Sashe 164
Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kumatun nashi tayi tace "I love you Daddy", shima pecking d'inta yayi yana cewa "I love you more Twinkle", "Daddy can I tell Mummy we will b going to Paris not California?", yace "You will tell her tomorrow, its late now, okay?", kai ta kad'a mishi tana k'ok'arin sauk'a daga jikinshi, Batuul dai na zaune tana jinsu batace komai ba, saida suka gama hirarsu wajen 8:15 tacewa "Twinkle ta tashi taje tayi mata wanka ta kwanta dan gobe zasuyi tafiya, a nan toilet d'in d'akin tayi mata wanka ta nad'ota cikin towel, lokacin Abu shima ya tafi yin nashi wankan a d'akinshi, saida ta gama shiryata tsaf snn sukayi addu'an bacci a tare, daga gefenta ta kwanta tana karanto mata stories of the Sahabas daga wayarta, dan har sun gama na prophets, jin ta dena tambaye tambaye hakan ya tabbatar mata da tayi bacci, ta gyara mata kwanciya tareda pecking d'inta snn ta sake tofe duka d'akin da addu'a, k'asa ta sauk'o ta samu Inna Halima(Mai kula da Twinkle da Ammah ta samar musu) a kitchen tana y'an goge goge, sanar mata tayi da ta kwantar da Twinkle, ta bar aikin haka ya isa taje su kwanta, saida ta kashe komai ta tabbata everywhere is safe ta koma sama itama, d'akinta ta koma dan yin wanka, tana k'ok'arin cire kaya ta mirror ta hango mutum kwance kan gadonta, k'ara ta saki zatayi waje yayi maza ya kamota, sam bata lura dashi ba lokacin da ta shigo, rungumeta yayi yana mata magana k'asa k'asa a kunne, yasanta da saurin tsorata amma bai tsamman yanzu ma zataji tsoro ba tunda d'akin duk haske ne, a kunne ya rad'a mata "Shhhhh Glitter, sorry kinji?, banso na tsorataki ba", har lokacin jikinta na b'ari, bata d'ago daga jikjnshi ba tace "I tot kana d'akinka fa", ya kamata suka zauna kan gado yace "its been long nayi wanka da kaina, keh nake jira kizo muyi tare", lafewa ta sake yi jikinshi tana turo baki tace "shine ka tsoratani ko?", murmushi yayi yace "Sorry Fatima, ki rage tsoron nan kinji banaso babu kyau, beside ba ke kad'ai bace, Lil champ d'ina is there, kar tsoronki yayi affecting d'inshi", ya fad'a yana k'ok'arin rage mata kayan dake jikinta, tace "Amorrr, watanshi fa d'aya duka duka amma shine har an fara zumud'inshi, haka akayi tamin a cikin Lil Farida ma", ya shafa cikin nata yace "I wish duk wata zaki bani sabon Baby ba, da nafi kowa murna, inason yara Fatima, kamar 12 or more, inason in ganshi kamar wani mini nursery, duk motsi inji yara kusa dani, i know i can't pay you but bakina bazai gaji da yi miki addu'a ba, Allah yayi miki albarka", tausayi ya bata, tasan yana da son yara, gashi ita kuma Allah bai sake bata wani cikin ba sai bayan shekara hud'u, Ajiddeh kuma har yau shiru ko b'arin wata batayi ba, har yau suna zaryan zuwa asibiti, rungume shi tayi tace "Amorrr, In sha Allah the best will happen kaji, Alkahairi da Albarka muke nema ba yawansu ba, in mukayi addu'a komai daidai zai tafiyar mana", muemushi yayi yana sake matseta a jikinshi, tare sukayi wanka sukayi shirin kwanciya bayan sunyi addu'o'insu, Washegari suka tashi da shirin tafiya Nigeria su dukkansu, suna isa Abuja suka sake boarding wani plane d'in to Maiduguri, banda Ajiddeh dan tace ita su barta a gidansu, in yan gidan nasu sun tashi zuwa zata biyosu su taho Maidugurin tare, da farko yaqi amma sbd magiyar da ta riqa mishi ya hak'ura, a gidanshi na can dake Old GRA suka sauk'a, daga gidan Ammah da gidan Aunty aka turo musu abinci dan su sunyi kwana biyu da zuwa, suna idar da Sallah Magrib suka shirya suka tafi gidan Aunty sbd zumud'in da Batuul keyi na son ganin yan gidansu, a parlour suka tarar da kowa, duk sun k'ara girma baki d'ayansu, da gudu Twinkle ta haye jikin Baba dake parlour dan tanason tsohon sosai, lokaci lokaci take sawa Abu ko Batuul su k'ira mata shi suyita waya, sama ya d'agata yana cewa "Ashe amaryar tawa na hanya shiyasa nake ta jin k'anshi ko ta ina", dariya tayi tana ajiye mishi jakan turaren da tayi ta rigiman ita zata d'auka tace "Handsome granny, this is for you", dariyan sunan da ta k'irashi yayi yace "Na manta ashe Baturiya ce, How was your journey?" kamin tayi magana Aunty ta d'agata ta baya tana cewa "Abinda ya kawoki kenan dama, ki gama kalle Handsome granny ko, toh ina nan babu mai kallar min shi, harta fara rigiman a sauk'ta ganin chocolate pack a hannunta yasa tayi shiru tana murmushi, Dariya suka sa su dukkan Aunty tace "Sarkin kwad'ayi, wato kinga chocolate shine kikayi shiru ko, ungo karb'i ya daifi ki sha ki barmin Handsome granny d'in", Nan su Abu suka zauna sukayita hira, sosai Aunty da Baba sukayi murnan ganinsu da result d'in da Batuul ta nuna musu na kammala makaranta, ta gama degree d'inta da first class honour, tho su Ahmad da Sa'eed sunje graduation d'inta da yake a UK suke karatu suma amma ba gari d'aya ba , sai albarka suke saka musu, anan Batuul ta Bawa kowa tsarabar da sukayo musu , har d'an kwalla Batuul tayi ganinta cikin y'an uwanta after years, kasa hakuri tayi gobe tazo ta gansu saida tazo a yau, har d'an kwalla ta share tana tuna rayuwarsu ta baya, da a dane da yanzu itace gefen Baba , But life has to move on, yau itace da tata y'ar tana raino, a ranta ta dinga furta "Alhamdulillah", k'arfe tara sukayi haramar tafiya gidan Ammah, Abu a Twinkle ne suka fara shigowa, turus ya tsaya ganin Farida zaune parlour da titsetsen ciki( shekararta d'aya da aure itada Affan d'inta) zaune ta tasa fruits gaba tana ci kanta ko d'an kwali babu, da gudu Twinkle ta je ta rungumeta tana fad'in "Small Mommah, Daddy didn't tell me you are here", rungumeta tayi tana jin dad'in ganinsu dan dama zuwansu take ta jira tun d'azu taqi tabi Aunty Sadiq kuma taqi baccu, da murnarta tace "Lil me, kin girma, Mommah na kula dake sosai", tayi dariya tace "Mommah are you too getting me a new lil smurf, Daddy said Mommah too is getting me a new Lil smurf?", ta fad'a tana tab'a cikin Faridan, muryan Abu ne ya katsesu yace "Yanzu shi Usman(Affan) dinne ya barki kina yawo tsakanin Nigeria da Paris a condition d'innan naki, marairaicewa tayi tace "Yaa Abu I was missing you all shine da naji zakuzo ya had'ani dasu Aunty Amna muka taho a tare, kuma I will be coming for Yaa Sadiqs wedding, inaso ayi duk shirye shiryen tare dani shiyasa nazo tun yanzu, shima next week zaizo", d'an tsaki yaja yace "Ai zanyi magana dashi inji inma ke kika matsa mishi da sai kin taho d'in", ya fad'a yana k'arasa shiga ciki, cikin d'aga murya tace "Dagaske nifa ban matsa ba Yaa Abu, ko ka tambayeshi he will tell you same", ko juyowa baiyi ba ya k'arasa ciki, A bakin kitchen ya had'u da Ammah tana fitowa, take murnarshi ta fad'ad'a ya rungumeta yace "Barka da gida Ammah", Ammah tana dariya tace "Da girmanka kana shirin tarb'o second child d'inka baka bar rungumata ba", ya marairaice fuska yace "Bazan tab'a canjawa daga Abutturab d'inki ba, kema you will always be my Ammah komai yawan yaran da zan haifa", ya fad'a yana pecking goshinta, tayi murmushi tana shafa kanshi tace "Inasu Bittin?", yace "suna parlour", k'arasawa sukayi parlour suka tarar da su duk sun zazzauna sai hira sukeyi gwanin sha'awa, Abu ya dubi Ammah yace "Ammah dubi yarinyar nan at this her condition aka barta take yawo haka", marairaice fuska Farida tayi tana duban Ammah with pleading eyes, Ammah tace "Toh ai ko ba yanzu ba zata dawo gida yin jego, shine dasu Amna zasu dawo Usman d'in yace ta biyosu", harara ya sakarwa Farida yace "Samun guri dai, dan zaka haihu sai kayi ta yawo", daga haka ya mik'e yayi side d'in Abui, Farida kam ko d'agowa batayi ba tasan intayi magana sabon fad'ane kuma, Batuul kam dariya ta dinga mata k'asa k'asa, ba a jima ba Sadiq ya shigo gidan shima, nan sukaci gaba da hirarrakinsu, Batuul kam sai tsokananshi takeyi ya kusa zama ango, Gashin nan da yake tarawa duk ya ragesu ya k'ara girma into a responsible mutum sosai amma duk da haka saida ya biyesu dan shima d'in gwanin tsokanan ne, Twinkle kam sam taqi zuwa wajen Ammah, tana b'oye jikin Farida duk maganar da take mata na tazo taqi, tana ganin an kawo kwab'ab'b'en jan lalle tayi maza ta mik'e daga jikin Farida tace "Will you do it for me Granny? I want to look beautiful", Ammah ta dubi Abu dake shan fruit Salad tace "badai har yanzu turancin nan kake mata ba Abu, haba inata magana yarinya tak'i zuwa", Batuul ce tayi maza tace "Tana fa jin Kanurin Ammah, haline dai da take dashi", Ammah tayi maza tace "Hali irin na Babanta ba, shima haka yake ai da yana k'arami ayi ta mishi magana yana jin mutane yaqi kulasu, amma dai keh ba turan cin nan kikeyi mata ba ko, dan wannan ai asara ne yaro ya taso baijin yarenshi", Batuul tayi murmushi tace "Da kanuri nake mata magana", Ammah tace "Kin ko kyauta, hakan yafi ai, Turanci da larabci ai ko a makaranta ka koyesu amma yarenka in bakayishi tun a gida ba babu kuma Inda zaka samu ka iyashi", ta dubi Twinkle tace "ja'ira da da nake ta miki magana kina jina kika k'i kulani shine saida kika ga lalle ko kike cemin a miki, you want to look beautiful, toh ko me zakiyi baza ki fini kyau ba bare ki samu k'wace min miji, zo zauna ayi miki, tsohon mijin naki ya biyani", duk wannan maganan da kanuri tayi mata shi, kallon Batuul tayi tana son tace mata taje d'in, kai ta gyad'a mata alama taje snn tace "wande nan fuun Nasaran(English)nduro mananimi, fanema naaa?"(Kada ki sake yiwa kowa magana da turanci nan gaba kinji?"), kai ta gyad'a mata tace "Yo Mommah", ta nad'e mata hannun riganta da yake dogo son ta tafi kusa da Ammah ta zauna, saida