← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 166

Sashe 106

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ajiyar zuciya Jainaba ta sauk'e a fili ta furta "Lallai da aiki a gabanmu", sannan ta juya ta haura saman itama, a bakin k'ofa sukaci karo da Ajiddeh janye da akwati, da mamaki take kallon Ajiddeh sannan ta riqe akwatin tace "Keh meye hakan?, ina zaki da akwati", Ajiddeh tace "kema in zaki tattaro naki ki d'auko kizo mu wuce dan ni na gama zaman gidan nan indai wannan bak'ar yarinyar tana nan, ni wlhy right from day one ba santa nakeyi ba, bare yanzu da tazo ta tare take zama min a gida, gashi har wata suka k'aro mishi dan munafurci da sa ido", kuka sosai ta fashe da, Aunty Jainaba ta ja ta suka koma dakim ta zaunar da ita, Fridge ta bud'e ta mik'o mata ruwa, ta sha sannan ta karb'a ta ajiye tace "ashe keh bakida hankali ban sani ba Ajiddeh, ashe ba da kai kike tunani ba?", kallonta Ajiddeh tayi hawaye na sakko mata tace "ban gane ba", zama itama Jainaban tayi daga gefenta tace "Gashi ko kin nunamin alamu, in banda rashin hankalinki ina kika kinkimi akwati zaki da?, wa yace miki ana yiwa namiji haka bare wannan mijin naki d'an isa da kallo ma mutane basu isheshi ba, kina gani fa ko kunyata baiji ba ya sharara miki mari, toh ina ga in kin bar gidan, ai sai abinda yaci gaba, duk danginmu kaf cikinmu babu wanda ya tab'a auren mai irin kud'in mijinki kin sani, duk da kema naki uban nada kud'i amma ko k'afar nashi uban bai kamo, gashi shima yaro dashi amma arzik'inshi yafi k'arfinshi gashi komai kikace kinaso sai ma ya miki dad'i badai ragi ba, zancen zaki bar mishi gida bai zo ba, Allah ne yayi zanzo inga rashin hankalin da kike kwab'awa, duk da nazo da shiri amma dai nasan sai mun sake akan nada, wannan duk yadda akayi ya riqe ibadarsa sosai shi yake hana aikinmu ya kamashi, kuma ina jin iyayensa ma basu bar shi haka ba, yanzu watanmu uku muna abu d'aya amma bama tab'a cin nasara, wannan karan kuwa ba da wasa zamu shigeshi ba, itama wannan yarinyar gaba d'aya b'atar da ita zamu sa ayi tunda har a dalilinta yake marinki, dan haka dole ne abi ta kanta a magance matsala, sati d'ayan da nazo yi na fasashi, jibin nan zan koma in fad'awa Yaya duk abinda ake ciki, sosai zamu tashi tsaye akanshi, sai mun sa ya gwammace kid'a da karatu", kamar wata wawiya tana nan zaune har sai da junaiba ta gama sannan tace "Toh yanxu ya zanyi, dan ni duk matar da ta rab'eshi ko tace zata shigo rayuwarshi wlhy Allah sai na hallaka koma wacece, sai dai nima a kasheni, Anty baxa ki gane irin son da nake ma Aliyu ba" cikin matsanancin kuka ta kare maganar, junaiba ta sauke ajiyar xuciya tace "Ai babu wani zancen wata matar in ba ke zakiyi sake ki bashi dama ba, yanzu ki tashi ki kintsa kije ki bashi hak'uri daga nan sai kiyi mishi zancen tafiyata dan ya bamu d'an tsoka mu samu na aikin, suma Malaman na yanzu ba abin yadda bane sai kaga da k'yar ake samun na gaske, dubi fa abinda wannan d'an isakan mutumin yayi mana", mikewa Ajiddeh tayi har lkcn xuciyarta na tafarfasa don da xa a bata wuka a lkcn babu abinda xae hanata caka ma Batuul, Allah sa ma cikin ne jikinta kamar yanda take xargi, shikenan xamanta ya xo karshe gidan cikin ruwan sanyi, kwafa tayi ta mik'e ta shiga cire kayan jikinta tana naxarin abinda Anty jainaba tace.

Ficewa Farida tayi daga dakin tana xumbura baki a xuciyarta tace "Ae ko da na kira maka Ammah yanxun nan, kuma in fita in fasa gaskiyan komai" bin ta yayi da harara sannan ya dawo daga gefen Batuul fuskarsa daure, kamar bata ganshi ba ta mik'e k'afafuwa zata kwanta ya rik'ota cikin kaushin murya yace "I will slap you idan baki tsaya kin saurareni ba", kuka ta fashe masa da, nan da nan ya rude ya dago kanta yace "me ya faru kuma, me nayi maki" kin cewa komai tayi sai kukan da take, nan ya shiga rarrashinta kamar wata jaririya, da kyar ya samu tayi shiru, ya rungumota jikinsa ya lumshe ido yayi shiru, mamakin kansa kawai yake, ya rasa gane dalilin da yasa yake behaving haka, maganar Ajiddeh ne ya fado masa, ya bude idonsa a hankali yace "Are you noticing some changes a jikinki?, I mean do you feel anything unusual?", had'e rai tayi ta dago kai tana kallonshi tace "Meye toh kake tambayata", yanda ta had'e ran ne ya kusa bashi dariya amma ya dake yace "wai yaushe kika koyi rashin kunya ne, ina miki magana kina had'e min rai, ehhn tell me", ya k'arashe maganan tareda zame mata hular dake kanta, tsuke mishi baki tayi tace "Ina ruwanka da hulata da zaka ciremin, ni ka maida min abuna", yace "bazan mayar ba har sai kin fad'a min mey ya canja ki lokaci d'aya", sake had'e fuska tayi tace "wai wani canjawa, ni dama can haka nake kaine baka sani ba", dariya yayi yace "d'azu fa naga har my wi.....", sai ya tuna alk'awarin da yayi mata na cewa bai sake k'iran Ajiddeh da my wife gabanta, kwana biyu bata yi kuka ba har wani dad'i yakeji, kallonta yayi yaga ta tsareshi da ido yace " I meant Ajiddeh, d'azu har gani nayi kin kare kanki gunta, hmmm I lyk that courage, d new you, but banda wannan sabon attitude d'in towards me, kuma idan xaki mata fitsaran ki tabbatar ina gida", kallonshi tayi ta d'an tabe baki tace "ni ka tafi bacci zanyi", yace "bacci? mey ke damunki ne, we have to see a doctor, dan baccin nan naki ba na lafiya bane", zumb'uro mishi baki tayi tace "inji waye banida lafiya, am fit and fine", yace "ina wani fit and fine, bakida aiki sai amai da bacci, ko breakfast ma bakiyi ba yanzu, ko jiya ma bakici dinner ba", kamar jira takeyi ya gama magana tace "Yawwa kaga ma ko, ice cream nakeso in sha yau ma, amma ba na Gelatorino ba yau, na Cold stone nakeso, sai ka siyo ma farida breakfast", kallonta kawai ya tsaya yi yadda cute lips d'inta ke moving, ganin baice komai ba ta tsuke baki tace "I knew it dama baza kayi min ba, toh kaje zanyi da kaina", lumshe ido yayi ya janyota ya had'ata da jikinshi ya shiga kissing d'inta passionately, ita kam sai tutturashi takeyi amma yaqi saketa, Farida ce ta tura k'ofan d'akin ta shigo riqe da waya, turasa Batuul tayi da sauri ta koma baya, ganin condition d'in da suke ciki yasa tayi maza ta juya ta riqe bakinta tace "Oooops, am sorry, Ammah ke son yin magana da Batuul", Batuul dai kasa d'agowa tayi ta kalleta sai shine da ya bita da harara yace "out", da sauri taja musu k'ofar ta fita tana kyalkyala dariya.
馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

71___72

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Chapter 106 · 0% Book details