Sashe 80
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
8:30 Abuturrab ya fito sanye da pyjamas d'inshi, tun daga bakin kofa yake jin k'anshin masu dad'i sun had'e gidan, kanshin turaren wuta da na abincin da ta dafa, sauk'owa kan stairs d'in yayi, yadda gidan ke shining ya bi da ido har ya k'araso dining, da mamaki yake kallon kan dinning d'in ganin anyi arranging abinci Kai, k'arasowa yayi ya bubbud'esu, aroma din abincin ya bugi hancinshi, maidawa yayi ya rufe, for the first yaji Batuul ta birgeshi, yasan training d'in Aunty ce ita din, murmushi yayi ya haura sama, d'akinta ya nufa ya tura kofar ya shiga, kwance ya ganta kan gado a kife, bayanta kawai yake gani sai screen din computer, ya karasa cikin d'akin don ganin abinda take kallo, har yazo bakin gadon bata sani ba sai tuntsirar dariyar da take ta faman yi, jin mutum ya zauna kan gadon yasa ta saurin mik'ewa zaune, matsawa tayi daga kusa dashi ta koma can k'arshen gadon, kallonta kawai yake, haka kawae ya samu kansa da murmushi, a hankali ta d'ago idonta taga ita yake kallo, maza tayi ta d'auke nata idon cikin sanyi tace mishi "ina kwana" ya bude ido yace "Morning! Ashe kin iya tashi da wuri?" Kauda kai tayi tace "Eh!" Yyi shiru yana kallonta, satan kallonsa tayi jin shiru suna hada ido ta dauke nata da sauri, ya d'aga kafada yace "Ya dysmenorrhea, ko dama na kwana daya yake maki?" D'an turo baki tayi ta juya masa baya, yyi murmushin da bae san dalilinsa ba, bae kuma ce mata komae ba ita ma bata juyo ba sae dae addu'a kawae take ya tashi ya tafi, wayarta ne dake gaban mirror ya shiga ring, ta mike a hankali ya bita da kallo har ta isa gaban madubin ta dauki wayar, wara ido tayi tana murmushi ta d'aga, sae kuma ta hade rai tace "Kin ban mamaki farida friendship din kenan dama sae yau kika san za ki kira ni koh?" D'aga daya bangaren farida tace "Wayyo Afuwan Besty, kusan kullum sae nayi xancen ki gun Ammah I just don't want to call ki fara min kuka ne wllh, waow hope you are enjoying ur new home, tell me how it is over there, have you made friends? Ina jarababbiyar matar ya Abu, how are you coping with her, hope she isn't giving u tough time...." Batuul ta xaro ido tace "Kai farida spare me those questions, hakuri ya kamata ki fara bani da yawa" Farida ta fashe da dariya tace "Ohhh yhu need to see how happy I am besty, ur voice is so lively, from all indication I guess u are enjoying it over there...." Batuul tayi murmushi a xuciyarta tace uhm lallai kam, ko ba enjoy ba, a fili tace "Ni dae ina Ammah fa?" Farida tace "Tana daki wllh let me put her on the line" Batuul tayi murmushi tace "Alryt!" Juyawa tayi tana kallon Abuturrab da ya kafa mata ido tayi maza ta dauke kanta, muryan Ammah ta ji da fara'a tace "Bitti?" Batuul tayi murmushi ta sulale nan k'asa ta xauna a hankali tace "Na'am Ammah ina kwana?" Ammah tace "Lfya lau Bitti ya gida? In ji ba matsala dae koh? Kar fa ki boye min don Allah" Batuul tace "Babu Ammah ya su Abui?" Ammah tace "Lfya lau suke, ya karatu kina xuwa dae koh?" Batuul tace "Ehh ina xuwa Ammah" Ammah tace "Ma'sha Allah! Ina Abuturrab din" kallonsa tayi taga ita yake kallo, a hankali tace "Ga shi nan, in bashi?" Ammah tace "Bashi!" Hade rae yyi yana kallonta, ta sunkuyar da kanta ta mike a hankali ta isa gabansa ta mika masa wayar, karba yyi ya fixgota lkci daya ta fado jikinsa tun kan tayi k'aran da take shirin yi ya rufe fuskarta a kirjinsa, tayi lamo tana shakan kamshin jikinsa me dadi, wayar ya kai kunne yayi ma Ammah sallama sannan ya gaisheta, da fara'a ta amsa masa don ba karamin dadi taji ba jin suna ma tare, tambayarsa Ajiddeh tayi yace tana dakinta, nan dae ta dinga masa nasiha kamar yanda ta saba a kan yaji tsoron Allah ya xama me adalci tsakanin matansa, dama irin abinda yake gudu kenan shi, don jikinsa sanyi yake, lumshe ido yyi yana sauraranta, ta kusa minti goma tana nasihan nata har lkcn kuma Batuul na jikinsa yaki saketa gabanta sae faduwa yake don she's not use to that, daga karshe ce masa tayi ya ba Batuul wayar, mika mata wayar yyi ta karba ta shiga kkrin kwace jikinta amma ya ki saketa, k'ara wayar a kunne tayi, Ammah tace "Kina jina Batuul" a hankali tace "Eh Ammah" Ammah tace "Kiyi ta hakuri kin ji Bitti, bbu ruwan ki da Abokiyar xaman ki tsakanin ki da ita sae girmamawa, ki kula da ibadun ki, ki xama me tsafta duk da nasan kina da amma ki kara kan na da, ko da yaushe dakin ki da jikin ki ya kasance cikin kamshi kin ji, Farida na nn xuwa idan sun yi hutu" Batuul ta wara ido cike da murna tace "Toh Ammah nagode, Allah kara girma" Ammah tace "Ameen Bitti sae mun kuma waya" nan suka yi sallama Batuul ta d'aga kai tana kallonsa ta ga idonsa lumshe, kokarin xame jikinta ta shiga yi ya bude ido yana kallonta, ta hade rae tace "Makaranta xan tafi ni" saketa yyi ya mike sanin lkcn tashin Ajiddeh yyi, ya fice daga dakin, bin sa da kallo tayi kafin ta lumshe ido ta kwanta kan gado.
Karfe Tara da wani abu ta sakko da shirin tafiya makaranta, xaune ta same su shi da matar tasa kan dinning suna breakfast, Ajiddeh na ganinta ta sunnar da kai don bata so ta sakko ta sameta tana cin girkin ta ba, idon Abuturrab na kanta har ta karaso falon kanta a k'asa ta ce "Ina kwana Anty" Ajiddeh ta kirkiri murmushi tace "Lfya lau sister, ashe kin tashi, nace Aliyu ya shigo ya dubo ki muyi breakfast yace wae ba kya tashi da wuri" Batuul dae bata ce komae ba sae kofa da take kallo, Ajiddeh tace "Toh ki karaso ki karya mana" girgixa kai Batuul tayi tace "A'a na sha tea tun daxu" Ajiddeh tace "Ohk," kofa Batuul ta nufa jin Abuturrab bae ce komae ba, yana ganin hka yace "Ki jira ni gun mota, na aiki driver" toh kawae tace ta fita, Ajiddeh da mood dinta ya canxa lkci daya ta sunkuyar da kai kar ya lura, da sauri ta D'ago tace "Honey ko kuma in kai ta kawae tunda motar biyu ne kar ka makara" ba tare da ya kalleta ba yace "Ae ita ma ta iya driving din, Akwae kudin da xan bata ne shi yasa nace ta jira" Ajiddeh taji kmr ta kwala ihu, wato har kudi xae bata, murmushi ta kirkira tace "C'mon babe nima ae kanwata ce, nawa xaka bata in bata kawae?" Ajiye cup din coffeen hannunsa yyi yace "Don't bother suna da yawa kudin" mikewa yayi yana goge bakin sa da tissue yace "Na tafi babe, sae na dawo take care of ur self for me" yana kai wa nan ya nufi kofa, bin sa da kallo tayi xuciyarta na tafarfasa, tana ganin fitansa ta mike da sauri har tana neman faduwa ta nufi kitchen don lekawa ta window ta ga inda Batuul xata xauna a motar, ae ko dai dai lkcn da Batuul ta bude front seat ta shiga, shi ma ya xaga ya shiga maxaunin driver, ta fashe da kuka da karfi wani mugun tsanar Batuul na k'aruwa a xuciyarta, anya xata iya ci gaba da yin abinda momy tace tayi kan Batuul kuwa, ynxu idan Abuturrab ya ji tana burgesa d'an girkin nan da ta iya ya xata yi da rayuwarta ita da ko indomie ba lallai ta dafa shi ruwa bae yi masa yawa ba, tunanin hakan yasa ta rushe da kuka ta fito kitchen din tana rerawa. 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐
55
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*