← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 166

Sashe 15

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

K'arfe 1:30 kowa yayi shirin watsewa, Farida ce tacewa Batuul "muje gidanmu sai daga nan mu tafi prom 膹in daga nan it will be easier ko", Shiru Batuul tayi sannan tace " okay muje mu fa膹awa su Aunty sai su turomin kayana gidanku, wajen Aunty Batuul taje ta fa膹a mata komai sannan tace okay kuje sai Baa Liman yazo miki da kayanki, mota su Aunty suka ahiga suka tafi , wajen dasu Ammah suke suka k'arasa taga su Ammah ma basa nan daga Abutturab sai wannan farar matar ta zauna daga gaban mota tana ta kumbure kumbure, hango su yayi yabi Farida da harara yace "ina kika tsaya inata k'iran wayanki bakya recieving", ce mishi tayi Yaa Abu a silent wayan yake, banji bane" Batuul ce a ranta addu'a take Allah yasa ba dashi zasu tafi ba, da ta sani da kawai su Aunty tabi in yaso daga baya a kawota, da taga Farida ta bu膹e k'ofan baya ta shiga ne yasa itama ta bu膹e ta shiga, tana zama 膹aga kan da zatayi suka ha膹a ido da Abutturab, harara ya sakar mata tayi saurin 膹auke kanta sannan yaja mota suka fita daga wajen 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

15

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Sau biyu idonsu na ha膹uwa ta rear mirror da Batuul tana saurin 膹aukewa, daga k'arshe komawa tayi gefe owners corner yadda baza ta na kallonshi ba, ita da tasan shi zata bi ma baza ta bari y'an gidansu su tafi ba, ga wannan heart beat 膹in da yaqi barinta kamar heart na shirin fitowa, gaba 膹aya ma ita she is not comfortable, Ajiddeh ya duba yaga tana ta fushi, rage volume 膹in music yayi sannan ya kallota a hankali yace "Babe meye ne kike ta b'ata rai", zumb'uro bakinta ta sakeyi ta juyar da kanta ga kallon window, bai sake bi ta kanta ba yaci gaba da tuk'in shi cikin kwanciyar hankali har suka isa wuse II, gaban wani tangamemen gate ya tsaya yayi horn, mai gadi ne ya bu膹e mishi ya sa kai ya shiga, yana shiga ya nemi waje yayi parking, Ajiddeh ce ta fito daga motan shima ya bita suka fita a tare, zagayawa yayi ta b'angarenta yayi mata magana, "wai fushin mey kike yi ne haka, tun a wajen event 膹in naga kina ta b'ata rai bayan kuma lafiya muka fito", ce mishi tayi yarinyar nan wacece, meye ha膹inka da ita da har za a ce kuyi snapping picture daga kai har ita sannan taqi bin motar gidansu sai naku", juyawa yayi ya dubi motar ya kalli Batuul dake danna waya kanta sunkuye, side view 膹inta ake gani da lashes 膹inta da suka kwanta, kallon da taga yana yiwa Batuul ne ya sata cewa "Aliyu da kai fa nake magana", juyowa yayi yace mata "she is my cousin", kallon mamaki ta bishi dashi dan tasan almost duka cousin 膹inshi, beside ai taga yarinyar y'ar minister ce kuma bai tab'a ce mata minister 膹an uwansu bane, cikin rashin yadda tace "Aliyu baka tab'a ce min a cousins 膹inka akwai yarinyar nan ba, ni gaba 膹aya naji bana sonta" ce mata yayi "well there is a first time for everything, yau kin santa", shi da kanshi mamakin kanshi yayi, why did he lie, mey sa yace Batuul cousin 膹inshi ce bayan ba haka abun yake ba, ce mishi ta sake "Fine naji, but duk cousins 膹inka i like her least, infact i dislike her", da mamaki ya dubet yace "contro, ki tuna da wanda kike magana, i told you she is my family and you are telling it to my face that you dont like her, kar ki manta we are getting married next three weeks, you cant just disregard duk wanda kika ga dama", ranshi da ta gani ya b'aci ne sosai yasa tace "Baby am sorry, i dunno, am just pessimistic about her, i have this negative feelingl, haushi ta bashi yace mata "naji am going, we will talk later", tunda ya shiga mota take tsaye a wajen, tasan halinshi baya son wasa, bare in ranshi ya b'aci, yanxun ma haka tasan sai tayi dagaske zata shawo kanshi, yadda ya figi motan ne kamar mai shirin tashi sama ya fita daga gate 膹in gidan, ya tsorata su Batuul ba ka膹an ba, maza maza ta jawo seat belt zata saka kenan suka ha膹a ido, wani kallo ya sakar mata tayi saurin sauk'e kanta a sanyaye, a ranta fa膹i tayi "kai ka sani, haka kawai kayi ta b'ata rai kana b'atawa kanka rai, ai matar ma da zata aureka ina tausayamata", Farida ce ta matso kusa da Batuul tace cikin ra膹a "yaje ta b'ata mishi rai shine zaizo ya sauk'e a kanmu, ai ka膹an ma ya gani sai ya aureta, dan da gani wannan babu abinda ta iya sai kwalliya, mu dai kar yaje ya zubar da mu", murmushi Batuul tayi tace "kai Farida ke dai , nidai babu ruwana", a wani brake sukaji yaja a gefen titi, tare suka 膹ago suka dubeshi dan suga abinda ya faru dan su suna ma ce hatsari akayi, ganin da sukayi lafiya yasa su ajiyar zuciya, cikin dakewar murya yace "膹aya ta dawo gaba", a tare suka 膹ago suka dubi junansu, Farida ce tayi saurin cewa "Batuul kije gaba", a razane Batuul ta kalli Farida, a ranta cewa tayi "Farida are you sick, ya za ayi kice inje gba", ce mata tayi " No am okay here ke kije", cewa Farida tayi kinga ni am by d road, kuma highway ne its risky in bu膹e k'ofa.....", bai bari ta k'atasa magana ba yayi magana cikin tsawa yace "kuna b'ata min lokaci, 膹aya ta dawo gaba, ba driver 膹inku bane ni", bu膹e k'ofan Batuul tayi ta koma front seat dan ta tsani ihu, tana shiga ya figi motar da k'arfi, sauk'e kanta tayi ta sa a tsakanin cinyoyinta dan k'amshin turarenshi ya isheta ta bugun da zuciyarta keyi, kallon ta yayi ta gefen ido yaga ko she is fine sannan ya k'arasa dasu gida
Chapter 15 · 0% Book details