← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 166

Sashe 145

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

Da yamma aka dawo dasu Mum asibiti aka wuce dasu kai tsaye, ita Jainaba, sai wata mata da Dad d'in bai Santa ba, babu wanda baiji mugun ciwo ba cikinsu, Da ya dawo gida suka taho tareda Ajiddeh, in banda kuka babu abinda Ajiddeh keyi, ta rasa bakin cewa komai, Zainab ma sai da Daddy ya qirata snn ta taho, itama kukan ta saka ganin yanayinsu, Dad baice musu komi ba ya tafi wajen Doctor, Doctor yayiwa Dad bayanin cewa Mum ta sami raunika hannu da k'afa da kuma spine d'inta, babu ita babu tafiya a yanzu, d'ayar matar kuma Brain d'inta ya tab'u amma suna fata in ta farfad'o a samu a sake dubawa, sai Jainba ita kuma hannayenta ne kawai suka ji raunin sai kuma kafar ta da sai an yanke sbd ya lalace, tunda doctor ya fara magana Dad ke danne zuciyarshi yana addu'a sbd wani irin abu da yakeji yana taso mishi, saida likita ya gama bayani yayi mishi godiya ya fita, gida ya wuce kai tsaye dan bayajin zai iya komawa cikin d'akin, har ya isa gida yana tunanin abinda ya kai Zuwaira Illorin.
[12/1, 15:42] 80k: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

94

By Phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Chapter 145 · 0% Book details