Sashe 111
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Wani matsiyacin kallo Farida ke bin Ajiddeh da ta tsaya tana hararanta taja tsaki tace "ke wllh kika sake gaya min maganar banxa baxa kiji da dad'i ba, ko ce miki akayi nice na rufe miki d'akin" juyawa tayi xata bar wajen ta ji Ajiddeh ta kuma damk'ota tayo cikin d'akin da ita, taga taga Farida tayi kamar zata fad'i tayi saurin regaining balance d'inta ta tsaya tana kallon Ajiddeh da mamaki tace "ke anya kanki daya kuwa, ko dai kina da tabin hankali ne" a fusace Ajiddeh tayo kanta, idon nan ya k'ank'ance dan jaraba tace "ke uwarki ke da tabin hankali ba ni ba, ni sa'ar uwarkice y'ar iskar mai kama da tsuntsaye da shegun dogayen k'afafuwanki, toh yanzun nan zanci ubanki shegiya munafuka, har ni za a ciwa mutunci a ci amanata, ku da munafukar uwar taku har kun isa ku wulakantani, ai sai nayi muku abinda duk baku zata ba, yadda kuka tozartani sai nasa kunyi kuka da idanunku, matsiyata munafukai, nafi k'arfin wulak'ancinku matsiyatan banza da wofi.....", tsabar frustration ma ta rasa tak'amai mai abinda zata fad'i sai huci take kamar karya, Farida dai kallonta ta tsaya yi baki bude dan ta tabbata yanzu cikin biyun nan da akwai d'aya inma dai tab'in hankali ko Kuma shigar aljanu, tana gyada kai tace "lallai ya Abuu na cikin masifa, ina ga tun farko bai san kina da tabin hankali ba ya auro ki, tun da ba ni na daura maki ba baxan maki addu'ar samun sauki ba sai dai ince Allah ya dauwamar da ke a haka" daga haka tayi gaba abinta ta wuce ta, cikin d'aga murya Ajiddeh tace "Uwarki ce mara hankali, Ehh Bilkisu ba, ita ce mara hankalin dan uwar....", bata k'arasa ba taji wani lafiyayyen mari har guda biyu da ya gigitata kan fuskarta, hawaye cike a idonta take kallon Farida zata tabbatar daga inda marin ya isota, Farida na huci tace "kika sake kika kuma zagina bama iyayena ba sai na zubar miki da rub'ab'b'un hak'oranki wllh, kazama kawai jahila wawiya wacce batada wayo, in shi da ya ajiyeki kin zageshi ya k'yaleki wlhy ni sai na lakad'a miki duka a cikin gidan nan kuma na daki banza tunda ke bakida hankali, kucaka dake har kin isa ki zagar min iyaye, toh koh Yaa Abun da kanshi in yana nan kika aikata haka bai hukunta ki ba toh ni a gabanshi zanyi wanda yafi haka ma, kuma aure an aura mishi d'in, keh har wata matace da za a k'ira da sunan mata in banda tsawo da kika sa a gaba kamar bishiyar dabino, in banda kaddara mey ma ya had'a Yaa Abu da auran irinki, bakida aiki sai kici ki kwanta, toh ko zaki rabe biyune dan takaici BATUUL matar Yaa Abu ce ta har abadan kuma mutu ka raba aurensu, sai dai in zaki mutu da takaici ki mutu, shasha kawai", ta watsa mata wani irin kallo ta juya taci gaba da tafiyarta, Ajiddeh dake tsaye kamar statue ji tayi zuciyarta na neman rabewa tsabar bakin cikin da ya taru ya mata yawa, wai har Farida ce zata mareta,wani irin k'arfi ne taji yazo mata, tsalle ta daka ta cakumo Farida da har ta kai k'ofa tayi baya da ita, Rai b'ace Faridan ke kallonta tace "ke wllh darajar auren Yayana dake kanki kike ci wlhy da kuma tarbiyar da aka min a gida inba haka ba yanzun nan sai na nuna miki k'aramin hauka kikeyi jahila kawai, cika ni", ta turata ta juya zata tafi Ajiddeh tayi wani kukan kura ta kuma cakumo Farida tace "Dan uwarki yau zakiga k'arshen rashin hankali" gaba d'aya ran Farida ya gama b'aci da wannan rashin hankalin na Ajiddeh, in ba tayi dagaske ba baza ta shafa mata lafiya ba, matsowa tayi dab da ita ta ta k'ara mata wasu lafiyayyun marin da suka fi na d'azu girgizata, a harzuk'e ta shiga dukanta ta ko ina kamar ta kama y'arta, Ajiddeh kam baki ya rufuwa sai ihu take tana cewa "dan uwarki dani kike , sai kin barmin gida tunda ba na ubanki bane shegiya gantalalla", sai da farida ta likid'eta iya son ranta ta nanata da k'asa, banda ihu da tsine tsine babu abinda Ajiddeh keyi bakinta na jini, Farida na huci tace "dama a cike nake dake, gobe ki kuma zagar min iyaye kuma ke in gidan na naki uban ne sai ki koreni", daga haka ta fice daga d'akin, Ajiddeh in banda kuka ta kasa yin komai, ko tashi ta sake cakumo Faridar bata sake yunk'urin yi ba.