Sashe 62
Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wuya Amirah tayi idanunta na cicciko da hawayen dan wata uwar rigima ne ke taso mata, ahankali Mami takai hannayenta gefen fuskanta cikeda so tace menene Amirah ? Hannuwanta takai tadaura akan idanunta kawai saita rushe da kuka ahankali tana rerawa wlh kawai hankalin Mami tace tashi cus kukan seems like hurting cry irin abu namata ciwo a zuciya kukan datayi dazu na ciwon datakeji ne this are two different cries, dasauri Mami tace menene eh Ameen atu na? Menene ? Cikin kuka sosai Amirah tace ni zan tafi wajen Ammi naaaaa tasake rushewa da kukan kawai taji gidansu takeso taje wajen Amminta Mami takamata, ahankali tashige jikin Mami ta kankameta tanasa kanta a kirjin Mami tai lamo tana kuka while Mami na shafa bayanta tanadan jijjigata cikeda dabara tace to kinaso kije wajen Ammi saiki fara kuka ba fadamin kawai zakiyi ba, bakisan yammata basa kukaba, maza daina kuka, bari akawo miki abinci kici ki koshi sai muje wajen Ammi ko ? Gyadama Mami kai tayi ahankali tana sauke ijiyan zuciya tai lamoooo ajikinta tana dena kukan tana sauke ajiyan zuciya. Wani irin tausayi Mami taji tabata tace dena kukan abinki tohhh ya isa, maza zauna ga wayata ki danna bari naje nataho miki da abinci mai dadi Mami tabata wayanta karba tayi Mami tace zaunar da ita saita wuce, kasa tasauka tace Ammah hada abinci kiba twins su kaimata adakina dan tanason Amirah tadan saki jiki dasu hakan zai debe mata kewa kadan, saita juya takoma sama kai tsaye dakin Marwan tawuce ahankali tabude kofan Saleem tagani yarike sun fito daga bayi kaman amai yagama yi Marwan ya kwantar dashi akan gado yaja bargo yana rufa masa yana kallon Mami dake tahowa gaban gadon tace sannu Saleem, Allah baka lpy ina Saleem takansa yake ciwo yake sosai saita kalli Marwan daya dago yana kallonta suka hada idanu strictly tace matarka is here dawani kalan sauri yakalli Mami dan bai dauka ko kadan Amirah na nan ba yadai dauka dayaga Mami maybe tabar ko Ya Fadila tareda ita dan dasuka shigo yaga kowa afalon banda Ya Fadila, anatse Mami tace tunda baka tambayi ya jikinta ba bazaka je kaduba ta ba? Dan sauke kansa yayi kasa ahankali yace bari nagama da Saleem zanzo Mami Mami bata sake cemai komiba tajuya kawai tafita tarufo musu dakin Marwan yadanyi jimmmm yana kallon kofan saiya kalli Saleem da he was expecting ko zai tambaya wace Matar ake magana saiyaga fama yake da kansa kaman ma bai gane abinda ake ciki ba. EPISODE 6 Dakinta Mami tabude da sallama Farida tagani da Faiza ciki sun kawoma Amirah abinci bata taba abincin ba amman dai sai kallonsu take dudda bata kulasu ba, maida kofan Mami tayi tarufe ta taho wajen gadon tace kinga Twins sun kawo miki abinci, ga Farida nan Mami tace Farida come and say Hi to Matar Uncle dinki dasauri Farida tazo wajen tana murmushi sosai tamikama Amirah hannu tace Ya Amirah Hiiiiii tsareta da idanu Amirah tayi tana tuna rannan datagansu sun kama hannun Ya Marwan, tunda yaran Mami ne ai bakomi kenan, saita kalli hannun Farida da akama lalle ga mamakin dukansu sai Amirah takai hannunta ta taba lallen tai murmushi tace irin nawa nima anmini tanunama Farida hannunta wlh wani irin dadi Mami taji, tama Faiza alamu itama taje dasauri Faiza tazo itama tanunama Amirah nata tace kinga nawa harda kafa aka mana dasauri Amirah tanuna musu kafafunta tace nima anmini a kafa atare Faiza da Farida sukace. Wowww yayi kyau Ya Amirah dasauri tai murmushi tace nakuma ma yayi, Miemie ma an mata, Ya Umar yacemata yayi kyau Faiza tace Miemie sister ki ce? Gyadamusu kai Amirah tayi tace eh ta auri Ya Umar tana gidansa, inaso nakira Ya Miemie idan aka samin SIM card ganin tasaki jiki tana hira dasu sai Mami tace kutashi kuyi salla sai kuci abincin tare tare dukansu sukai salla Mami dakanta takawo musu more abinci atare sukaci Amirah was so free su Faiza sai surutu suke sata suma suna mata surutun cikon ikon Allah saita mance da maganan wajen Ammi zataje sAbida game suka fara bugawa da ita a iPad dinsu dukansu atare Amirah was so so happy. Saleem was very very sick da at a point saida Marwan yamasa allura ma, ko abincin da Mami ta aiko musu dashi baiciba kula da Saleem kawai yake. Bayan magrib Abba yashigo gidan dan Mami tasanar da shi Marwan yadawo da Saleem, ayanda Abba ke fushi da Saleem tunda yake baitaba kalan fushin nan dashi ba, Mami was even trying to calm him down ina sama yawuce kai tsaye dakin Marwan yashiga daidai bacci yadauki Saleem cikin tsananin fushi Abba yace me Saleem keyi cikin gidana? Yatashi ya tattara yakoma inda yafito ni nariga na yafesa yayi yaje yayi rayuwan dayaga daman yi fa Precious ko sauran matan banzan kome yaga dama yayi sauke kansa kasa Marwan yayi ahankali, Mami tasha gabansa tace haba Alhaji haba alhaji bansanka da fushi hakaba dan Allah calm down, Ameenatu is here tajika kana fada haka zata tsorata, look at Saleem he s so sick da baimasan mekake cewa ba dan Allah kayakuri Abba yace dakata please don t involve yourself anan sabida this time around babu wanda zan saurara wlh wlh kinji na rantse miki yakalli Marwan ransa a tsananin bace yace I don t care a ina kagansa ko a ina kasamo sa ni nabaka izinin kawomin shi gidana ? Kan Marwan na kasa dan yaga ran Abba abace yake sosai, cikeda masifa Abba yace wai kanama da hankali kuwa Marwan wannan yaron har zakaje ka nemo ka kawosa gidan nan inda matarka take, wannan bunsurun dake rayuwan dabbobi yahaye nan yahaye chan runtse idanu Marwan yayi wlh har cikin zuciyansa yaji kalman nan da Abba yafadi itama haka Mami bata san Abba ma da kalan masifan nan ba, amman tasan sex video nan was what completely pushed Abba to the wall, ahankali Marwan yace Abba dan Allah kaya kuri, kadena kiran dan uwana da suna mara kyau haka, kayakuri Abba! Shiruuu Abba yayi yana kallon Marwan da kansa ke kasa sosai mamaki ya kazhesa, asanyaye Marwan yadago kansa yadan kalli Abba saiyace nasan abubuwan da Saleem yayi bai kyautaba amman Abba koyaya yake dan uwanmu ne Saleem baida kowa saikai, banida inda zan kaisa inba nan ba gidan ka wajen dan uwansa, komin yaya yake hannunka baya rubewa kayanke kayar, kome Saleem yazama I will never give up on him, Abba don t give up on him either dan Allah Abba dan Allah! Marwan yayi maganan asanyaye yana rokon Abba dake kallonsa same thing with Mami, ahankali yace all this while yana nan bayan layinmu yau da asuba nafito daga masallaci naga motarsa saina bisa yashiga basu labarin komi har zuwa wajen mallam, ahankali yace after gobe in Sha Allah zai warke but dole ya dage da azkar na kariya da tsari wani dariya Abba yayi na manya yana kadakai yace kadan yagani! Saleem dai ba wallahi kadan yagani! Ai duk tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa zai dauka, badai sabon Allah ya sa agaba ba wlh wlh baiga komiba, gashinan tun aduniya yafara ganin sakamako, Allah yasama ba kanjamau yasamu ba cikin fushi Mami tace Alhaji menene haka wai haba dan Allah what if shiriyan sa ne yazo eh? I m not happy with the way kake magana akan Saleem haka nuna Saleem Abba yayi da yatsu shifa yariga ya dawo daga rakiyan Saleem ne gabaki daya yakasa mance yanda yagansa yanashan nonon karuwa yana gayamai yafasa aure, Saleem zai iya nuna masa karara yana zunubi, Abba yace wannan, wannan ya shiryu wannan? Abba yayi murmushi kawai yakada kai yajuya yawuce yafita daga dakin, Mami tabisa dasauri suka rufo kofan Marwan na tsaye wajen yana kallon kofan dakin, motsi yaji hakan yasa yajuyo Saleem yagani idanunsa biyu dasauri Marwan yawuce wajen gadon yaduka yana kallonsa ahankali cikeda kulawa yace katashi? Dan kallonsa Saleem yayi muryansa asanyaye yace ba bacci nakeba daman ai Marwan yayi turus yana kallonsa, Saleem yayi murmushi maidan ciwo yace yayana wanda muke jini daya ya tsaneni, he called me bunsu hannunsa Marwan yakai yadaura akan bakinsa, strictly yace t look at abubuwan daya fadi, he s angry, very very angry, his anger is justifiable, just get better Saleem and change kaji, babu amfani bin matan banza, at least yanzu kaga how dangerous they re look at abinda wannan tamaka da banzo ba da haka rayuwanka zai kare eh? Dan shiru Saleem yayi komi daya faru na dawomai tun rannan daurin auren da yanda Precious takira Abba yana kanta tsirara bai masan about the sex video ba but he knows about kiran Abba yana kan sha mata nono, ya runtse idanu baitabajin yayi nadaman abu kaman yanda yaji yayi nadaman ever stepping in that company har yaga precious yabita bayi yaciba he remembers clearly takaisa masallaci an daura musu aure, bude idanunsa yayi yace can i have a pen and paper ? Kallonsa Marwan yayi sai yatashi yaje gaban table nasa yadauki pen da jotter yazo wajen yabasa yunkurin tashi Saleem yayi yakasa Marwan dasauri yasa hannu yadagosa dan huci yayi na tsananin rashin lafiya saiya shiga rubutu. Ni Saleem nasaki precious saki daya saki biyu saki uku, ta aureni in a moment da baya hayyacina banda iko akan decision dina, saiyaba Marwan paper Marwan yasa hannu ahankali ya karba saiya karanta saiya kallesa saiya ijiye akan side drawer Marwan yadan kamasa yace koma ka kwanta hannun Marwan yarike ahankali dasauri Marwan ya kallesa, ahankali Saleem yace why are you not angry with me Marwan kaman su Yaya eh? Why? Beat me, fight me, show me you re angry Saleem yayi maganan yana huci, yace all I ever did was to hurt you guys why are you not angry zama ahankali Marwan yayi bakin gadon sai yadan sauke ijiyan zuciya ahankali yace I can never be angry with you Saleem Yadanyi shiru saiyayi murmushi yace ve always told you this, you re my brother through and through, I will never give up on you yayi shiru, chan yace I know all this jarabace, Allah ke testing naka bazan taba gajiya da kokarin kamoka na jawoka and bring you back to the