← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 166

Sashe 52

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daga gaban gadon Abdallah ya tsaya a tunaninsa Abuturrab xae basu waje sae ya ga otherwise, don kujera gogan ya ja yyi xaman sa yana facing dinsu, Abubakar na ganin hka ya xauna gefenta ya shiga mata magana murya can k'asa da damuwa, Batuul ta k'asa 膹ago kai ta kalleshi, sake matsowa yayi kusa da ita yace "Habibty tok to me mana, mey doctor yace na damunki", a hankali kamar bata son aji mey take fa膹i tana wasa da fingers dinta tace "nima ban sani ba, but i think doctor ya fa膹awa su Aunty, ni ban sani ba", ta k'arasa maganan tare da 膹ago kanta, ido hudu suka yi da Abutturab dake kallonta ko kiftawa bae yi, ya watsa mata wani irin kallon da ya sata saurin sadda kai, haka Abdallah yaci gaba da yi mata tambayoyi da yi mata sannu da damuwa, bata cewa komai daga "um", sai "um um", banging k'ofa suka ji suka juya, Batuul ta sauke ajiyar xuciya ganin shi ne ya fita, juyowa Abdallah yayi yace "Habibty who is he? your uncle", girgiza kai tayi tace mishi "brother 膹in Farida ne", juyawa yayi ya sake kallon k'ofan sannan ya mik'e tsaye yace " Shknn Habibty i will b going, Mum na mota tana jirana get well soon, i will b back tomorrow in'sha Allah", yayi mata wani lallausan murmushi da itama maida mishi, daga haka ya fita yana waigen ta, a bakin k'ofa ya tarar da Abutturab na waya, tsayawa yayi ya gama wayan su yi sallama, ganin ya kusa minti biyar tsaye kuma ya ki k'are wayar yasa ya 膹aga mishi hannu ya wuce, Abuturrab na ganin ya wuce ya katse wayan ya tura k'ofar 膹akin, hawayen dake idonta take gogewa da tissue, tsayawa yayi yana kallonta daga bakin k'ofa, snn ya shigi tare da tura k'ofan ya rufr, jin k'aran k'ofan ne ya sata 膹agowa da sauri, duk da rashin k'arfin jikinta hkn bai hanata mik'ewa cikin sauri tayi hanyan toilet ba, da gudu taje zata bu膹e k'ofan, taji ya fixgota, tsayawa tayi a wajen ta kasa motsi gabanta na faduwa, ya juyo da ita yana kallon yadda ta rintse ido hawaye na zubowa, fuskanta ya tsura ma ido da 膹an k'aramin lips 膹inta da ya koma ja, hannunshi ya 膹aura kan kafa膹unta ya matso da ita gabanshi yana kallonta da kyau yace "waye shi?" Kin cewa komae tayi har lkcn idonta a runtse, ya daga kafada yace "As if i care, kina jina dama Aunty na shigowa ki ce mata kin warke a maidaki gida kuma ke kina da wanda kike so, nasan wannan da yazo ya saki gaba yana miki surutu kmr radio saurayinki ne, toh dama kice musu shi kikeso kuma keh shi zaki aura, is dat clear?", sai da taji yayi shiru har lokacin tana hawaye ta bu膹e ido a hnkli tace "kai mey zai hana ka fa膹a musu, kaima ai kasan su kuma zaka iya samun su ka fa膹a musu kace kana da matarka basai an sani aurenka ba dan ni bbu abinda xanyi da mai mata, sabon jini dama ai sai sabo, mey ma zanyi da......", ganin yadda ya zuba mata lumsassun idanunshi yasa ta maida sauran maganan tana gogewa hawayen dake fuskanta, bin fuskanta yayi da kallo har idonshi ya sauk'a kan k'irjinta dake ta heaving, dariya abun ya bashi amma ya dake, yasan duk maganan da tayi a tsorace take, saketa yayi yana mata wani irin kallo yace "Really?, Fine then, zamu ha膹u ne tun da bakiji abinda na fa膹a miki ba, ki yadda ayi auren, xagi gane mai mata kuma tsohon jini kika aura yarinya", yana kaiwa nan ya juya ya fita daga 膹akin, a nan wajen ta tsuguna ta sa kuka kamar wacce aka aikowa lbrn mutuwa, a nan Aunty ta shigo ta sameta, da gudu Aunty tazo ta 膹agata tana tambayanta mey ya sameta, kasa magana tayi sai kukan da take tayi, Anty ta maida ta kan gado ta rungumeta hankali tashe tana lallashin ta, a nan tayi bacci jikin Aunty.

11 o'clock bayan doctor ya dubata yayi discharging 膹insu akan zai na zuwa har gida yayi mata alluranta da suka rage sannan yace a guji duk wani abu da zai rik'a b'ata mata rai kuma kar a rik'a fa膹a mata maganan da bata expecting har ya rik'a shocking 膹inta tana zama unconscious, Baba ne yayi magana yace zasu kiyaye, da haka suka yiwa doctor sallama, suna komawa gida tace ita baza taje 膹akinta ba a 膹akin Aunty zata zauna, wanka tayi bayan ta shiga 膹akin sannan ta kwanta, ba ita ta tashi ba sai k'arfe biyu, tayi alwala ta tada Sallah, tana idarwa Aunty ta shigo rik'e da tray a hannunta, ajiyewa tayi ta zubawa Batuul abinci sannan tace mata ta sauk'o taci, da kyar taci ka膹an tace ta koshi,

Da yamma wajen k'arfe biyar tana zaune tana kallon E.tv Aunty na ha膹a kayan Aabid Baba ya shigo 膹akin, kan gadon da Batuul ke zaune ya zauna, tashi tayi zata sauk'a ta gaisheshi yace mata "Yaanyi" (Mamata), 膹agowa tayi ta kalleshi da idonta da ya fara kawo ruwa, hannu yasa ya goge mata hawayen ya matso da ita jikinshi ya fara mata magana kamar haka "Ya jikin ki Batuul", jiki a sanyaye ta amsa mishi da "Alhamdulillah Baa, yayi sauk'i, na warke yanxu", yace "Masha Allah, har yanzu kinason zuwa Uk kiyi karatun?, ya tambayeta yana kallonta, 膹agowa tayi ta dubeshi dan ta tabbatar da abinda taji yana fa膹a mata, ganin dagaske yake da sauri ta shiga gya膹a kai ta da膹a rungume shi, tasan dama babu wani aure da za ayi mata kawai Yayyace ta fa膹a, ce mishi tayi "ehh Baa inaso" murmushi 膹auke fuskanta, murmushin yayi shima yana shafa kanta yace "toh zan samo miki admission sai kije kiyi karatunki kinji ko, ai zakiyi karatu sosai ko?", kanta ta gya膹a har lkcn murmushi shimfi膹e fuskanta har yafi nada, cewa tayi "Baba toh yaushe ne za ayi, ko sai na gama semester 膹innan sai inyi transfer", ta tambayeshi tana jiran jin mey zaice, Aunty dake aikinta tana jinsu ta saki dariyan takaici dan tasan so kawai Baba yake ya shawo kan Batuul dan yasan tana son karatu sosai, zata iya hak'ura da komai dan tayi achieving dream 膹inta, Babane yace "very soon Mamata, amma kinsan mey nakeso dake", kai ta girgiza mishi yace "yawwa, kinga dama bana son zaman hostel, ko", nanma kai ta gya膹a, yace "toh kinga sai kiyi zamanki tareda Yayanki, nasan sosai zai kula dake", kanta ne ya膹aure ta fara tunanin wane Yayan kuma, ce mata yayi "nasan tunanin wane yayen kike, Abutturab nake nufi", wara ido tayi ta kalli Baba tana girgiza kai tace "Baa toh zan zauna inyi a gida na fasa wllh, bana son zuwa," hawaye cike idonta ta kare maganar "k'ara janyo ta yayi jikinshi ya goge mata hawayen dake zuba a idonta yace "ki kwantar da hankalinki kinji Batuul, nasan anytime you will be proud of whatever decision i made, nasan Aliyu tun yana k'arami, nasan abunda zai iya da wanda bazai iya ba, ki kwantar da hankalinki kinji, kuma auren da Yayya ta fa膹a miki gaskiya ne", sosai ta shiga kuka harda sheshshek'a" muryarta na rawa tace "Baba nifa yarinya ce, just last month na cika 18, kayi hak'uri in na girma sai kayi min ko da waye ma kaji Baa", dariya maganan nata ya bashi yace "Batuul akwai Babba ne da k'arami a bautar ubangiji, babu, toh kinga ina laifin tun kina k'arama ki fara bautawa ubangijinki, kinga ladanki nema zai k'aru, ga kuma ladan da zaki samu na yi mana biyayya, ko ba kya so", ya tambayeta yana kallon fuskanta dake ta ambaliyan hawaye, kasa cewa komai tayi, ci gaba yayi da mata magana yace "toh mamata y dont you start it early and be rewarded abundantly, tunda at any point zakiyishi its better you do it now, and am assuring you Abu will b d best husband we will ever recommend for you, Nida Babanshi have been good friends for over 30yrs, har gida yazo ya sameni ya nemawa Aliyu aurenki, duk mutumin da yaso jininka har yaso ha膹a zuriya dakai yafi k'arfin wulak'anci, kinga ba da膹i ince musu a'a, sosai yake ganina da mutunci, friendship 膹inmu da muka gina based on trust yafi k'arfin ya nemi abu a wajena in hanashi", jikinta ne yayi sanyi sosai, 膹agota yayi yana kallon fuskanta yace "Ko in koma ince musu kince bakya so", a hankali ta girgiza kanta alamar a'a, yace "yawwa Mamana Allah ya miki albarka, yanxu ki share hawayenki ki rok'i Allah ya tabbatar miki da duk alherin dake cikin bikin nan", haka ya dinga bata baki yana kwantar mata da hankali har yasa Batuul ta hak'ura, sai da aka k'ira magrib tukunna ya fita daga 膹akin ya tafi yin Sallah.
Chapter 52 · 0% Book details