Sashe 159
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
馃挐馃挅BATUUL馃挅馃挐 By Phartiemarhk 100 Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR* Kai tsaye Aunty Kulthum closet d'inta ta nufa ta bud'e tana cewa "Ajiddeh ki tashi Allah maji rokon bayinsa ya amsa mana addu'armu, Allah gafarur rahim ya dubi niyyarki ta tuba kuma yaji kukanku, maza tashi ki shiryaki baqinki na guest parlour suna jiranki", kamar ba da ita akayi zancen ba ko juyowa batayi ba saima rintse ido da tayi tana maida k'afafunta k'ark'ashin duvet, Aunty Kulthum tafi kowa sanin matsalarta mesa zatazo ta dameta da surutun tayi baqo, ita ba kowa tayi da yaxo wajenta ba, koma wacece saidai ta tafi dan batajin tanada kuzarin da zai iya mik'ar da ita daga wannan kwanciyar, ita kanta ma ciwo yake mata, juyowa Aunty Kulthum tayi bayan ta ciro wani lace cikin closet d'in tace "Kehhh ashe haka Aliyun nake had'add'e, dole mana ki rikice kanshi irin wannan gayun haka da had'uwa, ai hotuna ma basa mishi adalci indai shine wannan", idanunta da ta rintse sbd sarawa da kanta keyi ta bud'esu a hankali daidai inda tasan zasu sauk'a kan d'aya daga cikin enlargements d'in Abutturab dake d'akin tanason sake ganin ko da wani sabon canji ne jikin hoton da sai yau Aunty kulthum d'in ke gani, dubawa tayi sosai bata ga wani sabon abun jiki ba, ganin Ajiddeh batada niyyan tashi ta k'araso bakin gadon ta zauna tareda yaye duvet d'in tace "Au inata magana kin barni ina zuba bazaki tashi ba, Aliyun naki nefa yazo gidan nan har yaga Daddynku kamin ya fita, yanzu haka yana guest parlour side d'innan shine ana ki tashi ki shirya kina kwance ke sarkin son jiki ko?, toh kwanta nan ki jawa kanki salalan tsiya", wani iri Ajiddeh ke jiyo magnar da Autyn nata keyi, yaushe ne Aliyu zaizo gidan nan, saidai in a mafarkanta da ta saba ko kuma in yazo kawo mata takardar sakinta, zumbur ta mik'e kamar wacce aka tsikara tunanin saki da tayi, hawayen taf idonta take kallon Aunty tana girgiza kai tace "Aunty Kulthum wlhy na yadda inyi ta zama da aurenshi koda bazai sake waiwayata ba amma kar ya sakeni, nashiga halin da ban tab'a shiga ba duk tsawon rayuwata, Allah ne ya jarabceni da son Aliyu, da inada yadda zanyi da tuni na cire na huta, son shine ya sani butulcewa Allah har ya kaini ga cutar wani, wlhy zan zauna da aurenshi koda bazai sake kallona ba a nan duniyan amma inason kasancewa matarsa a rayuwar da zamuyi nan gaba, yana bani takardata Dad zai aurar dani ga duk wanda yaga dama ina gama idda kamar yanda yayiwa Yaa Zee, nasan nima cemin zai yi in nemi wani uban idan har yayi min wani auren na kuskura na kashe, kuma na tabbata auren wani ne zai zame mini ajali, Dan Allaah Aunty kije ki bashi hak'uri ya koma da takardarsa, alfarmar da kad'ai zaimin kenan duk da nasan ban cancanci ayi min alfarma ba, ya barni da rad'ad'in da nake kwana in tashi dashi, kinji Aunty", sosai Aunty Kulthum ta tausaya mata ganin yanda ta gama rud'ewa har wani rawa jikinta keyi ta rungumota tace "Hauwa bana tunanin takardarki yazo kawo miki, ga dukkan alamu salama(Peace) yake nema ba akasin shi ba kuma inma hakance ta faru haka Allah ya qaddara miki, haka Allah yayi ke ba matarsa bace, hak'ura zakiyi ki rungumi kaddara, ki sa a ranki Dan Allah kika tuba badan ki samu kyakyawan sakayya ta hanyar samun Aliyu ba", girgiza kai takeyi tana hawaye jin maganganun Aunty Kulthum ta d'ago daga jikinta tace "Aunty so kike ki kwantar min da hankali ko?, so kike kawai inji dad'i, ni nasan wasa kike min", hannayenta duka biyun Aunty Kulthum ta riqo cikin nata tace "Hauwa tun ranar da na fara ganinki Allah ya samin sonki dukda bansan wacece ke d'inba amma na karanci damuwa k'arara a fuskarki, ban d'aukeki a matsayin y'ar miji saidai kallon k'anwa da nakeyi miki kullum, kullum fatana shine inyi abinda zai faranta ran Daddyn ku kamar yadda nima ya faranta min, ya cika min burina da nayi niyyan na mik'a azzaluman da suka cucemu nida y'ay'ana ga hukuma, ya sani cikin farin ciki har nake ganin nafi kowa sa'a, bazan so ganin jininshi cikin k'unci ba, Allah ma muna mishi laifi yana yafe mana, kisa Allah a ranki ki tashi ki shirya kije ki samesu, daga gani yaron d'an babban gidane yanada dattako da mutunci, kiyi fatan Allah ya zab'a miki duk abinda yafi alheri, ke dai ki tuna duk abinda zakiyi da Allah na nan, kinji?" jiki a sanyaye Ajiddeh ke jin duk wani abu da Aunty Kulthum ke fad'a mata, maza Aunty Kulthum ta sata ta shirya cikin lace mai kyau, ta sata ta gyara fuskarta tayi kyan gani, wardrobe d'inta ta bud'e ta ciro mata hijab d'aya cikin hijaban da ta d'inka mata, kallon Aunty Kulthum kawai takeyi har ta gama zira Hijabin, Aunty Kulthum tayi murmushi tace "Masha Allah, kinyi kyau abinki kamar amarya", d'ago ido ajiddeh tayi tana kallonta, Aunty Kulthum taci gaba "Ahap na manta, ashe amarya kike yau tunda za a wajen ango", sunkuyar da kai tayi dan jin kunyar maganar, turaruka ta feshe ta dashi snn tace mata ta k'arasa wajensu, in banda bugu babu abinda k'irjin Ajiddeh keyi, duk wata addu'a da ta kama ma sub'uce mata yakeyi, ta dad'e tsaye wajen kamin tayi shahada ta d'age labulen kanta a k'asa, Abutturab dake zaune duk yacika sbd yana son gano halin da Batuul da Babynshi ke ciki duk ya gaji da jira ya mik'e zai fita kenan ta sako kai, dafarko bai gane ko wacece ma saida yaji Massa yace "Madugu Uban tafiya ai sai ka dawo tunda gata nan gimbiyar taka da kasa hak'urin ta k'araso zaka bita nan ta shigo", dukda gabanta na fad'uwa maganganun Massa sun sa taji dad'i har ta samu k'warin gwiwa sake d'aga k'afa ta k'araso cikin d'akin, jin maganar Massa yasashu juyowa yana k'arewa halittan dake tsaye gabanshi kallo, ya rasa gane me ke bashi mamaki, hijabin da ya gani har k'asa jikin Ajiddeh ko kuma yanda ta koma, Idanunta a k'asa ta kasa d'agowa ta dubesu kuma ta kasa tsayuwa, shi d'inma kallonta yakeyi har saida yaji Muryan Massa yace "ina laifin kace ta zauna sai kaji dad'in kallon nata, amma ka barta tsaye duk k'afarta tayi tsami?", duk da tasan Massa nada barkwanci amma na yau Sam bata jinshi, wani irin relief kawai taji ganin ba kawo mata takardarta sukazo yi ba , wani kallo Abutturab ya jefawa Massa kamin ya samu waje ya zauna, ganin bashida niyyan cewa Ajiddeh ta zauna yasa yace "Uwar gida shine aka guje mu bamusan laifin da mukayi ba, toh nidai bari in baku waje dan wannan kallon da angon naki kemin zai iya sa hannu ya makeni, kema in na fitan sai kiji dad'in zaman tunda kin qi ki zaunan", ya fad'a yana mik'ewa tareda exiting d'akin, cikin masculine husky voice d'inshi da take muradin ji ko da yaushe taji yace "tsayuwar ke miki dad'i ne da baza ki zauna ba?", jiki a sanyaye hawaye taf idonta ta samu waje ta zauna a gefen kujeran daga k'asa, kallonta kawai yake kamar ba ita bace Ajiddeh da ya sani, sarkin gayu da kwalliya, fuskarta da kullum cike yake da rigima yau duk babu hakan, saima wata nutsuwa da sanyin dake shimfid'e kan fuskar, har wani dogon hijab ta zira abunda bai tab'a ganinta dashi, ko guntune bare yau har k'asa, ko a da in ya matsa mata da tayi Sallah wata riga take zirawa tayi Sallarta da ita sab'anin yau da ta sanya hijab, cikeda nutsuwa yayi maganarsa yace "kinyi laifi amma shine baki iya bada hak'uri ba ko?", hawayen da ya taru mata ne ya shiga silalowa ta d'ago y'an fici ficin idanunta da suka rine ta kallleshi, sai yanzu ta kalleshi for the first time tun d'azu, har wani d'an haske ya k'ara da kyau, janye idonta tayi daga kanshi tana jin nauyinshi da kunyan abinda ta aikata, cikin siriyar muryarta dake cike da kuka tace "I know I was never a good wife, I wasn't a good daughter Inlaw, duk abinda nayi doesn't deserve a second chance, komai nayi nayishi ne sabida son da nake maka, na manta da Allah na nan, na manta shike biyawa bayinshi bukatunsu na alheri, na manta sai da yardarshi abu zai faru, sai da izinin zaka sami abu, na manta da ba komai mutum ke so zai samu ya zame mishi alheri ba, wani hanin ga Allah baiwa ne, son da nake maka yasa na butulcewa ubangijina duk da ya bani komai na rayuwa, nasan I don't deserve your love, Aliyu nasan zuciyarka tsarkakkiyace, fushinka da alhakinka ya kamani, badan halina ba kayi hak'uri ka yafemin, av learnt a lot, na koyi darussa da dama da a ada nake ganin bazan iya yinsu ba, zanje in har gida ince Fatima ta yafemin, Ammah ma zanje ince musu su yafe min, I promise you am not repeating such a mistake, In sha Allah baza ka sake facing problem dan ni ba, everything happens for a reason, kuskurena happened for me to change to a better person, av changed for the good, forgive me plss", ta k'arashe maganan cikin matsanancin kuka da nuna tayi nadamar abinda ta aikatan gaba d'aya abinma mamaki yake bashi, wai Ajiddeh ce ke magana haka a nutse, gaba d'aya jikinshi sanyi yayi, da yaso yi mata fad'a sosai ya nuna mata kurenta kan abinda ta aikata amma gaba d'aya sai yaji tausayinta ya cikashi, a hankali yaji yace "Hauwa", gaba d'aya jikinta saida ya amsa k'iran da Abutturab d'in yayi mata, kamar yaune ta fara jin sunanta daga bakinshi, a hankali ta d'ago rinannun idanunta jin ya sake ambaton sunanta ta sauk'e kanshi, hannunshi d'aya ya mik'a mata alamun tazo ta zauna daga gefenshi, in banda bugawa babu abinda zuciyanta keyi, batayi musu ba ta tashi ta isa kujeran dake gefenshi ta zauna a d'arare, hannunshi d'aya yasa ya kamo d'ayan hannun nata, rawa kawai hannun keyi har saida ya sake sa d'ayan hannun nashi ya rik'e mata hannun duka biyu, a hankali kukan nata ya fara sassautawa, saida yaga rawan jikin nata ya dena