Sashe 134
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Yana komawa d'aki ya d'auki Batuul cak a hannunshi ya rungume ya fito da ita, ganinshi riqe da Batuul Ammah ta tambayeshi "lafiya ka d'aukota, ko ta tashi ne?", kai ya kad'a mata yace "Inaso ne ta huta a saman" snn ya k'ira Farida ta biyoshi, yana shiga d'akinshi ya kwantar da ita kan gado, dai dai nan Farida ma ta shigo, yace "Je ki samo mata kaya mara nauyi, I want her to change", kai ta kad'a mishi tace "okay", ta fice, ya kurawa fuskan Batuul ido y'ana kallonta a hankali ya kamo siraran yatsunta ya kai bakinshi ya manna mata kiss yace "I love you Batuul", kamar taji abinda ya fad'a a hankali ta bud'e ido ta kalleshi, ido ya lumshe ya bud'e yana so ya tabbatar dagaske ta farka, da sauri ya matso yana riqeta yace "Alhamdulillah, am glad kin farka", murmushi tayi mishi ta shiga k'okarin tashi ta zauna, shima d'in murmushin yayi mata ya rungumeta jikinshi yana lumshe ido yana shak'ar k'anshinta da yakeso a koda yaushe, jin yaqi saketa yasa ta d'an turashi, ya d'agata daga jikinshi yana kallon fuskanta, hawaye ya gani cike da idonta kuma har lokacin da murmushinta a fuska ta k'arewa d'akin kallo tace "Yaa Abu inane nan?", ya dad'a matso da ita kan cinyarshi yace "Cry no more kinji, baza ki sake kuka ba sai na farin ciki In sha Allah, We are home, and you will be safe here in sha Allah", Farida ce ta shigo riqe da kaya a hannunta, watsar da kayan tayi ta fasa ihu ta hawo kan gadon ta k'ank'ame Batuul tace "Alhamdulillah, omg Batuul am happy kin warke, don't fall sick Dan Allah kinji?", sai kuma ta fashe da kuka, Abu ya kalleta yace "Keh mey haka, kin shigo kina ihu, ina aiken da nayi miki?", Farida ta cunno baki tace "Yaa Abu am just happy my friend is well again", Batuul tayi murmushi ta kamo hannunta tace "Yeah Alhamdulillah, am feeling much better now, Ammah fa", zata bata amsa yace mata "Leave", ta zumb'uro baki ta sauk'o daga kan gadon, Batuul ta kalleshi da idanunta da sukayi raurau tace "Yaa Abu mana, let her stay", bai kulata ba ya sake kallon Faridan data fita kamar mai shirin karya k'ofan, ya kalleta yace "Baby you hungry ko?", kai ta girgiza mishi, hancinta ya d'an ja yace "Nasan kina jin yunwa, and my lil champ too", ya kai hannu kan mararta, sam ta manta da wani ciki a jikinta sai yanzu, murmushi kawai tayi mishi, yace "Let's freshen you up, sai kici abinci", tace "Ni bacci zanyi, am not hungry", tashi yayi ya tattare kayan da Farida ta watsar snn ya dawo kan gadon ya shiga k'ok'arin cire mata kaya, hannunshi ta riqe tace "Zan cirefa", kamar baiji mai take cewa ba yaci gaba da abinda yakeyi, cak ya d'agata yayi toilet da ita, wanka yayi mata tayi brush snn tayi alwala ya d'aukota suka fito, shi ya shiryata ya canja mata kaya, a lokacin Ammah da masu aikinta suka shigo da abinci, ba abin mamaki bane dan tasan irin son da Ammah ke yi mata tun kamin ta auri d'anta, ranan ko Sallah Abu bai fita ba a d'aki yake yinshi ya jasu jam'i, lokaci lokaci Ammah ke shigowa dubata, da daddare ma shi yayi mata wanka ya shiryata cikin kayan bacci snn ya tofa mata addu'a tareda ja mata bargo,wutan d'akin ya kashe ya jawota jikinshi yayi pecking lips d'inta yace "Have a sound sleep Haya", sake shigewa jikinshi tayi, a hankali kamar mai rad'a tace "Ban ganta ba duka yau?, ina ta tafi?, kamar baiji abinda tace ba ya dad'a gyara mata kwanciya yace "You need rest, kiyi bacci", sake maimaita mishi tambayar tayi tace "Yaa Abu mana, she needs to know na warke, ina Ajiddeh?", jin ambaton sunan Ajiddeh yasa yaji abubuwa da dama na taso mishi, hannunta ya kamo cikin nashi yace "Fatima Kiyi bacci Dan Allah", k'ok'arin tashi ta shigayi tace "Toh ina taje mana, I just need to know", a fusace ya janyota yace "I will slap you right away in baki kwanta ba, bakisan you are still weak bane? komawa tayi ta kwanta, ajiyar zuciya yaji ta sauk'e, yaja d'an tsaki, bada son ranshi yayi mata fad'an nan ba, so yake ya dena tunawa da Ajiddeh, gabanshi har fad'uwa yakeyi in ya tuna abinda tayi, he have to caution Batuul d'in da kanta ta dena tuna mishi da ita, atleats for the mean time, ajiyar zuciya ya sauk'e ya rungumota jikinshi yace "Am sorry Fatima", bata ce mishi komai ba, hakan yasa ya mirginota tana fuskantarshi yace "You should rest Fatima Dan Allah, I love you"
[12/1, 15:42] 80k: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐
89
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
[12/1, 15:42] 80k: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐
89
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*