← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 166

Sashe 65

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Kan abin sallah ta zauna tayi jigum bayan ta idar da sallah, akwatinta da wayarta ke ciki ta hango daga gefe, bata san ma ko yaushe aka shigo dashi ba, da murna ta tashi ta isa ta bu膹e akwatin, wayarta dake ciki ta ciro ta kunna, ganin layin dake ciki yasa jikinta yin sanyi ta koma bakin gadon ta zauna, yanxu sai ta sayi sabon layi kenan, 膹an tsaki tayi ta jefa wayan kan gado, tana missing gida, tana son tayi magana da Aunty da kowa ma, hawaye ne ya fara gangarowa daga idonta, tunanin roaming ne ya fa膹o mata, da hanzari ta mik'e tana dariya ta 膹auko wayar daga kan gado, babu b'ata lokaci tayi roaming, da murmushi a fuskanta ta shiga dialing Aunty, kamar jira akeyi aka 膹auki wayan, da murna tace "Hello Aunty ina kwana", ajiyar zuciya Aunty ta sauk'e daga 膹aya b'angaren har Batuul na jiyowa tace "Lafiya Batuul, halan yanxu kika tashi daga bacci naji kina kwana", dariya Batuul tayi tana goge hawayen idonta tace "A ah Aunty, garin ne kamar safiya shiyasa nace kwana, yanxu nayi azahar ma", Aunty tace, "yayi kyau Batuul, tun 膹azu ma muke trying number ki baya shiga, Su Mahir sai damuna suke a k'ira musu ke", kukan dake shirin fitowa ta maida jin abinda Aunty ta fa膹a mata tace "Allah sarki Aunty suna ina, a basu mu gaisa", Aunty tace "sunyi bacci Batuul tun 膹azu, sai dai gobe in basu ku gaisa", kai ta ka膹a kamar Aunty na ganinta, Aunty tace mata "Batuul kun isa lafiya babu matsala ko, ina y'ar uwar taki", wani iri taji maganan Aunty, wai har itama cewa take Ajiddeh y'ar uwartace, dan batasan mey ya gama faruwa bane bama yau da safe, sai da Aunty ta sake maimaita tambayan jin tayi shiru, a hankali tace "Aunty tana lafiya, ai tana 膹akinta", Aunty tace "yayi kyau Batuul, in kin huta zamuyi waya kinji, inason muyi magana", Batuul tace "Toh Aunty, Baba fa, yana gida?", Aunty tace gashi nan Batuul, tayi rau rau da ido tace "Aunty shine baice zaiyi magana dani ba", Aunty tayi dariya tace "ai gashi nan fa膹a mishi da kanki", kamar zatayi kuka bayan Aunty ta mik'awa Baba wayan tace "HellO Baa, nda dubdo", da murmushin shi na manya yace "Mamana nda dubdo, ya sabon waje", a hankali tace "Baa Alhamdulillah", yace "Masha Allah Batuul, Allah yayi miki albarka, ki kula da ibadunki, ki girmama na gaba dake kinji, babu ruwanki da tsokana ko tadawa mijinki hankali, ki zama mai biyayya kuma kiyi ta hkuri kinji, Allah ya taimaka", tana kuka da k'yar ta iya bu膹e baki tace "In sha Allah Baa, nagode", da haka suka katse k'iran, kuka sosai ta sa bayan sun gama wayan, shikenan rayuwanta ya canja kenan, ta dde xaune ganin yunwa ya dameta don har uku na rana yyi yasa ta mike a hnkli da Hijab jikinta ta tura kofan dakin ta fito, downstairs ta nufa a xuciyarta tana addu'an Allah yasa Ajiddeh bata nn, xaune ta sameta falon tana kallo tana cin sauran pizzan ta, duk irin faduwar da gabanta yyi hkn bae sa ta koma ba, cikin natsuwa ta tako har cikin falon ta kalleta a hnkli tana ci gaba da tafiya tace "Ina yini Anty?" Wani matsiyacin kallo Ajiddeh ta bi ta da shi har ta shiga kitchen din, snn ta mike, sae da ta fara kallon stairs snn ta bi ta cikin kitchen dib, Batuul na tsaye tsoro ya cikata don xuciyarta ya bata sae ta biyota, lallai tayi gangancin sakkowa Ajiddeh na falo, daga bakin kofa ta tsaya tana kallonta tana murmushin rainin hankali tace "Ke a tunanin ki kin samu gun xama a gidana koh? To yhu are mistaken yarinya, don sae kin gwammace da baki shigo gidana da sunan xama kiyi karatu ba, banda kinibibi, gulma, da munafurci irin na iyayen ki sun san basu da halin kama maki hostel me xae kai su karambanin turo ki UK karatu, shine xa a wani xo a daura ma miji na nauyi da wahala to wllh kun yi kadan, duk uban da ma ya kawo wnn shawarar zae saketa ne, don sae sai kin gwammace da titi kike kwana kan gidana, makwadaita kawae" Ae Batuul bata san lkcn da ta fashe da kuka jin xagi da cin fuskar da Ajiddeh ke ma iyayenta, ita din ba mai son fada bace bare ta mayar mata da martani, durkushewa gurin tayi ta dinga kukan takaici da tausayin rayuwarta, ran Ajiddeh yyi fari don har da murmushinta, ta cigaba daga inda ta tsaya.
Chapter 65 · 0% Book details