← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 166

Sashe 149

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Cikin gida ta koma kai tsaye ta wuce kitchen tana kokarin mance duk abinda ta gama ji yamzun, Freezer ta bud'e ta ciro wani babban rubber assorted ne soye ciki duk sunyi block, plate ta d'auka ta d'ibi kad'an ta saka ciki snn ta saka a micro wave zatayi warming, kan freezer ta koma ta zauna bayan ta ciro ta d'auki fork tana cin kayan cikin, ta Bawa dake wanke fruits tace "Yaa Batuul naga baki nemi yaji ba kuma akwai su iri iri", Batuul ta d'an yatsina fuska tace "Aunty ta Bawa kinsan a can bamuyi wani aikin nama ba, masallaci kawai mukaje muka dawo, ya dai yi mana yanka", Ta bawa ta riqe baki tace "kai haba, toh ina aka kai ragunan?", Batuul ta tab'e baki tace "Ehhhm, Sadaka akeyi dashi kasashen mabuk'ata", "Ahhh lallai an gaisheku, ai koda za ayi sadaka ba duka ba, nan gaba kice a bar miki naki ko nan kya turo na gyara miki in aikace shi, wa yace duka ake sadakar?", Batuul tayi dariya tace "Toh shikenan", ta dubi Janet dake ta faman goge plates d'in da ta wanke tace "Janet miqo min yajin na tafarnuwa, da sauri ta kawo mata shi ta koma bakin aikinta, tana zaune tana ci Aunty ta dawo kitchen d'in taga Batuul zaune kan freezer tana take
kayan ciki tace "har ya tafi?", kai ta gyad'a tareda amsawa bayan ta cinye wanda yake bakinta, Aunty tace "in kin gama ki sameni sama", Aunty bata gama bama ta sauk'o kan freezer tana ajiye plate d'in ta biyo bayan Aunty, sosai sukayi having mother daughter time d'insu, ta bata addu'o'i da shawarwari masu kyau, tace ta shiga tayi wanka bayan ta had'a mata ruwan da sinadarai masu yawa, bayan ta fito ta taga wata da ganinta y'ar Tchad ce zaune, gyaran jiki Aunty tasa matar nan tayiwa Batuul tayi mata, cikin lokaci kad'an Batuul ta canja sai shek'i takeyi, saida aka gama suka sauk'o dining cin abinci, sai lokacin taga Baba da y'an k'annenta, da murna shima ta rungumeshi, koda zata fara mishi shagwab'a wayo yayi mata yace ai ta girma yanzu sai dai su Yusra suyi, haka suka zauna cin abinci murna fal ranta, har wani emotionally ta rik'a ji a ranta, bayan sun gama cin abinci mai gyaran nan kuma. tayi mata kitso, k'arfe goma daidai ya dawo, tun da ya shigo gidan idonshi ke kanta, babu abinda yake furtawa cikin ranshi sai "Subhanallah, Masha Allah cikin ranshi", har ya k'araso cikin parlour, da murmushinta mai kyau ta juyo ta dubeshi, a nutse suka gaisa da Baba ya sake gaida Aunty, yaran ma dukkansu suka gaisheshi, a nan yake sanar da Baba gobe sha d'aya jirginsu zai tashi, Albarka Baba yayi ta saka musu tareda Nasihohi, Aunty ta cikata da abubuwa dayawa da wasu ma bata san amfaninsu ba, kamar kar ta tafi haka tayi sallama dasu suka wuce, yana barin compound d'in gidan yayi parking gefen titi ya ciro wayarshi yana haskata yace "Glitter kinyi kyau da yawa", murmushi tayi tace "Aunty tasa aka min duka, kaga har kitso anyi min", ta cire d'an kwalinta tareda nuna mishi sabon kitson nata, gaba d'aya motar k'anshinta mai dad'i yakeyi, hannu yakai yana shafa kitson yana lumshe ido a hankali ya dunga furta wasu addu'o'i da shikad'i yakeji snn ya bud'e idon yace "Glitter plss ki tayani addu'a ki haifa min Baby girl mai kama dake", tayi dariya tace "nikam baby boy nakeso, kaga I want to name him after this fav name" hararanta yayi yace "wane sunane favorite d'in naki?", batareda tunanin komai ba tace "I have loved the name tun ina yarinya, I wanted marrying someone with such a name ko kuma in haifi mai sunan, I just have a thing for the name ALIYU", ta fad'a kanta tsaye, ajiyar zuciya ya sauk'e jin sunan da ta ambata, sai da ta ambata ta tuna mey ya fito daga bakinta, ta tun. a shima fa sunanshi kenan, ido ta rintse tana dariya, hannu yasa yana cupping fuskarta yace "Every Aliyu have his own Fatima, it happened you are mine, I can't imagine life without you now, I love you", itama tayi murmushi tace "I love you too", da haka yaja mota sukayi gida, koda suka isa har Ammah tasa an gama shirya musu kaya, d'an hira suka tab'a snn sukayi sama suka kwanta, washe gari tunda suka tashi da asuba basu koma sun kwanta ba har suka gama shirin tafiya, 9 Sadiq ya fita dasu airport, Batuul dai sai kallon ikon Allah takeyi jin babu mai zancen Ajiddeh, Sadiq na dropping d'insu bai jima ba ya juyo, duk motsin da zatayi idonshi yana kanta, candy floss ta hango wani d'an yaro naci, a hankali ta juyo ta dubeshi tace "Yaa Abu inaso", ya kalleta yaga inda take kallo yace "we should go nd get", tayi raurau da fuska tace "Nifa na gaji, ka samomin kai zan jiraka a nan, in na tashi zan gaji dayawa", yayi murmushi tareda lakuce mata hanci yace "okay take care, bara inje duty free nan in duba", har ya juya yaji tace "da spicy French fries plss", murmushi yayi mata kawai ya tafi, baifi five minutes da tafiya ba ya dawo, baisan lokacin da murmushi ya k'wace mishi ba ganinta zaune k'ark'ashin wasu manan rose Petals a wani perfume stall, sosai tayi kyau sbd kayan dake jikinta suma pink ne, abubuwan dake hannunshi ya ajiye ya ciro wayarshi daga aljihu yayi snapping d'inta pictures batareda ta lura ba, har ya isa wajenta yana murmushi, gabanta ya tsuguna tareda mik'a mata floss d'in, da wide smile ta karb'a tayi mishi mouthing "Thank you", kai ya girgiza mata yana nuna mata cheeks d'inshi, wara ido tayi tana blushing tana girgiza mishi kai, baza ta iya ba, kunyan shi duk ya gama cikata, ganin taqi yi ya zumb'uro mishi bakinshi ya miqe zai bar wajen, hannu tasa ta riqoshi, saida yayi murmushi snn ya juyo yana kallonta, a hankali tace "da mutane anan, in munje gida pls", hannunshi zai sake karb'a tace "toh close your eyes", lumshe ido yayi a hankali ta dawo gabanshi, d'age tayi sbd tsawonshi, ji tayi ya d'aura hannu waist d'inta ya d'agata sama, pecking kumatunshi duka biyu snn ta maida kanta ta sinnewa jikinshi, tafi taji duka wajen ya d'auka, tsabar kunya kasa d'agowa tayi, tana jikinshi ya mayar dasu wajensu sukayi zamansu, 11 daidai sukayi boarding jirgi, in banda bacci babu abinda takeyi, lokaci lokaci take tashi, murmushi kawai zai mata ko kuma ya tambayeta in tana da buk'atar wani abin, har suka isa UK
[18:48, 12/22/2017] 鈥�+234 806 969 9042鈥�: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

96

By Phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Chapter 149 · 0% Book details