Sashe 161
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
kasa hak'ura tayi su dawo daga Masallaci ta tafi bakin gate tana jiran dawowansu, yana shigowa yaji an rungumeshi, kuka ta fashe da jinta jikin Abu, ta dad'e da sanin son da yake mata amma bata san har ya kai haka ba, da murmushi a fuskanshi ya d'agota yana kallon yanda hawaye ke zarya, ya had'e rai yace "zakisa twinkle ma ta zama cry baby ko, to zan fasa", dariya tasa tana girgiza kai tace "Na daina, kaga ko, nayi shiru", ta fad'a tana share hawayenta, dariya shima yayi yana shafa kanta yace "that's my lil sis", dariya tayi ta sake komawa jikinshi tace "Yaa Abu I love you for being the best brother ever", "I love you too", ya kama hannunta suka shiga ciki, a d'aki Batuul ta fito wanka kenan Ammah ke fad'a mata sunan Fareeda aka maidawa Babyn, sosai itama taji dad'i, a nan take bawa Batuul lbrn Abu ne ya sawa Farida inkiyarta ta Farida lokacin da aka haifeta sbd son da yake mata, yaso Farida ya zama shine ainahin sunanta amma lokacin Abui ya mata hud'uba da A'eesha, shine sai Faridan ne ya bita, yanzu haka ba kowane yasan asalin sunan Faridan ba, Addu'a tayi musu Allah ya k'ara musu zumuncinsu, Farida ce ta shigo riqe da wani k'aramin chest box, Batuul ta mik'awa box d'in tace "You know I love you ko?", dariya Batuul tayi tana saka kayanta tace "sai yau kike jin tunamin da son da kike min?", Farida ta mik'a mata akwatin tace "This is for Lil Farida", karb'a tayi taga golds ne ciki, mirmushi kawai tayi ta ajiyeshi gefe dan batasan mey zatce mata ba, tare suka gama shirinsu, sosai akayi shagalin suna, Batuul da Baby suka samu kyaututtuka sosai, sai ranan Ammah ke jin Komarwa Ajiddeh ganinta tazo sunan itama da kyaututukanta, Ammah sam ba haka taso ba, amma jin Batuul ce tayi insisting dawon nata ta hak'ura, dama dan ita take k'in komawan Ajiddeh, bayan wata hud'u suka tarkata suka koma UK har Ajiddeh *FOUR YEARS LEAP* EPILOGUE 💖💝BATUUL💖💝