Sashe 147
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
tana ta saka musu albarka snn suakje gidan Yayan Abui dake unguwarsu d'aya da Yaa Meran, sai gidan Aunty Amna, sosai taji dad'in ganinsu ta bawa Batuul abubuwa dayawa tareda bayanin yadda zatayi amfani dasu, bayan sun bar gidan Aunty Amnah taga sunyi hanyan gidansu, with so much excitement ta juyo ta dubeshi, ido d'aya ya kashe mata yace "Surprise", cikeda murna ta kamo hannunshi d'aya tayi kissing tace "I love you", murmuahi yayi this time ya kai hannuta bakinshi yayi kissing yace "I love you too Glitter", a hankali tace "Thank you", har tausayi ta bashi ganin murnar dake fuskanta yace "Shhh anything for you", daidai bakin gate d'in gidansu Batuul wayarshi tayi ringing, dubawa yayi ganin mai k'iran nashi take expression d'in dake fuskarshi ta b'ace, Batuul dake ta murna bata ma lura da yanayinshi ba, yana parking ta bud'e k'ofa da gudu ta fita, bayanta yabi ya had'e rai yana mata wani kallo tareda d'aura hannunshi kan cikinta yace "Gudun mey kikeyi?", rau rau tayi da ido tace "Am just happy ne zan ga Aunty fa", yace "Na fad'a miki bana son kina tsalle, my Baby", ya fad'a yana kallon idonta,sai lokacin ta fahimci inda maganar ta dosa, ita mantwa ma takeyi da wani halitta cikinta, puppy eyes tayi mishi tace "Tohh, toh ka sakeni sai in shiga gida", bai saketa ba saida ya koma ya rufe k'ofar motan snn ya kamata suka shiga ciki a tare, suna shiga ya saketa, tana son gudu tana tsoron fad'anshi , Sunan Aunty ta shiga k'ira, jawota yayi yace "Glitter meye haka kikeyi?, zamu koma tunda haka zaki rik'ayi", kai ta girgiza mishi tace "Na daina fa", Daidai nan Aunty ta fito side d'in Baba, da gudu taje ta rungumeta ta fashe da kuka, Aunty da mamaki ya cikata ta d'ago tana kallonta tace "Aa a, Batuul daga ina haka ke Kam harda kuka?", sake kwanciya tayi jikin Aunty tace "Aunty I Missed you, 4months ban ganki ba fa", dariya ta bawa Aunty, itama tayi kewar y'ar tata sosai tace "Keda yanzu kin girma, ba kullum zaki na ganina ba dama", Ta shagwab'e fuska tace "nikam wane girma nayi?, am still your kid Batuul", Aunty tace "naji toh, keda waye haka da magrib d'inna?", juyawa tayi ta kalli inda Abu ke tsayawa ya zuba musu idanu yana kallon bond da affection d'in dake tsakaninsu yana murmushi", Aunty ta fad'a murmushinta tace "Aliyu ashe tare kuke tafe shine ta k'yaleka a tsaye, shigo ka zauna", bai ce komai ba ya k'arasa shigowa ya zauna snn suka gaisa da shi, Aunty ta juya zata tafi Batuul ta bita a baya, text ne ya shigo wayan Abun ya duba yaga, bai damu da ya karanta ba sabida ko ganin maishi bayason yi bare kuma har ya kai ga karanta text d'in, yana gogewa k'ira ya sake shigowa wayan, bai d'auka ba ya ajiye wayar gefenshi, Batuul da ta fito riqe da tray ta kawo mishi ruwa ta tsiyaya mishi cikin tumbler ta mik'a mishi, yayi mata murmushinshi mai kyau ya karb'a yana sha, wayarshi ce ta sake ringing, duban wayan tayi gabanta na fad'uwa ganin sunan da ta gani rubuce, wani irin curiosity ke fizgarta da yasata d'aukar wayar tayi receiving ta kai kunne, muryar Ajiddeh taji tana cewa "Aliyu Dan girman Allah badan halayena ba ka taimaka kazo Mum tayi accident ko sau d'aya ka ganta ta nemi yafiyarka", ido ta lumshe hawaye na taruwa idonta lokaci daya jikinta yayi sanyi, yana sauk'e cup d'in yaga wayarshi kunnen Batuul, da sauri ya karb'e wayan yana kallonta yace "Do you have to?", ido ta rintse hawayen da suka taru suna zubowa. 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐