Sashe 150
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Hawayen da kanshi nema take ya zubo ko zataji dad'i ta rasashi, ido ta k'urawa Mummy dake kwance duk jikinta anyi bandaging gwanin tausayi, tunda taga yaqi d'aga k'iranta tasan babu yadda za ayi yazo, tunanin Abutturab yasa ta jin silalowar hawayen da take ta neman zubowarsu ko zata samu y'ar nutsuwa, amma Sam abun ba haka yake ba, saima rad'ad'i da ya k'arama zuciyarta, tun da Dad ya fita bai sake shigowa ba har yau, a hankali taga Mum na k'ok'arin bud'e ido, da kyar ta bud'esu tana k'arewa d'akin kallo, kan Jainaba dake kwance ta d'aya b'arin idonta ya fad'a, hawayene kawai ya dinga silalo mata, a hankali ta maida dubanta ga Ajiddeh dake zaune, rintse ido Ajiddeh tayi ta bud'e snn tace "Mum wani irin fitina ne wannan nake gani a rayuwa?, duk wata masifa ta rayuwa na gama ganinta, Mum kece silar duk wani tashin hankali da nake ciki yanxu, tun ina k'arama tun Dad baiyi arzik'i ba, tun kamin inyi hankali na fahimci duk abinda kike so sai kin sameshi ko da ya kaucewa shari'a, tun bamuda arziki kike cewa mucewa k'awayenmu mufa y'ay'an wane da wanene, tun ban fahimta ba har na gano ma'anar inda kika dosa muka fara biye miki, babu yanda Dad bai nuna k'ok'arisnhi kanmu ba dan mu gyara amma kan ya faskara saboda kullum tare dake muke, zamanmu dake yafi yawa dole mu d'au ak'idarki, Mum kece uwa ta farko da na fara ganin bata tab'a yiwa y'ay'anta fad'a kan abinda babu kyau ba, baki tab'a tsawatar mana akan laifinmu ba, Dad ne kad'ai ke mana fad'a, ana haka Dad yazo ya samu arziki, d'an time d'inshi da muke samu yazo ya zama bama samu, duk wani jin dad'in rayuwa mun samu saboda irin son da yakeyi mana, amma ko shi Dad naga ba time d'inshi kikeda ba sai abinda yake dashi, kin koya mana son abin duniya da muka d'auka muka girma da, nima nasa a raina zanso mutum amma saboda kud'inshi", tayi shiru tana shesheka ta kalli Mummy da ta rintse ido tana kuka, taci gaba, "Allah mai yi yadda yaso da bayinshi ya had'ani da Aliyu da kallo na d'aya naji duk duniyar nan babu wanda nakeso kamar shi, babu possible ways d'in da ban bi dan yasoni amma ko zamana baisan da ba, a haka na tareki da zancen, tashin farko Mum cewa kikayi zamuyi maganinshi, haka mukayi ta bin bokaye, duk basuyi tasiri akanshi ba har saida na samu nayi plan d'in da ya bigeni da mota, ni nasan Aliyu bai tab'a sona ba, amma saboda son da nake mishi yasa bazan iya barinshi ba, ya aureni bawai dan yana so ba, nasan ya rasa abin yine saboda matsa mishi da akayi a gida, na samu fatana ya cika, my dream came true na zama matar Aliyu amma son zuciya da tsoron rasashi suka rinjayeni, babu abinda na tashi saka mishi da sai rabashi da nayi da iyayenshi da danginshi har tsawon shekara, Allah da yake shi ba azzalumin bawanshi bane ya saka mishi, iyayenshi sanin da sukayi ba haka kawai zaiyi haka ba, ba zasu zauna suna gani d'ansu ya halaka ba suka nema mishi aure", dariyan takaici ta saki tana girgiza kai taci gaba tace "Dole ma Allah ma yayi mishi sakayya ta alheri, mey na tab'a yi mishi na zamantakewar aure?, ko tsinke ban tab'a dagawa gidana ba bare inje ga zancen girki, a haka ya dawomin da yarinyar gida, tun had'uwata ta farko hankalina bai kwanta da ita ba, dukda kullum ina admiring duk wani abu nata, nutsuwa, kunya, k'awaici amma hakan baisani ganin gaskiya ba sabida son zuciya, Baiwar Allah jikina dama yana bani da wani abu a tattare da ita mai girma, amma son zuciyata yasa na cutar da ita, da na tab'a sanin akwai ranan da zan bud'i ido inji Aliyu na korata kan yarinyar nan da ko kallon banza ban jifarta dashi bare mugun kaba'iri, gashi a dalilin cutarta da nayi yasa yace ko kallona bai sakeyi, am not putting all the blame on you Mum, I have a commision a ciki, in kinyi abu mara ai nima nasan daidai zan iya gyarawa, shiyasa Allah ya bani hankali amma naqi aiki dashi,聽 gashi we are accounting for all our deeds, we are reaping what we sow, Mum ni bansan mey kikaje yi har illorin ba amma nasan ba alheri bane ya kaiki, gashi nan Allah yana nuna mana ishararsa, Na kirashi yazo mu nemi yafiyarsu Mum yaqi d'agawa, ko yafiyarshi ne yazo in roqa", Sai lokacin Mum ta bud'e idonta da suka kad'a da k'yar tace "Hauwa duk wani abu da nayi dan Ku nayishi, babu wanda nakeso da k'auna duk duniyan nan sai ku da Allah ya mallakamin, banida kowa sai y'ar uwata Jainaba, mun taso cikin k'unci nida Jainaba da nayiwa kaina alk'awarin y'ay'ana bazasu fuskanta ba, ba haka naso rayuwa ta juya mana ba, kuyi hakuri Ajiddeh, nafiku jin ciwon duk abin nan da yake faruwa, tafiyan nan da nayi duk dan nema muku farin ciki na fita yinshi, farin cikinku shine nawa, ku yafemin, ta fashe da wani sabon kukan