Sashe 47
Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yanayinsa daman yagaya musu ina zaije daki yashiga yace zo Maman Amirah da Lami dasauri Lami tabi Baffa ciki Ammi takalli Amirah dakecin kaza abinta tace Miemie karki bari taje wajen rijiya Miemie tace toh Ammi tafito tazo zata cigaba da mata tsifan Amirah ta make mai cikin tar kannauwan murya tace naki zafi Uwardaka Baffa yashiga Lami tabiyosa dasauri tace meya faru Babansu? Mesa kai wani iri haka? Daidai Ammi tai sallama Lami tace shigo shigo Maman Amirah labule Ammi tadaga tashigo tana kallon Baffa daya zauna bakin gado saitaja kujeran dake gaban dressing mirror ta zauna takalli Baffa tace Baffa meya faru? Karka wani damu kanka indai mutumin nanne, meya faru? Ammi ta kallesa sosai tana jira yayi magana, ijiyan zuciya Baffa yasauke ahankali yace Haleematu ammm yasake shiru sai gaban Ammi tashiga bugawa sosai, ahankali Baffa yace mutumin nan ya aurar da Amirah! Wani kalan zabura Ammi tayi tamike tsaye Lami ma haka ta dafe kirji tace Innalillahi wa innailaihi raji un, Amirah ya aurar Baffa yadan sauke ijiyan zuciya yace kodanakai masallacin naga mutane yace na zauna zamuyi magana bayan an daura auren nan kawai jinayi ana daurama Amirah aure, aka gama yakirani zuwa motansa yabani dubu dari biyar cikin miliyan daya na sadakinta wai nakawo miki, nabar masa kudin awajen yace zai bada address namu azo daukan Amarya kirjin Ammi bugawa yake sosai ba wasaba, saita koma ta zauna ahankali takai hannu tadaura hannunta saman fuskanta brain dinta was blocked for a moment saita kalli Baffa da murya wanda bazaka iya tantance wani yanayi take cikiba tace kasan wanda ya aura mata Yaya? Ahankali Abba yace that is where it gets complicated sabida Yusuf cewa yayi wai yayan yakamata ya aureta sai kuma aka aurama kanin Dr Marwan! Dawani kalan sauri Ammi takalli Baffa, Baffa yace kuma mahaifin ya sanar a masallaci cewan yayi hatsari yana asibiti iyakan abinda nasani kenan Ammi tai shiru tai mutuwan zaune yaya yakamata ya auri Amirah sai aka bama kani wanda ke asibiti in all this thing the only person data sani is Marwan, da Yaushe har sukaje neman auren Amirah ita tana mahaifiyar Amirah batasan komiba, Dr Marwan bata taba ganin alamun yana son diyarta ba, wayan nan mutanen dasauri Ammi tace yaya zaka iyamin kwatancen uban angon? Baffa yace yanada jiki da katon ciki haka yanasa glasses a idanu gemunsa fari tabbas sune wayanda yagani rannan da sukaje inda Marwan yake does that mean wanda yaduka ya gaidata dinnan shine Saleem din sai yafasa aurenta maybe sabida mahaifin najin kunya sai aka bawa Dr ita, wani abu taji a wuyanta, saitaji zafi aranta badan komiba saidan cewa Dr Marwan datake ganinsa mai amana yasan da anason diyarta bai sanar da itaba, ahankali Baffa yace dakata Haleematu yawanci akaga diya anaso uba ake nema ama magana ba uwa ba kada ki fushi dashi wannan itace gaskiya! Ammi bamatasan maganan zucin datayi awaje tayisa ba, mikewa tayi azuciye dasauri Baffa yace ina zaki? Batare da Ammi tajuyoba tace zanje naga mutumin nan nanne fuu zata fice a falo Baffa yaci mata yarike mata hannu yace Haleematou! Dasauri Ammi tajuyo tace Yaya me kakeso nayi look at her kalleta! Tanuna Amirah dake compound kan tabarma Miemie namata tsifa saura guda daya hannuwanta biyu duka abaki tace Yaya kai karan kanka zaka yarda a aurar da yarinya mai kalan wannan laluran me aure zai amfaneta dashi eh? Ka kalleta Yaya Baffa yace nasani Haleematu but fushi baya maganin komi ki tsaya ayi magana Asan yanda zamubi abim nan cikeda hikima dan aure fa ya dauru unless mijinta ne ya saketa kokuma kotu taraba aure amman dai Amirah kam ta auru MATAR wani ce yanzu hawaye masu zafi Ammi suka fito daga idanunta, Baffa yace I know what you re feeling amatsayina na babba abu daya zan gayamiki tashin hankali baida amfani karki manta abinda aka gayamiki game da Amirah bata kaynar ganinki cikin tashin hankali ko damuwa dan warke wan nan da muka samu tayi zata koma gidan jiyane, da Dane kin isa kibar Amirah kizo nan bata biyoki ba? Ammi ta girgizamai kai Ammi tace to kingani, shi mutumin chan so yake ki biyosa kuyuta bala i kuma bazaki bisa ba, kome yayi yaje shida Allah, aure fa ta auru yabada iko yanada hurumin aurar da Amirah da Miemie dan haka kibar wannan I think ni atunanina tunda kunsan likitan nan amatsayinmu na manya mu nemesa da iyayensa mu sanar dasu laluran Amirah mu nemi yasaketa kawai Ahankali Ammi tace babu abinda bai sani kan Amirah ba anatse Baffa yace shine mutumin da Amirah tagayamin tanaso? Shiru Ammi tayi saita gyadamai kai, zatai magana sai Lami dasauri tace tsaya Maman Miemie, zuwa asibitin sa ya a Amirah taji sauki haka kinyi tunanin cewa tunda tana sonshi aurensa yasa kuma ta warke gabaki daya fa ? Ammi dasauri tace to shi yanasonta ne Lami? Shirme kawai Amirah takeyi? Yana likita akan wani dalili zai auri mai matsalan kai eh anatse Baffa yace banson ki nemi mutumin chan, ni zan nemi gidansu ko asibitin inda yake zaki gayamin naje nai magana dashi Ammi tadade tana kallon Baffa batai magana ba, Baffa yace I know you re hurting kiyakuri kinji hawaye ne masu zafi suka zubo daga idanun Ammi batasan metama Daddy ya tsaneta da yaranta hakaba amman dai tabarsa da Allah. EPISODE 4 Daga wajen daurin auren nan bayan ya gaggaisa da mutane driver ne yatuka Abba bai tsaya ko ina ba sai asibiti, Mami na zaune kan gadon kusada Marwan data ke basa oath da kanta da yau shiya tambayi oat din, yarame Mami tayi kuka fin adad bata taba sanin soyaya zata iyasa Marwan yafice hayyacin sa ba, wayanta ne yahau ringing hannu daya tasa zata dauka sai Marwan yasa hannunsa ahankali ya karbi bowl din yana magana kasa kasa yace take your call Mami Mami tadan kallesa taga yacigaba dashan Oats din ahankali, takai wayan kunne batamaso ta tambayesa an daura aure lafiya cus she s afraid she will hurt Marwan more sai kawai tai shiru, ahankali Abba yace fito parking space akwai maganan dazamuyi yanayinsa taji saitace okay tom saita kalli Marwan dayayi kaman baimasan da Abba take magana ba, tace Abban ka na kirana, ina zuwa Gyadamata kai kawai yayi baice komiba Mami tawuce tafita daga dakin tana gyara mayafinta tafito direct zuwa motan Abba daga ciki yabude mata baya tana zuwa saita shiga tana kallonsa baya farin ciki yana cikin damuwa tace baka da lafiya ne meya sameka? Takai hannunta zata taba jikinsa saiya kama hannunta tareda sauke ijiyan zuciya yace Zainab yau namiki laifi Abba yayi shiru Mami takasa magana gabanta sai faduwa yake Ahankali yace I know Marwan kanni ki ne, kece matsayin mahaifiya garesa amman yau amatsayina na wanda ya dauki Marwan dan cikinsa na dauki wani babban hukunci kanaa batare dana tambayi shawaran ki ba Abba yayi shiru saiyace babu abinda zan iya boye miki aduniya saiya bude wayansa yashiga chats na Saleem yace watch this video da zuciya daya Mami ta amsa tana danna video tai wani ihu ta yarda wayan kasa ta kulle idanunta tana salati Abba ma haka dukansu sunajin karan muryan Saleem da karan yanda yake sex dan Mami bata danna purse ba ta yarda wayan Abba ne yaduka yadauki wayan saiya tsaye da video yakalli Mami yace nasan bai dace na nuna mikiba but inaso kiga abinda ya tunzurani nayi abinda nayi ne yayi shiru yace bayan Saleem yaturomin video nan yakirani video call yana kan aikata alfashan sa idona idanun Saleem ya sanar dani shi bazai auri Amirah ba karuwansa yakeso ina miko magana lokacin biyu tawuce jama a birjik masallaci manyan mutane da fada aure bama a a ango ba zai zama abin kunya gareni da iyalaina dana sana ata, the only solution to the problem danagani is yaron daya daukeni tamkar mahaifi wanda bazai taba saba umarnina ba and bakowa bane wannan ba illa Marwan! Abba yayi shiru yana kallon Mami kaman yanda take kallonsa, saiya kama hannunta asanyaye yace I don t know idan zaki dauki abinda nayi kaman na cutar da kaninki ne na aura masa wacce bawai lafiya kaman kowa gareta ba, zaki iyamin kowani hukunci kikaga dama amman na aurama Marwan Amirah Sweetheart! Mami tadade tana kallonsa she s extremely happy dan yau takara yarda cewan Allah baya bacci kuma inhar mutum matarka ce ko anika kake sai tazama matarka, ciwon da Marwan yake yakici yaki cinyewa sabida mugun so dayakema yarinyar nan, Abba knows nothing about Marwan na sonta amman look at how ya aurama Marwan, soyayyan da Marwan kema Amirah is a secret wanda ba huruminta bane ta fadaba tunda shi Marwan bai fadaba itama ganewa tayi dan haka bazata fadama Abba ba, lumshe idanu tayi tabude ahankali asanyaye tace ka tabbatar da Saleem yafasa auren koko shaye shaye yasa ya furta haka banson abinda zai zama suzo suna ga maciji shida dan uwansa Marwan banso Alhaji Mami tafadi ciki da damuwa Girgiza mata kai Abba yayi bacin ransa nakara bayyana yace kinga Saleem! Saiyayi shiru yace banso na furta abinda ke zuciyana but I will tell you one thing wlh wlh koda ban aurama Marwan yarinyar nan ba bazan taba aurama Saleem itaba ko ina hauka yaje ya kashe yar mutane da kanjamao, koya dinga bata giya tanasha ko kayan hayaki, ai yaje chan ya auri daidai shi, nasan Saleem amanane amman baka iya tike amanan da baiso arike, nayi iyakan bakin kokarina, ni Saleem zai tozarta, ni zai aikama video alfashan dayakeyi sabida bai daukeni a matsayin komi ba i am nothing gani banza, ni Saleem zaima haka Abba is really really hurt Mami ta matse hannunsa ahankali tace ya isa, Allah ubangiji ya shiryar dashi, Allah ya ganar dashi gaskiya, Allah ya yafemak zunubansa Abba baice komiba yace muje naga d yabude mota yafito, Mami ma haka, suka wuce cikin hospital din Abba yana rike da certificate na aurensu wanda ayanzu manya manyan masallatai suke bayarwa, ahankali Mami tabude dakin da sallama Marwan na zaune yadan kishin gida, black tee ne ajikinsa mara any design sai white glasses a idanunsa, yayi wani haske, gashin kansa sun kara nannadewa sosai sabida yawan kwanciya dayake this days,