Sashe 5
Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yayi kofa daidai ana bude kofa aka shigo Miemie ce idanunta sunyi ja alamun bacci, dawani irin sauri Daddy yace riketa Maryama zata kashemiki Daddy arude Miemie ta tare data biyo Babansu gadangadan tace Ya Amirah takai hannunta tariketa ta dasauri, wani tureta Amirah tafara kokarin yi taki barinta, Ammi tafito daga dakin wajen kofa dasuke da kyar, Miemie na ganin Ammi dudda tana fama da rike Amirah saida tace Ammi meyasameki ? Tahowa wajen Ammi tayi tace faduwa nayi Ammi takai hannunta zata karbe wukan tace bani wani ihu Amirah tayi taki basu da kyar Ammi suka karbe wukan, rawa jikinta yafara sosai ga jikinta da Ammi taji yadauki zafi kawai takamata ta kankame tace bani spirit da audugu Miemie kiga dasauri Miemie tai ciki tafito da audugu, Ammi tai juyin duniya tabude tafin hannunta da kyar tabude tazuba mata spirit a yankan wani irin ijiyan zuciya Amirah tasauke tahau motsi da hannun alamun abin yamata zafi amman babu wani reaction a fuskanta, jin yanda zuciyanta ke bugawa sannan har lokacin jikinta na rawa yasa Ammi tashiga shafa bayanta tace Amirah, Mirah ya isa kinji, calm down kinji, bani ruwa Maryam dasauri Miemie tawuce takawo ruwa a cup tazo wajen ta duka tace Ammi gashi tai maganan tana kallon Amirah dake jikin Ammi ta manne fuskanta a kirjin Ammi gabaki daya, Ammi ta karbi ruwan ahankali ta ijiye gefenta tasa hannu tadaura saman kanta tace taso ga ruwa sha kin dago kanta Amirah tayi, Ammi tai shiru kawai, Miemie tace tsaya Ammi tai murmushi tace Ya Amirah sha ruwa calm down Daddy ya tafi shiru Miemie tayi tana ganin ko kallonsu batayiba, saita kalli Ammi ahankali, Ammi keeps hiding it bataso su sani but tasani sarai Daddy na dukanta, from fuskan Ammi tadagani tasan dukanta yayi abinda yasa jikin Ya Amirah yatashi kenan hartamai haka, she just hates Daddy, tarasa maisa baya daraja Amminsu. Koda Baba yafito tabaya yazaga yashiga bangarensa har lokacin baya gani da kyau idanunsa dishi suke masa har lokacin kuma jini na diddiga, bedroom dinsa yashiga Maman Baby yagani wajen wardrobe dinsa tana maida zinarenta dan anan take boyewa bai dauka zai ganta a bangarensa ba salati tabuga ganin sa haka tace Innalillahi wa innailaihi raji un, hatsari kayi ko mene meya sameka Sweetheart? Tai maganan tana zuwa wajensa dasauri ta taresa, ahankali yace bani first aid box dasauri tace toh toh tawuce tadauko tazo ta ijiye bakin gadon while Daddy na karasa cire suit na jikinsa, yazauna bakin gadon Maman Baby tazuba spirit tazo tafara goge jinin goshinsa Daddy yace aashhh ahankali dasauri tace to, amma hatsari kayi ne? Yana runtse idanu sabida zafi yace mahaukaciyar yarinyar chan ce! Chak Maman Baby ta tsaya tace mene? Wannan jakan yarinyar tamaka haka? Gyadamata kai Daddy yayi rai abace Maman Baby tace aiko saina hallakata yau dan kutumar ubanta mijina zata kashemin ni zatasa atakaba, zata gane Maman Baby tajuya zata wuce dasauri Daddy yarike hannunta yace kinga zonan karkije yau hauka take sosai idan taje kema ta illata ki fa? Sumewa fa nayi warwas da yankani zatayi fa Maman Baby tace mene? Daddy yace daman tana haukacewa sosai haka cikin fushi Maman Baby tace ni bantaba gani ba, Alhaji gaskiya abin nan yayi yawa wlh bazan iyaba kadauki mataki ina dalili, ka aikata gidan mahaukata mana tabar mana gidan mu yara irinsu ba warkewa zasuyi ba tunda har takai shekaru ashirin da daya bata warkeba kakoga ai ciwon harna abada ne dan haka ka wurgata asibiti ta karasa rayuwanta achan muhututa, hakanan yar wasu zata hallakaka na cikinka basu hallakaba sai wacce bataka ba ina dalili iyye, inada yara ta kashemin kai waye zai zama ubansu, gaskiya taje chan gidan yan uwanta gidan mahaukata shiru Daddy yayi kaman mai tunani chan yace banki takiba Giwa amman gaskiya bazan miki karya ba bazan iya kashe kudadena akanta ba kinsan nawane asibitin mahaukata kuwa? Dasauri Maman Baby taduka agabansa kaman mai kneeling ganin ya yarda da maganan kudi yake tunani tace tsaya wlh ko sisi bazaka kasheba, ko jiya jiyan nan saida nagani a news cewa NGO na UNICEF sunzo sunyi renovating physciatrict world na Teaching hospital sun kawo kwararrun likitoci sunce zasuyi free komi na 2yrs duk wani mai ciwon hauka zai iya zuwa, project din is about making mahaukatan dake yawo a street sun Sami magani da kulawa, ka kaita wajen ka zubad da ita chan su karata Daddy yace are you sure komi free ne dan kwandalata bazai yi ciwo akanta ba Billahillazi Maman Baby tace da gaske nake nima ina zan barka ka kashe kudi akanta yoh menene amfaninsa Daddy yace shikenan Allah kaimu zan samo kattai dazasu daddauremin ita su dauketa su samin a mota saidai uwarta tamutu wlh amman saita tafi asibitin mahaukata wani murmushi Maman Baby tayi dan batada burin daya wuce taga Ammi na bakin ciki, yanda Ammi keson mahaukaciyan nan rabata da ita sai yakusan kaita lahira sabida bakin ciki. Har wajajen 2 nadare Ammi bata runtsa ba Miemie harta sulale tai bacci anan kasa a gefensu, Amirah idanunta biyu har lokacin ta kankame Ammi kanta akan kirjin Ammi jikinta yayi zafi sosai, kawai tarikice, Ammi tai juyin duniya yarnan tasaketa amman Amirah taki, yawanci ciwonta yatashi this is how she becomes, lumshe idanu Ammi tayi tashafa bayanta ahankali tace I am fine Aminatu, kinji Mamana, I am fine wlh, faduwa fa nayi baki gani ba, kuma bawani abu babanki yaminba abu yazo ciremin awuya fa eh, sakeni muje gado ki kwanta taki sakin Ammi saima kara kankameta datayi, haka Ammi ta barta, ahaka bacci yadauketa ma sabida ta daku a hannun Babansu tagaji. Kiran sallan asuba yasa Ammi tabude idanunta batamasan ya akayi bacci yadauketa ba, kwance taganta kusa da Miemie dake bacci itama dasauri ta tashi zaune tana waige waige jin cingum dinta Amirah bata jikinta, zaune taga Amirah ga yawu na dilalowa daga bakinta she always does this idan tana zazzabi, dasauri Ammi ta taho wajenta ta kai hannunta wuyanta jikinta kaman wuta tace Innalillahi Amirah, Amirah amman batako motsi tashi Ammi tayi tana dagata takamata sai bayi ruwa mai dumi kadan tahada tana cire mata kaya Ammi tashiga watsa mata ruwan sannan tamata brush tadauki towel tafito da ita Miemie tagani zaune cikeda damuwa tace Ammi mukaita asibiti dasauri Ammi tace eh abinda zanyi kenan, hadomin tea nabata Miemie fita Miemie tayi daga dakin, Ammi ta ijiyeta agado tawuce wardrobe vest Ammi tadauka da pant sai wata gown na atampa da hijab, tsaf Ammi tasamata kayan bamata da karfi at all, Ammi ta fe samata body spray, Miemie takawo tea Ammi tace ijiye tea kizo muyi salla Ammi tadagata tasa akan dadduma tace muyi salla tama kasa tsayuwa Ammi ta zaunar da ita azauna tai sallan, suna idarwa Ammi tadauki tea tadeba a spoon takai bakinta kauda kai tayi takisha Ammi tace dan Allah kisha Amirah hannu tasa ahankali ta ture hannun Ammi alamun bataso sai kawai ta kwanto ta kwanta ajikin Ammi, Ammi tadagata ahankali tace rikemin ita Miemie bari na shirya dasauri Miemie ta karbeta yau batai musuba, Miemie cikeda so takai cup na tea bakinta tace Mai dadi nahadamiki fa, nasamiki madara dayawa sha kiji kauda kanta tayi sai kawai ta kwanto tadaura kanta akan cinyan Miemie ahankali tana lumshe idanu jikinta zafi radau, Miemie tashafa bayanta ahankali tace in sha Allah zakiji sauki kinji Fitowa Ammi tai daga bayin dasauri Amirah tayunkuro idanunta sunyi jajir na zazzzabi, Ammi tace kwanta ba inda zani Miemie tace kwanta Ya Amirah Ammi kaya zata saka yanzu sake komawa tayi ta kwanta dudda idanunta ba karfi amman sai in Ammi take da idanu, shiryawa Ammi tayi tsaf cikin atampa mai kyau da hijab dinta har kasa tadauki jaka tadaga kasan kayanta taciro wasu kudi 30k, tasaka a jakan sannan tadauki wayanta taduba account nata 10k gareta tai shiru. Saitazo dasauri Amirah ta tashi zaune ganin Ammi, takama Amirah tataso da kyar Ammi tace samo mana keke Miemie dasauri Miemie tadauki hijab dinta tace tafice. Wani maroon hijab mai hula a goge tsaf Ammi ta warware tasakama tana gyara zaman hijab din, yamata bala in kyau, Ammi na kallon idanunta tace bari asaka kwalli a idanun nan Ammi tamika hannu tadauki kwalli tana shirin budewa Amirah ta kifa fuskanta a wuyan Ammi alamun bataso sai kawai Ammi ta ijiye, crocks tasamata pink masu cute charms a sama na spelling din Barbie wanda aikin Miemie ne ita ta mammakalasu, saiga Miemie tashigo tace Ammi nasami keke muje Ammi tace bazaki zauna kiyi karatu ba exam gareki ba ? Dasauri tace Ammi dan Allah zan biku Ammi bata ce komiba, kawai takama Amirah da kafa takeja kawai jikinta nadam rawa suka fito Miemie ta kulle kofansu ta taya Ammi suka kama Amirah har kofar gida suka saka ta a tsakiya keken yajasu tana jikin Ammi har sukakai general asibiti wuraren 7:30. Dudda sammakon dasukayi haka mutanen dake wajen sunfi 100, Ammi tasami waje ta zaunar da ita tana share mata baki da handkerchief Miemie ta zauna Ammi tace bari nabada katinki tajuya dasauri Amirah takama hijabin Ammi tawani tsandara ihu da saida gabaki dayan GOPD yadauka aka jujjuyo ana kallonsu tawani mike Miemie ma tamike jikin Amirah har kyarma yake yawu na fitowa sosai, sai kawai dasauri Ammi tazauna tana bama Miemie katin tace kai katin wajen chan Maryam bazata bari naje ba taga jama a zata fara kuma dasauri Amirah tawani rukunkumi Ammi sai kallonsu ake, Miemie taje gaban kanta, tabada katin matar dake wajen takarbi katin tabude tace Aminatu Adamu, what is wrong meyakawo ki ganin likita? Dasauri Miemie tace bani bane y ayatace, gatachan batada lafiya tanuna Amira dake jikin Ammi fuskanta a kirjin Ammi dake kallon wajen, Matan ta kallosu saita cigaba da rubutu tace okay meke damunta? Shiru Miemie tayi tarasama mezatace kawai saita taba kanta ahankali tace tanada matsalan uhmm amman zazzabi take tai shiru, Matan takarasa rubutu sannan tabama Miemie katin back tace likitansu will be here by 9 zaku jira, consultation is free amman zaku biya kudin number Miemie ta Gyadamata kai tace okay nawa ne? Matan tace ga account counter chan achan zaku biya 5k gyadamata kai Miemie tayi tace nagode Miemie tawuce wajen Ammi tace Ammi doctor