← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 166

Sashe 78

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Palo ya koma ya kwanta, remote ya d'auka yayi powering TVn, yunwa yakeji amma bazai iya tashi ba, he is too stressed, kitchen ya koma ya had'a coffee, snn ya dawo parlour ya jinginar da kanshi kan sofa yana kurb'an coffee d'inshi a hankali, tasha ya canja daga TLC zuwa NATgeo Gold, don Ajiddeh ke kallon TLC, d'an tsaki yaja tunawa da yayi da ita da shirmen da ta gama yi mishi d'azun, ko kadan bae yi nadamar abinda yyi mata ba don ta kai sa bango, iska ya furzar daga bakinshi yaci gaba da shan coffeensa a hankali, ta baya yaji an rungumeshi, ko ba k'anshin turarenta ba yasan ita ce, ya b'ata rai, a hankali cikin rad'a tace mishi, "baby fushi kayi", k'in kulata yayi kamar baisan tana wajen ba sae dae he was so surprise bae yi tunanin xata sakko da wuri haka ba, kai it's vry unusual of her ma kawae, sae dae if she's up to something, zagayowa tayi ta gabanshi ta zauna kan cinyarshi tareda sak'alo hannayenta duka biyun wuyanshi tace "babe, am am sorry", ci gaba yayi da kallonshi kamar baiji mey take cewa ba, fuskanta ta kawo daidai nashi tace "talk to me mana babe, am truely remorseful wllh, sae daga baya naga ban kyauta ba forgive me plss, in dae akan....." Kasa ambaton sunan tayi, cije leb'enta tayi daga baya ta d'anyi murmushi ta kalleshi tace "indae akan Sister Batuul ne I promise baxa mu sake samun matsala ba", rintse ido tayi jin sunan Batuul ya fito daga bakinta, da mamaki shi kam yake kallota jin ta ambaci Batuul as her sister, anya Ajiddeh bata da brain disorder ma kuwa, k'ara shigewa jikinshi tayi tace "Yes our sister, I mean it, I was so stupid da na dinga yin abubuwan da nayi maka, I don't know what came over me that I reacted that way calling her names, but babe I promise bazan sake ba, kayi hak'uri kaji, I was just being pessimistic about her , thinking zaka sota if she stays here, but yanxu I have realised my mistake, she is like a sister to me also, I will gladly keep her in my house, I promise" a hankali ta kare maganar ta d'ago kanta tana kallon kyakkyawan fuskanshi, lumshe idonshi yayi sannan ya bud'esu, rungume shi ta sake yi murya can kasa tace "Trust me babe" rungume ta shi ma yyi sosae, ya lumshe ido yace "why didn't you realise it since then, but anyway am happy that you finally realised it, kinga yarinyar nan bata da matsala, nasan she will b obedient to you indai har kika kwantar da hankalinki kika jata a jiki, zakiji dad'in zama da ita, am also sorry for everything Honey" kai ta gyad'a mishi tace "nima nasan bata da matsala baby, kasan sharrin shaid'an kuma da irin son da nakeyi maka, I can't risk seeing you with another woman, zan Iya mutuw....", hannu yasa a bakinta yace "shhhh, I will always be yours alone" kallonshi tayi tace "promise", bakinshi ya d'aura kan nata tare da janyota jikinshi, sai da ya gaji dan kanshi ya saketa, k'ank'ameshi tayi jikinta ta saki wani mugun murmushi, hiran da suka gama da Mummy d'azu ta tuna, da kuka dama ta shiga d'aki bayan Abu ya haura sama ya bar ta falo, waya ta d'auka ta shiga neman layin Mum, bugu biyu ta d'aga, wani irin razanannnen k'ara Ajiddeh ta saki da har ya tsorata Mum d'in ya sata janye wayar daga kunnenta tana tabbatarwa ko da Ajjideh take waya, a rikice ta maida wayan kunnenta ta shiga tace "keh daina shirmen nan kiyi min magana, mey ya faru kuma", Cikin sheshek'a ta gama zayyanewa Mum yadda akayi, da mamaki da tsoron jin abinda Ajiddeh ta gama fad'a mata ta sauk'e ajiyar zuciya tace, "wane rashin hankalin ne ya kaiki zagar mishi y'ar uwa harda ce mata karuwa a gabanshi, keh kinsan halinshi mey ya kaiki yin abunda har zai dakeki, wama yace kije ki tafka wannan haukan wai", cikin sheshek'a tace "Mum ni bansan ya zanyi bane, I was furious a lokacin, raina duk ya gama b'aci, bazan iya jurewa ba shiyasa nayi mishi wannan haukan, ko ba komai dai ai shima ranshi ya b'aci, sai ita wannan y'ar iskar, da na samu nayi laying hannuna kanta wlhy da sai yadda Allah yayi da ita dan tsanar da nake mata baya misaltuwa", katseta Mummy tayi da cewa, "naji ya isa, d'azun nan su Zainab suka wuce Tchad, kuma duk kan aikin namu na turasu dan ni Daddynku ya hanani zuwa, toh yanzu abinda nakeso dake, siyasa zaki shiga yi masa ki nuna masa kinyi kuskure kuma kin gane laifinki amma hakan bazai sake faruwa, ki nuna mishi kina k'aunar ita yarinyar har sai ya aminta da hakan, itama ki nuna mata k'auna har sai mun samu munyi maganinsu shi da itan dukkansu da ma duk wani munafiki dake gefe, ni yanxu haka ba kud'i hannu na kuma Dad d'inku rabon da ya bani kud'i har na manta dan cewa yayi baisan mey nakeyi dasu ba, wai har sai na nuna mishi abu d'aya da na tsinana mai amfani da nayi da kud'in, yanzu haka nayi niyyan k'iranki in miki bayani akan tafiyansu Zainab d'in sai kika rigani, kud'i kawai xaki turo har Zainab d'inma wani senator da yazo wajen Babanku ya ganta yace yana sonta amma kuma yanada mata sannan Babanku yace ya turo dan ya bashi ita shine mukeso musan yadda za ayi da Matan nashi dan bazan yadda da kishiya ba, kinga kina turo kud'in sai ayi komai a gama, an jefi tsuntsu da dutse d'aya", Hankalin Ajiddeh ne ya fara kwanciya jin bayanin da Mummy ta gama yi mata tace "Mummy wannan kud'i duk ba matsala bane, yau da safen nan ya rubuta min cheque d'in miliyan uku da nace mishi ina buk'ata, banmaje nayi cashing d'insu ba a bank, xan turo sai ayi abinda ya kamata, amma Mummy d'ayan ne ban iyawa, wlhy na tsaneta yadda baki zato, bazan iya nuna ina sonta ba, Kawai in ansamu anyi abinda za ayi ta tattara nata ta barmin gida", tsaki Mummy taja tace "ai kinji ki, toh kije kiyi abinda kika ga dama tunda baza ki d'auki abinda na fad'a miki ba", cewa tayi "Mum ba hakane bane, kawai ni kallonta ma bana son yi ne", Mummy tace "na fahimceki, amma kowane mutum yana son a so d'an uwanshi, da hakan sai ya dad'a kyautata miki, kinga ko ta dalilin ta zaki moreshi bare shi dake son y'an uwanshi, lokaci d'aya zai Iya rabuwa dake ya maida wata gurbinki, amma y'an uwanshi bai tab'a iya canja su, shiyasa nakeso ki nuna mata so", cikin hanzari Ajiddeh tace, "Mummy abar wannan maganan, ni yanzu xan turo komai a gama", ta tsorata da jin da tayi za a iya canja ta, Mummy tace "toh shikenan yanxu ki tashi ki shirya kije ki bashi hak'uri ki nuna kinyi nadaman duk abubuwan da kikayi", wani munafikin murmushi tayi ta sake shigewa jikinshi da ta dawo daga tunaninta, shi kam Abutturab tunani yadda zaiyi da Batuul Kawai yakeyi duk randa Ajiddeh ta gano ita d'in matarsa ce yasan gidan nn sae yayi musu kadan, tunanin Batuul kawai yakeyi zamansu a wajen, Ajiddeh ta kalleshi tace "baby na fara jin bacci muje mu kwanta", kallonta yayi dan shi sam bayajin bacci, Batuul ma kawai yakeson gani yaga halin da take, yace Mata "I will b coming dear, bari in gama program d'innan its interesting, I will meet you up there", peck yayi mata daga haka ta mik'e tayi hanyan stairs, har ta fara tafiya ta juyo ta kalleshi tace "Baby, I will check on my Sister before leaving", da wani munafikin wide smile shimfid'e fuskanta da kana gani kasan yak'e take, kallonta kawai yayi har ta juya ta tafi, ya sauke ajiyar xuciya cikin ransa yace Allah sa har cikin ranki Ajiddeh.
Chapter 78 · 0% Book details