Sashe 146
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da yamma suna zaune garden itada da Farida da take ta mata iya shege kan ta k'ara k'iba, bata kulata ba dan Yaa Abu ya fad'a mata babu wani k'iba da ta k'ara, gaba d'aya hankalinta yana kan fruit Bump game d'in da take bugawa, Juyo mata da Macbook d'in dake kan cinyarta Farida tayi tace "Kinga nacewa Affan in zaizo ya taho min da wannan cradle d'in, its cute ai ko?", sai a sannan ta d'ago ta kalli cradle mai kyau dashi snn ta kalli Farida with confusion fuskarta tace "Huh?, cradle nefa, kwana zaki koma yi kai?", Farida ta d'ago ta dubeta tayi mata kallon you ain't okay ta girgiza kai snn tace "Babynmu na siyawa, the newest niece/ Nephew, kinga fa unisex nace ma tunda bansan mey zaki haifa ba, Dan Allah kicewa Yaa Abu kuje a duba cuz in san irin kayan da zan riqa keeping", ta fad'a with soo much excitement a muryarta, Sai lokacin Batuul ta fahimci ina ta dosa ta tsuke fuska tace "Ni nace miki zan haihu toh?", Farida ta kyalkyale da wani irin dariya da ya bawa Batuul haushi tace "Wake jiran sai kin fad'a mishi, tun da naje wajenki UK na gano, shiru kawai nayi maki ina kallonki kawai", Jin ambaton sunan UK ta tuna da Ajiddeh, jiki a sanyaye tace "tun yaushe ne bata nan, ni tunda naji sauk'i ban ganta ba", ba tareda ta dubeta ba Farida tace "Wa kenan?", a hankali Batuul ta furta Ajiddeh, kafad'a Farida ta d'aga tace "Oho, da yake she is not my cup of slush", Batuul ta dawo kusa da Farida tana k'ok'arin rufe System d'in tace "Riri mana, dagaske fa nake, she was nice to me da banida lafiya, har Addu'a fa tayimin", wani irin kallo Farida tayi mata, kallon lallai you are not okay, har ta bud'e baki zatayi magana ta fasa, ta sake janyo System d'in zata bud'e, Batuul tayi maza ta riqe tace "dagaske nake I could remember everything har da kukanta, she insisted mu dawo fa ayi min magani a nan, amma tunda na warke ban ganta ba, kuma d'azu naji Abu na cewa bayason ganinta cuz bayason taking decision out of anger, mey ya sameta Dan Allah?", Sai yanzu Farida ta tabbatar da Lallai Batuul batasan mey ke faruwa, kuma baza taji daga bakinta ba, gyara zamanta tayi tana fuskantar Batuul da kyau kamar wacce zatayi wani maganan kirki tace "Kina jina dai koh?", Batuul ma ta gyara zama dan ta fad'a mata, Farida taci gaba "Naga kin fi kusa da Yaaa Abu, just ask him about her, baza kiji daga bakina ba", had'e rai Batuul tayi tareda kaiwa Faridar duka a kafad'a tace "You are a jerk Allah, shine kika b'atamin lokaci kamar wacce zata fad'i abin kirki", mtewww taja tsaki daidai lokacin wayanta ya hau ringing, dubawa taga unknown number ne, har baza ta d'auka sai kuma ta fasa tayi recieving tasa a kune, cikin masculine voice d'inshi taji yace "Are you ready?", lumshe ido tayi ta bud'e tareda cire wayar聽 ta sake kallon screen d'in da kyau snn ta maida kunne tace "Hello?", yace "Glitter you there?", a hankali cikin siririyar murya tace "Inace fa sai dare zamu tafi kuma", yace "Nah get ready yanzu zanzo mu tafi kinji?", tace "Okay", yace "Yeah sai na k'araso, take care", a hankali ta lumshe ido, this is the first time Yaaa Abu ya k'irata, ko ina ya samu number d'inta, ko dai dama yana dashi ne, kauda tunanin tayi ta d'ago taga Farida ta kafeta da ido tana wani irin smirk tace "And you will later tell me kefa baki iya soyayya ba, dubi yadda kika wani kashe murya kina magana, badan shegen son jin gulmana ba da bazanji ma mey kike cewa ba", Harararta Batuul tayi ta mik'e tace "You have a problem these days kin sani ko, ni matsa min in tafi, kya ji dashi, I pity best friend", ta fad'a tana mik'ewa zata bar wajen, da sauri ta ajiye Macbook d'in hannunta ta biyota tana dariya tace "exactly why he can't do with me", tsaki Batuul taja taci gaba da tafiya abinta Farida na biye da ita tana ta zuba, ko da suka shigo a parlour suka tarar da Ammah, Ammah tace "Bitti badai baki shirya ba kam, inace da yamma yace zaku fita", sauk'ar da kai tayi k'asa tace "Shine nazo in shirya yanzu Ammah", Ammah tace "Toh shikenan" Farida tace "Ohhh ashe fita zakiyi shine kike shamin k'anshi dan kada in biki, toh nikam sai naje bara inje in shirya nima", dariya kawai Batuul tayi dan tasan in ta biyewa Farida sai ta hanata shiryawar ma gaba d'aya, tana shiga d'aki ta fad'a toilet tayi wanka snn ta fito, akwatin da Farida ta shigo dashi d'azu ta bud'e ta ciro wani swiss voile purple had'e da underwears suma purple, saida ta shafa mai snn ta saka kayan, turarukanshi dake gaban vanity table d'in ta fesa wad'anda taji sun kwanta mata, Farida na zaune parlour suna hira da Ammah wayarta tayi ringing, da sauri ta d'aga ganin Yaa Abu rubuce jiki takai kunnenta tace "Hello Yaa Abu ina wuni", bai amsa ba sai cewa da yayi "Kina jina?", ta kad'a kai tareda cewa "Ehhh", yace "Har ta gama shiryawan ne?", sarai tasan wacce yake nufi amma ta dake tace "waye kenen?", yace "I mean Fatima, ta shirya ne?", daga yadda yayi maganan tana jiyo how stern muryarshi take, murmushi tayi tace "Yeah ta dai hau sama shiryawa, inaga ta gama by now", yace "ita kad'ai ce saman nan ko?", kamin tayi magana yace "Anyway, kina jina koh?, inaso ne ki taimaka mata ki shiryamin ita yadda duk wannan ramar da tayi zata koma, I mean she should look all presentable, har wannan make up d'in naku na mata if possible kiyi mata", murmushi kawai takeyi tace "Tohh Yaa Abu, lemme check on her rn", ya sauk'e ajiyar zuciya yace "Okay Plss do, Thank you" cikeda da murna yau Yaa Abu yace mata Thank you ta ajiye wayan ta dubi Ammah tace "Wai Yaa Abu ne yace in taimaka wa Batuul ta shirya", batareda ta kalleta ba Ammah tace "Toh shine kike zaune?", mik'ewa tayi ta haura sama ta tura k'ofar d'akin da tasan Batuul na ciki, gaban vanity table ta tarar da ita zaune tana faman taje dogon gashinta da yake gajiya mata da hannu, hannu tasa ta anshi comb d'in tana cewa "Kedai har yanzu baza ki fara retouching ba", bakinta ta tsuke dan in da abinda ta tsana bai wuce a tab'a mata gashi ba ace za ayi mata kitso ko taji amma da yake yanzu yana bata wahala babu yadda ta iya, dariya Farida tayi tace "Hey chill!, bafa ni na kar zomon ba, rataya aka bani, start retouching zaki bar k'uncin nan da kikeyi yanzu", d'an tsaki taja tace "Nikam kiyi shiru ki tajemin", haka ta gama taje mata tayi bun dashi ta baya snn tacewa Batuul "ina zuwa", ta fita daga d'akin bata dad'e ba ta dawo riqe da Makeup kit kan madubin ta fara jera komai, Batuul ta dubeta da kyau tace "You also going", Farida ta kad'a kai tace "Nah, ke zanyi wa d'an touch up", Batuul ta yatsina fuska tace "dayake nace miki inason yi koh", Farida tace "Nifa am trying to help, babu ruwana in kukaje yaga y'anmata masu kyau wajen, kuma kinsan dukkansu y'an matan nan yanzu abinda sukeyi kenan ko", da kyau Batuul ke kallon Farida gabanta na fad'uwa jin abinda take cewa, gyara zama tayi kan stool d'in tace "Toh kiyi min", murmushi kawai Farida tayi tazo ta fara shafe shafe fuskar Batuul, d'an touch up tayi mata da ya k'ara fito da kyan Batuul d'in snn ta fita, bata jima da Fita ba taji an turo k'ofar d'akin, batareda ta damu ta juyo taga waye ba taci gaba da rataya towel d'in da take ratayawa, shikam tun daga corridor yakejin k'anshin turaruka masu dad'i, ido ya lumshe ya bud'e ganinta tsaye tana k'ok'arin rataye towel, a hankali ya shigo d'akin ya rungumeta ta baya tareda sauk'e ajiyar Zuciya, itama abinda tayi kenan jin k'anshin shi da d'umi jikinshi, ajiye towel d'in tayi dan yana neman fad'uwa jin d'umin lips d'inshi a wuyarta tana jin sauk'ar numfashinshi, a hankali ya juyo da ita tana fuskantarshi idonshi na zagaye ko wane angle d'in fuskan, hab'arta ya d'ago yace "Kinyi kyau Glitter", duk da rashin haskenta zaka iya ganin blush d'in da Farida ta shafa mata na dad'a turuwa, a hankali tace "Thank you, kaima ai kayi kyau", hannu yasa ya lakuto purple ombre lipstick d'in da aka shafa mata yana yatsina fuska yace "wa yace mata ta shafa miki wannan?, I can't take wani ya kallemin keh har idonshi ya kai kan lips d'inki", kamin tace wani abu ya sunkuya ya had'e bakinsu waje d'aya, sai da ya tabbatar ya tsotse dukan lipstick snn ya saketa yana maida numfashi raurau tayi da ido tace "ka b'ata min fa kenan", ya rik'o hannunta yace "Na gyara dai, ni kad'ai za ayiwa irin wannan kwalliya ba in zamu fita ba", agogon shi k'irar Hublot ya duba yace "Glitter muje, its getting late", ya mik'o mata mayafinta dake ajiye kan gadon, sauka sukayi k'asa har lokacin Ammah na zaune falo, tana ganin Batuul tace "Masha Allah Bitti, ya babu d'an kunne kuma bare sarqa, Farida maza jeki ki d'auko mata d'akina", Da hanzari Farida ta tashi taje ta d'auko wani gold chain da earring d'insu da agogo, ita ta taimaka mata ta saka Ammah tace "Masha Allah, yayi daidai yanzu, ki gaida min su in kinje Bitti", ta amsa da toh dukda batasan inda zasun ba, ta kalli Farida tace "Muje mana?", Farida tace "Wa zai biku?, keda ma bakisan inda zaku ba, marairaice mata tayi tace "I have assignment kuma gobe zanyi submitting, kuje kawai sai kun dawo", juyawa kawai tayi ta bi bayan Abu, shi ya bud'e mata k'ofar mota snn ya zagaya side d'inshi ya shiga ya tada motar, hira sosai ya dinga yi mata yana driving, har mamakinshi takeyi yadda yake ta magana, gidan Yaa Mera suka fara Zuwa, basu wani jima ba suka yi mata sallama suka tafi