Sashe 60
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
D'akin Abuu Ammah ta shiga bayan Batuul ta shige toilet, har ya canja kaya lokacin yana zipping wani akwati, ganin Ammah da yayi 膹akinshi ne ya sashi barin abinda yake cikin hanzari ya k'araso inda take, bata ce mishi komai ba har ta k'arasa shigowa tukunna ta zauna daga bakin gadon, rabon da Ammah ta shiga 膹akinshi har ya manta, jiki a sanyaye ya bita ya zauna daga k'asa, ce mata yayi "Ammah ai da kin k'irani nazo ba sai kinzo da kanki ba" har ta bu膹e baki zata fara mishi magana ta fasa tace "in ka gama ka sameni a 膹aki toh", daga haka ta mik'e tayi waje, ajiyar zuciya ya sauk'e dan yasan da magana bakin Ammah, koh minti biyu batayi ba da fita shima ya fita yabi bayanta, zaune ta tadda Batuul bakin gado har lkcn, ganin Ammah ta shigo yasa ta sauk'e kanta k'asa zata sauk'a k'an rug 膹in Ammah tace mata tayi zamanta, kin zama tayi kan gadon ta sauk'o k'asa, da sallama ya shigo 膹akin shima ya zauna kan stool 膹in mirror, Ammah na kallonshi ta fara magana "Abuu ga amanan Batuul nan na baka da hannuna", da sauri Batuul ta 膹ago jin abunda Ammah tace, jiki a sanyaye ta sauk'e kanta dan har idonta ya fara tara ruwa, Ammah taci gaba tana kallon yadda ya sauk'e idonshi k'asa tace "tunda kayi aure kasa k'afa ka fita daga garin nan hankalina bai kwanta ba, ni bansan tsakaninka da matarka ba amma mu dai kam babu abin alheri da tayi mana, ni da kaina na sa aka nemo maka auren Batuul dan tun kamin aurenka da Ajiddeh Batuul naso ka aura amma Allah bai yi ba sai yanxu, ko sau 膹aya ban yadda kasa hawaye zuba daga idon Batuul ba, ban yadda ko da wasa matarka ta wulak'anta min ita ba, yadda take zab'inka haka nima Batuul take zab'ina sannan amana na baka ita kamar yadda iyayenta suka aminta dakai suka baka y'arsu, ka kula da ita fiyeda yadda xa ka kula da kanka, sannan makarantarta ba denawa zatayi ba, an sama mata admission a can, ka taimaka mata da dukkan k'arfinka har sai ta kamalla dan tana karatunta muka nema maka aurenta, Allah ya tayaka rik'o ya baka ikon yin adalci tsakaninsu", ta juya tana kallon da Batuul da ta jik'a gyalenta da hawaye a lokacin tace "Bitti ga yayanki nan xa ku tafi, na fa膹a miki duk abinda zaiyi miki mara da膹i, don't hesitate in zama ta farko da zaki fa膹awa, ki zama mai respecting 膹inshi kinji, he will be your guide In sha Allah, tsakanin ki da matarsa girmamawa, ki goge hawayenki kinji, kuma duk lokacin da kike son dawowa ki fa膹a mishi zai dawo dake kina yin kwana biyu kinji", Sadiq ne ya turo k'ofan tareda sallama, da murmushi a fuskanshi ya dubi Abu yace "ba dai kun fasa tafiya ba yau", Abuu ya dubeshi fuskanshi babu walwala yace "We are coming", Ammah ta dubi Batuul ta 膹agota tace "Bitti share hawayenki ki tashi kuje, Allah yayi muku albarka, ya baku xuri'a dayyaba", da k'yar Batuul ta iya mik'ewa tana gyara gyalen dake kanta har wani shidewa take don kuka, Sadiq sai tsokananta yake sae dae shi ma xuciyarsa fal yake da tausayinta, suna sauk'a k'asa suka tarar da Massa shima yazo, gaba 膹ayansu suna zaune palon sun gama shanye drinks 膹in da aka kawo musu, Ammah tace "jeka Abui ya shigo yanxu kuje kuyi sallama dashi, tare sukaje sukayiwa Abui sallama yana gaba tana biye da shi a baya, Abui ya sake musu Nasiha tareda yi musu Allah ya kiyaye hanya, mota uku suka yi suka nufi airport.