Sashe 104
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Washe gari da asuba bayan yayi Sallah direct airport ya wuce d'aukan Farida, arrivals ya wuce kai tsaye bayan ya gama parking, dai dai lokacin da Farida ta fito daga terminal janye da akwatinta, ita ta fara hangoshi, da gudu ta k'araso ta rungumeshi, shima d'in rungumeta yayi, cike da farin cikin ganinsa tace "Yaa Abu ina kwana, thought tare xa ku xo da Anty Batuul" da xolaya ta kare maganan da wide smile d'inta mai kyau shimfid'e fuskarta, murmushin shima yayi yace "Lafiya Alhamdulillah, Ya hanya?", zumb'uro mishi baki tayi jin yace ya hanya tace "hmmmm ai ni shiyasa bana son bin wani flight inba B.A ba ko Emirates, kasan transit kawai muka tsaya amma suka fake da wani wai bad weather, baza mu taso ba sai bayan nan da 14hrs , ni ai da so nayi in koma Nigeria, amma sabida ina son ganin my other half", ta wani lumshe ido tana d'aura duka hannayenta biyu a k'irji tace "Allah dan ita kad'ai na yadda na k'araso, kuma kasan wani abu......", bai barta ta k'arasa ba yace "Let's get going, d'an wannan surutun naki zamu kwana nan baki gama ba", suna tafiya yake tambayanta Yasu Ammah da kowa a gida, kamar jira takeyi ta dinga mishi zuba, wasu abubuwanma ba ji yakeyi ba har suka isa inda yayi parking mota, butt ya bud'e mata ta saka jakarta a ciki, sannan ta xagayo ta zauna, sai da ya tada motar suna tafiya sannan ya juyo ya dubeta yace "kina jina?", gaba d'aya hankalinta ta tattaro ta kalleshi jin yana mata magana, yaci gaba da cewa "Babu ruwanki da duk wani abu da zaki gani in mun je, Ajiddeh isn't aware Batuul is my wife", a firgice ta kalleshi tace "What?", kallonta yayi ya wani hade rai yace "Yeah you heard me right, dan haka babu ruwanki da duk abinda ke faruwa cikin gidan, am repeating it, don't try anything stupid like you did last time, babu ruwanki da Ajiddeh", tabe baki tayi ta kauda kai, yace " Baki da hankali ina maki magana kina dauke min kai" xumburo baki tayi ta gyad'a mishi kai alamar ta ji, ya hade rai sosai yace "bakida bakine?", ta dan murguda baki tace "Toh naji mana", kwafa yayi ya ci gaba da driving dinsa, ta d'auke kai ta juya tana kallon window, ranta ne taji ya baci ba k'adan ba wai Ajiddeh batasan Batuul matarsa bace, toh does that mean they weren't intimate ko me, shine har Ammah ta fara lissafin jikoki, "Chabdi" ta fad'a a ranta ba tare da tasan ya fito fili ba, juyowa yayi yana kallonta yace "kikace meye?", maza tayi ta kad'a mishi kai tace "No ni bance komai ba", ya harareta ya maida hankalinsa kan driving din da yake,farida taci gaba da sak'e sak'enta, a ranta tace masifaffe wai wani I shouldn't try anything stupid, tabdi ai kuwa wlhy sai dai in wannan matar tasa mai kama da bishiyar gwanda sai tsawo babu shape tayi hankali itama, dan indai ta tab'ani ba yadda za ayi in k'yaleta wlhy sai na rama, kuma sai nasan ynda nayi tasan wacece Batuul, "kutt, ai wlhy bama zai yiwu ba", batasan a fili tayi maganar ba saida taga yayi parking yana mata wani irin kallo yace "meye d'in ne bazai yiwu ba?", da sauri ta shiga girgiza mishi kai a rikice tace "I wasn't talking to you fa", ya jima yana kallonta fuskarsa daure kafin yayi k'wafa ya ci gaba da driving, bata kuma gigin wani tunanin ba bare har ya fito fili, kamin su isa har gari ya washe, bayan yayi parking kamin ta fito in a serious tone yace mata "hope you heard all I said clear?", kai kawai take girgiza mishi dan ita ta matsu taga Batuul, yana bud'ewa ta fita guje ta shige gidan, tun daga bakin k'ofa ta fara ihun "His beloved, His First Lady, kina ina na iso", A guje Batuul dake kitchen ta d'an samu karfi tana gyare gyaren kitchen din ta fito jin muryar Farida, Ajiddeh da Aunty dake d'aki ma fitowa sukayi lokaci d'aya ganin wake ihun, Abu kam mamakin Farida ne ya cikashi jin abinda take fad'i, ya k'asa karasawa parlorn, ita ko ta tafi da gudu suka rungume juna da Batuul cike da murnan ganin juna, farida ta tura Batuul daga jikinta tana kare mata kallo ta wara ido har da d'an tsallanta tace "Waoww waow, yayana ya iya kiwo wllh, kinga yanda kika yi wani fresh kika yi kyau kuwa love, OMG" wani tsawa da ya rikita ta daga ita har Batuul din Abuturrab ya daka mata.
馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐
70
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐
70
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*