← Book details Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 87

Sashe 9

Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mami she s not my type, inakan searching murya ciki ciki yace I dont like girls that are so expose har sun iya tafiya kasashe on their own su kadai sarai Mami tajisa amman sai itama tayi kaman bata jisa ba tashiga danna wayanta har sukakai wani kantapareren gida kafinma yayi horn mai gadi yabude suka shiga ciki wasu yammata guda biyu wanda sukenan yaran da Allah yabama Mami suma ta IVF tasamesu suka fito da gudu ba identical twins bane daya na kama da Mami daya na kama da Babanta suna ihu Mami, Mami, shiya fara fitowa daga motan kallo daya yamusu kowacce ta juya dan babu dan kwali kansu yazagayo yabudema Mami baya tafito yakamata suka fara tafiya tana dariya tace Farida da Fa iza bansan me kallabi yamusu aduniya ba saida ya ijiyeta a katafaren falon yajuya yace m going back to the clinic zan taho miki da magani kafin Mami ta amsa yafice yaran suka fito da gudu jin yafita. EPISODE 6 Da kyar Ammi tasamu tasha Fanta waran ma bataci ba, sannan suka tafi waje suka tare keke suka shiga, suna shiga tai lamo jikin Ammi chan tafara lumlumshe idanu, Ammi tace Alhamdulillah bacci yazo ko Hajiya Amirah Miemie tace inaga alluran ne Ammi gyangyadi sosai tadinga yi tayi kadan tabude idanu har sukakai gida Ammi takamata tace sauko to sai muje ciki ki kwanta Miemie tabiya kudin keken suka shiga ciki. Babu motan Daddy a compound hakan yasa Ammi tagane yafita babu kowa a compound din cus tasan za aje karasa yima amarya jere ahaka har sukakai flat nasu, Miemie tabude kofa suka shiga direct Ammi tawuce da ita uwardaka ta kama hijabinta tacire tace muje bayi kiyi fitsari saikizo kiyi baccin har bayi Ammi takaita tai fitsarin suka fito Ammi takaita gado tazaunar da ita tana kokarin kwantar da ita tace kwanta toh kin kwanciya tayi tarike rigan Ammi gam, Miemie dake tsaye tace Ammi ai wlh saikin kwanta da ita, ni bari naje na daura abinci awuta, mezan daura? Ammi tace dafa kome kukeso me sauki dan taci abinci, ko zakisha tea ? Ta tambayi Amirah dabatai magana ba, cike da lallabawa Ammi ta kwanta tana kamota tace to kwanta kema kwantowa ahankali Amirah tayi dab da Ammi tana dan lumshe idanu kadan kadan na bacci Ammi duk tana kallonta cikeda so, kafin ahankali tabude idanunta sosai takai hannunta ahankali tadaura akan wuyan Ammi dayayi ja duk hannun Daddy awajen sabida shaketa da yayi jiya ita bamatajin ciwon nata jikin sabida na Amirah take, batamasan ko akwai tabo a wuyanta ba but from yanda Amirah ta taba wuyan tasan da wani abu awuyan dasauri takama hannunta tacire daga wuyanta tace wuyan hijabin dana saka ya kamanine saisa yayi ja, maza yi bacci, ga zafin jikin yasoma raguwa Alhamdulillah Ammi tasauke hannunta ta ijiye saman gado, sannan takai hannunta saman sumanta data kama mata jiya, tashafa ahankali cikin yar karaman murya tace suman nan yakamata a kitsa shi eh yammatan Ammi, yaushe zaki yarda ayi kitso? Har lokacin wuyan Ammi Amirah ke kallo da fararen idanunta hakan yasa Ammi kawai tajawota da sauri jikinta tasa kanta akirjinta ta kankameta ahankali tace Allah yabaki lafiya Aminatu na, maza yi bacci ijiyan zuciya Amirah ta sauke ahankali feeling very calm Ammi na shafa bayanta, ahankali Ammi tadingajin jikinta na sakewa this is always the easiest way that helps her sleep, within 2min bacci yayi awon gaba da ita mai karfin gaske, Ammi ta sauke ijiyan zuciya kafin tashiga jaye jikinta daga nata ahankali tatashi zaune ta gyaramata kwanciya takalli chocholate da Dr asibiti yabata dake hannunta gam har lokacin sai kawai tayi murmushi tasauka daga gadon tafita daga dakin tabar kofa abude sabida Amirah tawuce kitchen inda Miemie ke girki, Ammi tayi murmushi tace kawo girkin kema jeki huta kiyi karatun exam gobe Monday dasauri tace a Ammi kibarshi zanyi kinji Ammi na, kingaji, ga Amirah, ga Daddy, idan ni ban sanyayi miki ba Ammi wazaiyi shiru Ammi tayi tana kallon Miemie she s just 20, Amirah 21 amman she s so wise, smart and very kind, kasa magana Ammi tayi, ahankali tace Ammi I know why Ya Amirah tafasama Daddy kai jiya, sabida ya dakeki ne dasauri Ammi tace ke banson shirme, ta ina babanku yadakeni tsayar da wanke plates datakeyi tayi saita juyo takalli Ammi tace Ammi I know everything ni ba yarinya bane, kawai bana nuna miki nasan meke faruwa sabida tausayinki nakeji Ammi, kina fama da Amirah ga Daddy da baya sonki, bayason Ya Amirah, what are you still doing here? Kirabu dashi tunda baida imani hade fuska Ammi tayi tace kika kara magana akan mahaifinki haka saina bata miki rai Maryam, maza tashi anan jekiyi assignment dinki na school zan karasa girkin Sosai idanunta suka ciko da hawaye tawuce dasauri tafita tashiga dakin dake next to na Ammi wanda shine nasu itada Amirah amman condition na Amirah yasa adakin Ammi yawanci take kwana, tabude bayi dasauri ta shiga tamaida tarufe ta kunna pampo tana kuka sosai sometimes she wish dama itane ke haukan sabida karma tagane abinda Babanta kema Mamanta, Daddy mugu ne azzalumi, Abinda ke cimata rai shine hakurin Ammi kuma taki rabuwa dashi, mutum yana jibganki kullum amman kin zauna kuma kina girmamawa wannan wani irin abune eh, gashi baya bada ko biyar na sayama Ya Amirah magani duka kudin da yan uwan Ammi ke bata take hadawa take sayan ma Amirah magani, tarasa mesa he hates Amirah amman ita yana mata komi da komi. Shigowa gidan Daddy yayi dawasu karafan maza guda uku tika tika dasu dasu bouncers yana gyara belt na jikinsa ga katon bandage akansa yace yauwa kubiyoni, mahaukaciyar na flat dinnan kumuje yayi gaba, Ammi tana tsaye a kitchen taji an bugo kofa dan jim tayi duk fadan dazatama Miemie bata buge bugen kofa toh kodai Amirah ne ta tashi hakan yasa dasauri tasa hannu ta murza gas tana kashewa zata juyo taji muryan Daddy yace kushigo nace wani mummunan faduwa gaban Ammi yayi dasauri tai wajen kofan kitchen tabude Daddy tagani yana sanye da riga da wando na jean da shirt da belt dawasu kattai su uku yayi hanyar bedroom dinta yace tana nan dakin zoku bude yamatsa gefe dawani kalan sauri Ammi hartana neman tai tuntube ta taho wajen dasauri tace Daddy lafiya su waye wayan nan? Lafiya tai maganan tana karasa jawo kofan, wani kallon tsana yama Ammi batare daya kulata ba yace kai Lasdon bude kofan nace ku shiga ku daukota muje arude Ammi tawani sha gabansu tace tsaya ban ganeba wa za a dauko? Mesa kake aika mazan daban sani ba zuwa cikin turakata kasan munada yara mata idan basu da sutura ajiki fa ? Ammi tai maganan tana kama hannun kofan gabanta na faduwa sosai, ran Daddy yafara baci yanunata da tsaya yace ki kiyayeni Haleema, Haleema ki kiyayeni, ko tsirara mahaukaciyar yarki take I don t care, sabida akwai dubu irinta dake yawo tsirara a titi, yau saita bar gidana ta koma asibitin mahaukata, tunda haukan nata haryakai matsayin tana neman daukan rai, tana neman kasheni, ijiye yara irinsu a gida mummunan hadari ne ga alumma, inada yara kanana bazata halakamin gidaba dan haka ki matsa ga maza nan nakawo su daukanmin ita muwuce asibitin mahaukata tunda Ammi take bata tabajin tsoro ya shigeta ya ratsata irin na yau ba, amman tadaure tace Daddy nasan abinda tamaka jiya bata kyauta ba kuma duk bisa kuskure ne amman dan Allah kayakuri ka sallamesu su tafi idan yaso saika hukuntata anan kaji, amman mazan nan su dauketa akaita asibitin mahaukata duk bashine daidai ba ayanzu, wlh batada lpy yanzu nan muka dawo daga asibiti bacci ma take, tun jiya sai yanzu tasami bacci, na rokeka da girman Allah ubangijin daya hallicemu kayakuri kaji wani shegen kallon fitina Daddy yama Ammi sannan yadaki bango yace kinga Haleematu ko kinaso ko bakiso yoh ke ko zaki mutu anan naga walakiri na zaran ranki Billahillazi saina aika yarnan asibitin mahaukata itada gidana har abada, tagama zama gidana, taje chan cikin yan uwanta mahaukata tayi rayuwa, mahaukata irinsu masu kisan kai ba a barinsu rayuwa agida sai asibiti dan haka tun ina miki bayani dalla dalla kitashi daga jikin kofan nan inba hakaba zanyi mummunan saba miki Ayanda Ammi tasanshi tasan yanda baison Amirah bazata taba yarda da abinda zaiyi ba, ahankali tace idan na dauketa muka barmaka gidan ka fa? Wani dariya yayi yace nan ne kuma zan gwadamiki ubanki yayi kadan! Tunda bakene ubanta ba kowani hukunci na yanke akanta daidaine, Kai ku shiga ku daukomin ita Ammi ta tsaya gaban kofan tai ihu cikin dakewa tace babu wanda zai tabamin diya, Baban Baby wai menene haka ? Hayaniya da Miemie taji yasa takashe pampo da sauri tana goge fuskanta taji muryan Mami na ihu da Daddy dasauri tabude kofa tafito tafito daga dakin ganin maza saida gabanta yafadi dasauri takalli Ammi tace Ammi Ammi juyowa tayi ta kalleta ba hijabi kanta ba hula tace koma daki ki dauko mayafi maza Maryama kasa motsi tayi kukan datake rikewa tafashe da shi takalli Daddy cikin kuka tace Daddy maisa ka tsani maman mu eh? Meta maka ne? Karabu da ita idan baka sonta kadena azabtar mana da Maman mu D Maryam! Ammi tadaka mata mugun tsawa dayasa Amirah ta firgita tare da bude idanunta ras dasukai ja cike da bacci alluran da aka mata harda na bacci cus masu mental issue haka na bukatan bacci, Ammi tace Babanki kikema magana haka? Daddy yace ahap kungani ba, she poised my daughters mind against me, one tries to take my life yesterday and the other is insulting and abusing me yanzu, kinga tarbiyanki Haleema you see! Jin muryan Daddy wani kararrawa kan Amirah yafara bugawa, tana ganin jiri tashiga tashi all abinda ke zuwa kanta is Mamanta is in danger tashiga kalle kalle adakin tana neman abinda zata dauka babu wani makami the only thing idanunta suka gani is slippers kawai tadauki slippers tashiga tafiya bakinta na furta Ammi Ammi Ammi ahankali da bazama ka iyaji ba, Ammi na tsaye jikin kofan kawai taji an bude kofan dawani irin sauri tajuyo kowa ma yajuyo Amirah ne daga ita sai gown na jikinta ga gashinta
Chapter 9 · 0% Book details