← Book details Batuul Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 166

Sashe 160

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tukunna ya d'ago hab'arta da hannunshi d'aya yana k'arewa fuskarta kallo yace "I need not say a lot Hauwa, idona ya gama ganemin komai akanki yanzu, I can clearly see the better changes in you, ina fad'amiki hakan ne bawai dan inason kisan how worthy and valuable Fatima is to me ba, nasan tun kamin wannan lokacin kinsan ya take a wajena, am telling you this dan ke kisan worth d'inta, am here because of her, tamin kuka, tamin magiya duk dan in maidaki tun bata san mey kika aikata ba har bayan ta sani hakan bai hanata yimin magiyar in yafe miki ba", hawayen da take ta k'ok'arin maidawa kar su zubo suka shiga zarya, kuka takeyi na nadaman abinda tayiwa Batuul d'in, ta cutar da ita amma ita da alheri take binta, yaci gaba "babu amfanin maida abinda ya wuce, Marrying her was never her choice, I married her tun bataso but sbd iyayenta, she obeyed them, she sacrificed her happiness for them to be happy and satisfied with her, it was never her fault, keh kinsan I had no intention of keeping a second wife, but yaya zanyi, you caused everything, you made me fall into it, bani kad'ai ba, har parents d'ina saida ya shafa, I can't say no to them, I had to do it a lokacin da suke so inyi d'in, everything happened so fast, I know you will be furious in har kika ji zancen, dukda ban san ya zanyi ba a lokacin nasan babu yadda za ayi in rabu da Batuul, badan ma su Ammah ba sai dan she had been a part of me tun kamin in san da zancen ita zan aura, I wanted telling you a lokacin, I couldn't get how, ban taba sawa a kaina ta haka zaki san matsayin Batuul ba a wajena, am sorry for everything", kukanta ta tsananta tana nadamar duk wani mugun abu da tayi tun kamin zuwaan Batuul gidan har lokacin da tasan matsayinta, murya cikeda kuka tace "Ni zance kuyi hak'uri, wacece ni da zan hana abinda Alllah ya hallata, na d'auka komai nakeso zan samu at my own disposal, nayi watsi da rahamar da Allah yayi min naqi bin umarninsa ai dole inga ba daidai ba", sam ya kasa yarda da Ajiddeh ce gabanshi yau take maganan masu hankali, ajiyar zuciya ta Sauk'e tace "How is she?", girarshi d'aya ya d'age alamar tambayn wa kenan?, a hankali ta furta "Batuul", wani wide smile ta gani shimfid'e kan fuskarshi jin ta ambaci sunan Batuul, tun d'azu yake son yaje ya sake ganinsu itada Babynshi, itama murmushin tayi ganin yanda murmushin yayi mishi kyau yace "She gave birth today, yanzu hakaR tana asibiti, I came to fulfill her promise", ido Ajiddeh ta wara tana dad'a widening smile d'inta tace "Aliyu dagaske?, yaushe ta haihu?, Ya Allah mey ta samu?, plss muje in ganta kaji?, plsss" murmushi yayi yana mik'ewa yace "d'azu, su nake son zuwa in duba, we will talk ltr", kamin tayi magana har yayi gaba kamar wanda ake turawa, har yaje bakin k'ofa ya tuna da Mum, juyowa yayi suka kusa cin karo yayi maza ya rik'ota, ko bata fad'a ba response d'in da jikinta keyi ya isar ya nuna mishi tayi missing d'inshi, murmushi yayi a hankali yayi leaning yayi kissing d'inta, saida ya saketa yana maida numfashi yace "Zaki sani yin abin kunya gidan surukai ko", murmushi tayi tareda lumshe ido tana godewa Allah da ya dawo mata da Aliyu tace "kaima ai gidankune", yace "Mum fa?", take murmushin dake fuskanta ya b'ace, a sanyaye tace "Its been seven months tunda Mum ta kwanta ciwo, ka tuna lokacin da nake ta k'iranka baka picking, I tot I dd lose her, inaso ko sau d'aya ka ganta ka yafe mata itama kai da su Fatima but duk inda nabi bana samun nasara", hannun ta dake hannunshi ya damqe yace "Tana gidane har yanzu?", ta kad'a kai tace "Yeah tana side d'inta", ya jawota gabanshi yace "Muje in dubata before I go", ba musu ta bishi a baya har side d'in Mum, saida ta fara shiga kamin ta fito tace ya shiga shima, Mum zaune cikin wheelchair duk ta rame kamar ba ita ba, tana ganin Abutturab hawaye ya fara zaryo mata, akan cutar da wannan bawan Allah taga ishara, gata nan zaune babu abinda zata iya yiwa kanta saidai ayi mata dashi, tana ji tana gani, har k'asa ya tsuguna ya gaida ta cikeda girmamawa, sosai ta nemi da su yafe mata su dukkansu tace kuma har gida zatazo ta samu su Batuul su yafe mata, Abutturab kam kasa cewa komai yayi, wai wannan itace Mum da last time da ya ganta tana ta bambamin anyi y'arta sharri baza ta yadda ba yau itace zaune haka bata iyawa kanta komai, dama in baka godewa Rahamar Allah ba ai ka godewa azabarsa, tun da lafiyarka baka more shi ba gashi yanzu kana nema ma babu hali, mik'ewa yayi bayan sun gaisa ya fad'awa Mum abinda ya kawoshi snn yayi sallama da ita akan anytime suka gama shirya Ajiddeh sai ayi mishi magana, murna fal ran Mum ta dinga mishi godiya, har mota Ajiddeh ta rakashi kamar kar ya tafi ta dinga ji, so yake kawai ya ganshi kusa da Batuul, a mota ya tarar da Massa yana jiranshi, sallama sukayi suka wuce, a hanya Massa ke fad'a mishi Ammah ta kirashi akan anyi discharging Batuul, da sauri ya ciro wayarsa cikin aljihu, missed calls ya gani nasu Ammah da sauran mutane kasancewar wayan na silent, number Batuul kawai yayi dialling dukda baiga missed call d'inta ba, bugu biyu ta d'aga, cikin siririyar muryarta tace "Hello", ajiyar zuciya ya sauk'e yace "Glitterrr", jin yanda yaja sunan nata tasan something is wrong, kamin tace wani abu yace "Glitter sun tafi min da ku ko?", murmusshi tayi kaman yana gabanta a hnakali tace "All thanks to Aunty, tace da nan da can d'in duk d'aya ne, duk care d'in da zata bani Ammah will give me better, taqi a tafi dani gidanta, I know you will be happy shiyasa banyi insisting ba", wani irin dogon ajiyan zuciya ya sauk'e yana fad'in "Alhamdulillah, Glitter! Allah ya k'arawa Aunty tsawon rai, lafiya da Imani, Aunty is the best kin sani ko", sosai Addu'ar tayi mata dad'i tace "Amin Yaa Abu", yace "Twinkle fa?, bacci take ko?", d'an yatsina fuska tayi dan bata gane wa yake nufi ba tace "Waye kenan?", yace "Glitter mana, bayan ke akwai wanda zan tambaya at this right moment bayan Babyna?", kai ta kad'a tana dariya tace "Ohhh sunan da ka saka mata kenan?", yace "Yeah, she twinkles kamar yadda kike glitter, she so cute, dama na fad'a miki I want a baby just like you, God has answered my prayers, Thank you kinji, Allah yayi miki albarka", dariya tayi tace "Amin Amore, Kaji Ammah na cewa in huta", yace yanzu zan k'araso ne ai, babu mai hanani ganinki, you rest well kinji, take care of yourself and twinkle for me", ido lumshe ta amsa da "sure I will do that", ajiyar zuciya ya sauk'e tareda sauk'e wayan ya juya yana kallon Massa da gaba d'aya hankalinshi ke kan driving, hira suka shiga yi har suka isa gida dab da magrib, saida suka fara yin sallah masallacin dake jikin gidan kamin su shiga gida, har mamakin matan dake gidan yayi kamar yau ake taron sunan, kukkutsawa ya riqayi suna gaisawa har ya samu ya shiga d'akin da ya San Batuul na ciki, wani irin serene and peaceful k'anshi d'akin yake, ga wani d'umi da d'akin yake, manyan burners d'in turaren wuta na k'asa a angle d'in d'akin har biyu, Batuul na kwance kan gadon itada jaririyarta, jingina yayi tareda k'ofan yana kallonsu tareda ajiyar zuciya, duk wani numfashi da zaiyi yana jin so da k'aunar halittun nan na Allah guda biyu da suka zama part of rayuwarshi cikin lokaci kad'an, a hankali ya tako ya k'araso bakin gadon tareda zama yana kallonsu, jin mutum kan gadon ya sata bud'e lumsassun idanunta ta sauk'e kanshi tareda mishi murmurs hi, murmushin shima yayi mata yana matsawa kusa da ita, tashi tayi tazauna tace "sannu da zuwa", baisan mey zai mata ya nuna mata farin cikinshi ba, hannu yasa ya zagayeta tareda rungumota jikinshi, murmushi tayi tareda yin lamo jikinshi tana jin dad'in d'umin dake jikinshi, kamar wacce ta tuna da wani abu tayi maza ta tashi daga jikinshi tana kallonshi, kallonta shima yakeyi dan wannan kallon nata bayason irinshi, langab'ar da kai yayi tareda d'age girarshi d'aya yana jiran jin mey zatace, a hankali har idonta ya fara kawo ruwa tace "your scent?, ban sanshi ba", gaba d'aya ya manta da ya rungume Ajiddeh, k'anshin turarenta ne dake jikinta ya kama mishi kaya shine Batuul taji yanzu, marairaicewa yayi kamar shima zaiyi hawayen shima yace "Fatima I went to her, ba kince in dawo da ita ba?", wani irin fad'uwa gabanta yayi, wlhy ta manta da tayi mishi zancen ya dawo da Ajiddeh, hannunta dake zagaye jikinshi ta k'arasa warwarewa, hannayen yayi maza ya rik'o yana girgiza mata kai yace "No Fatima, kefa kikace in dawo da ita, I gave you my word and I honoured it, for you, for your happiness", a hankali ta sauk'ar da idonta hawaye na gangarowa tace "I didn't say anything", ta fad'a tana kawar da kanta, hannu yasa ya tallabo fuskarta yace "Look at me kinji, plsss", a hankali ta dubeshi yace "ya kikeso inyi Fatima?, I want you happy, mey kikeso inyi to keep you happy?", jiki a sanyaye tace "just love me, always", ta fad'a tana lafewa jikinshi, hugging d'inta yayi yana kissing goshinta yace "In sha Allah Fatima, to the best of my ability kinji?", kai ta gyad'a mishi kawai, saida aka k'ira isha kamin ya fita bayan yayita kwantar mata da hankali lokacin Farida da Aunty Amna sun shigo d'akin, Ranan Suna da asuba a masallalci bayan an idar da Sallah aka rad'awa Baby suna A'eesha(Fareeda), Sadiq ne ya fara k'iran Fareeda ya fad'a mata sunanta aka sawa Babyn, ihu ta saka, ta rasa ina zata saka kanta dan murna, duk wani angle d'in gidan saida tabi tana fad'awa kowa sunanta aka maidawa Baby,
Chapter 160 · 0% Book details