saka, ki wuce kije ki canja ki dena b'ata min lokaci", rafiya tayi ta haura sama ,kaya ta canja ta saka shadda duck mai blue da bak'i, 膹inkin riga robe da straight skirt, ta 膹auko k'aramin jan gyale ta yafa, ta saka sark'a da 膹an kunne suma ja da abun hannunsu, shoe Rack 膹inta ta nufa ta 膹auki slippers 膹inta louis vuitton mai ja da bak'i ta saka, tayi kyau sosai har ta fi da, sauk'owa tayi, Aunty batace mata komai ba tayi hanyan waje, Batuul ma ta bita a baya, mota Aunty ta bu膹e ta shiga, Batuul ma ta shiga gidan gaba, Fa'iza da ke rike da Aabid suka zauna a baya itada Yusra, Aunty ke tuk'a motan suka 膹au hanyan inda za ayi event 膹in, parking sukayi a wajen parking 膹in motoci , suna fitowa daga mota, sautin ki膹a ke tashi a wajen, tana fitowa daga mota wata rolls royce ta danno kanta wajen, daidai fuskan Batuul motan ya haska, tsayawa tayi mai motan ya gama iskancinshi na haske mata ido sai ta tafi dan bata gani, su Aunty har sunyi gaba sun barta, k'ofan motan aka bu膹e, iska ne ya buso mata k'anshi turaren, kanta ta 膹ago dan tasan mai turaren, kashen wutan motar akayi tana 膹aga ido, fuskan Abutturab idonta ya sauk'a akai, ba ka膹an ba yayi kyau, kaftan sky blue ya saka, yayi kyau sosai, shades 膹in ray ban ne mak'ale a idonshi, gani tayi yana tahowa hanyanta, tsayawa tayi ta kasa motsi sai bugun da zuciya ya fara
Aunty(Mama) haka k'annen Batuul ke k'iranta 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐
19
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Aunty(Mama) haka k'annen Batuul ke k'iranta 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐
19
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*