← Book details Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 87

Sashe 49

Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin kudin data samu banda gadon data siyama Miemie tasa musu babba adakin da katifa mai kyau babban gado ne da ita da yaran duka suna kai, Miemie ce char karshen gado Amirah ko saita tabiyo Ammi ta kwakumeta sannan take iya bacci, tsare fuskanta Ammi tayi da kallo, she just can t help it ne dazaran kanada d a dakeda damuwa you can t help it but to worry about yaron, tunaninta is tayaya wannan yar yarinyar da batasan komiba zatai aure, har yau har gobe tanama Amirah wanka ta shiryata da kanta, idan tana period ita ke shiryata, she knows tun suna yara tasa Amirah islamiyya but she s not even sure idan Amirah ta iya wani abu cus bata magana daga baya tazo tafara tsoron mutane hakanan tahakura tadena aikata islamiyyan, tasan cewa duk abinda aka koyama Miemie Islamiyya da gida idan tadawo tana koyama Amirah tare kuma sukeyi homework, but will she depend on that tace yarta tasan wani abu a islamiyya? Sabida condition nata Amirah bata taba azumi ba, tanasata tai salla but ita kanta Ammi batasan ko sallan ma mai kyau bace cus Amirah bata cikin yaran daza a kira da sunada cikakken hankali, as long as suna tare duk sallan da Ammi zatayi tana sata tayo alwala tare sukeyi, Amirah ko indomie batasan ya ake dafawa ba, ko tea Amirah bata taba dafawa da kanta ba, itada Miemie does everything for her, bata wanki saidai tasa hannu taita wasa da ruwan kumfa tanajin dadi idan taga Ammi na wanki tayaya Amirah zatai rayuwa gidan miji or is she thinking too much? Is she exaggerating? Ammi ta tambayi kanta, abu na farko kenan da Ammi ke tunani, bata kalli Amirah as wacce keda wayau na tarairayan miji, kula da muhalli da abincin da miji zai ci ba, idan aka koma kan bangaren tarayyan miji fa? Ammi tun yaranta na kanana 3yrs haka take dena cire kaya gabansu dan babu kyau, she s not even sure cewa Amirah tamasan ya jikin mata yake balle na maza, ko Miemie batajin Amirah ta taba wani ganin jikinta haka ba balle kuma namiji tayaya zasuyi wannan rayuwan? Mijin ta zai iya hakura bai nemeta ba har zuwa sanda zata warke tasan menene rayuwa? Tayaya Amirah zatai handling bukatan miji idan kuma Mijin mabukaci ne yaya diyarta zatayi? Will aure help condition Amirah kuwa koko it will make it worse? Dr Marwan dudda yanada kirki amatsayinsa na likita shin zai kasance yanada kirki a matsayinsa na miji? Zai kula da diyarta? Yanason diyarta kuwa tunda wanaa ne yaso diyarta shi yace yafasa aka aurama Dr, dan da Dr na son diyarta dashi zai fara fadi tunda ai shine likitan Amirah? Ammi takama nan takama chan tadamu gani take banda ita babu wanda zai iya kula mata da diyarta aduniya batason Amirah tafada hannun miji kalan u Daddy a azabartar mata da yarinya da daman bawai lafiyan ya isheta bane, yanzu yazatayi tajira su Baffa yaje yagansu tukunna ko mene?. Wuraren 7:00AM Baffa ya fito tsar gida ya shirya tsaf cikin shiddan sa mai kyau kal kal, Ammi dake shirya Amirah datai wanka tana jamata zip na bayan riga ne Baffa ya kwalama kira, Ammi tace maza to je wajen Miemie ta daura miki kallabi wucewa tayi wajen Miemie da ita tagama sa kaya Ammi tafice waje tace Baffa ina kwana amm ku tashi lpy zanje asibitin yanzu idan ba a sallamesu ba nagansu, idan kuma an sallamesu zanyi tambaya naga kozan gano gidansu gyadamasa kai Ammi tayi yawuce yaja Babur nasa yatafi. Wuraren 8:30 Baffa yakai asibitin yayi parking har room number Ammi tabashi saiya wuce yashiga yawuce sama. Tun jiya da daddare da Dr yazo yaduba Marwan yace zai sallamesa sosai yaga he was much better this morning zasu tafi, Abba ma da sassafe yazo dan dakansa yakeso yatafi da su, Marwan na zaune ya chanza kaya zuwa wasu simple t-shirt na wando black inda aka masa operation ma baya masa ciwo ya warke tass, Mami tahada komi, knocking akayi a kofan dukansu suka kalli kofan sai Abba dayafi kusada kofan yataho yasa hannu ya bude wani dattijo yagani that is dressed properly yana kamshi mai dadi looking homely kai tsaye yamika masa hannu suka gaisa Baffa yace amm kaine mahaifin Marwan? Nan ne dakin da Marwan yake ? Dasauri daga Mami har Marwan suka kallo kofa sai Abba yace eh nan ne bismillah Bismillah shigowa Baffa yayi kallo daya Marwan yamasa saiya sauke kansa kasa cikeda kunya yaga yanayinsa da Ammin Amirah Baffa yashigo Mami tace ina kwana dasauri yace ina kwana yamai jikin yakalli Marwan da kansa ke kasa anatse Marwan yace ina kwana kallonsa Baffa yayi anatse yace ya karfin jikin Marwan? Allah ya sa kaffara ne ahankali kowa yace Ameen Abba yanuna masa kujera yace bismillah zauna zauna amm saidai ban gane fuskan ba anatse Baffa yace amm kuma ku zauna dan Allah yar magana yakawoni bamusan gidanku ba da nan mukazo amman anmin kwatancen nan saisa nazo nan din zama Mami tayi Marwan ma yazauna kansa akasa Baffa yace ammm sunana Muhammad nine Yayan Mahaifiyar Amirah uwa daya uba daya Abba yace Masha Allah ahh sannu da zuwa dan shiruuu Baffa yayi sai yace tsakanin mu babu boye boye, kanwata bata gidan Yusuf wanda yabaku auren Amirah, sannan Amirah ba diyarsa bace diyar kaninsa ce uwa daya uba daya wanda yarasu tun Amirah na karama sai aka hada mahaifiyarta da yayan baban Amirah Yusuf kenan aure Allah yabasu Maryam Baffa yayi shiru shi kansa Marwan baitaba sanin mutumin ba shine mahaifin Amirah ba sai yau no wonder yanzu komi ke making sense, Baffa yace dudda rabuwansu bai dade ba amman dai sun rabu, zancen danake maka bamuda sanin zancen auren nan sai jiya da safe daya kirani awaya kan yanaso nazo masallaci kaza danazo yace nadan jirasa bari agama dayrin auren nan yaganni nadaiji ana daura aure da Amirah, Baffa yayi shiru hakama duka yan dakin yace mahaifiyarta batasan komi akan zancen ba, Abba yasauke ijiyan zuciya, ahankali Baffa yace dalilin dayakawo ni anan yau sabida nagana daku ne iyayen Marwan, sabida Yusuf ya sanar dane cewa ada yayan Marwan ne zai auri Amirah amman yafasa Dr ya aureta, daga mahaifiyarta hatta ni munada yar damuwa, na farko dai Amirah yarinya ce da bazan boye muku ba condition dinta ba yau ko jiyane yafara ba a a tun tana yar kankanuwa abin yafara, so ba lallai tama iya wani zamantakewan aure ba, and condition nata is not a good thing da on top of everything zatai rayuwa da wanda ba lallai yana kaunantaba! Hakanan Marwan yaji kirjinsa yafara bugawa yana Jin wani tsoro har baiso Baffa yasake wani magana dan gani yake kaman za ace yasaketa kirjinsa bugawa yake kawai wlh wlh Sauda Mami ya lura, Baffa ahankali yace munsan komi nufi ne Allah sannan bawai nazo danna kashe auren bane a a abinda Allah yahada shine zai raba ba niba! Wani boyayen ajiyan zuciya Marwan yasaki, Baffa yace kawai inaso nasan cewa eh Marwan yasan wacece diyarmu sannan zai riketa amana, idan bazai iyaba amm Dasauri Abba yataresa yace Hakan bazai taba faruwa ba! Baffa yakallesa, ahankali Abba yace ko bana duniya Marwan mutum ne dazan shedesa cewa bazai taba cutar da Amirah ba wallahi wallahi, zai riketa amana, and zai sama mata lafiya da izinin Allah wani sanyi Baffa yaji azuciyansa ganin yanda iyayen mutanen arziki ne, anatse Mami tace zaka iya binkici kan wanene Marwan tundaga kan asibitin nan zuwa gida dako ina, Marwan mutum ne mai amana, tausayi, dakuma zuciya mai kyau murmushi Baffa yayi sai cikeda hikima irin na manya yace Marwan! Saida gaban Marwan yafadi yanda Baffa yakirasa, dago kansa yayi ahankali suka hada idanu da Baffa dake kallonsa anatse yace zaka rike Amirah amana Marwan? Lumshe idanu Marwan yayi saiya budesu ahankali, cikin murya mai dadi dakenan anytse ba garaje ciki yace zan rike Ameenah amana Baffa namaka alkawari! Wlh wani sanyi Baffa yaji sai yaji ya yarda da yaron sai yayi murmushi yace Masha Allah ina addu a Allah ya albarkaci auren ku Ameen Ameen Mami tadan kalli Marwan sai ta kalli Baffa tace yaushe zamu iya zuwa daukan Amaryan mu dan dariyan manya Baffa yayi yace eh toh ga mai gidan nan Hajiya ai sai abinda yace Marwan yasake sauke kansa dake kasa sosai cikeda kunya Baffa na kallonsa, Baffa yace da so samune dai, Maryama zata tare gidan Mijin nata nan da sati biyu da yan kwanaki, to zanso ahada bikin ayisu idan Mijin nata ya yarda Dasauri Mami tace ai yama yarda muma kafin nan mun gama shiryawa gabaki daya Abba yace kwarai kam, Allah yakaimu lokacin duk akace Ameen Ameen sai Baffa yatashi yace to bari na koma Abba jiyayi yanason Baffa sosai yace muje na taka maka tare suka fito suna zance na manya, harya rako Baffa wajen machine dinsa, Abba jiyayi yanason Baffa sosai saiya taba aljihunsa yaciro kudi duka dayake jikinsa wanda bundle na yan 100dollars ne yace ga wannan ayi tsaraba dasauri Baffa yace ahhh bazamuyi hakaba Allah na amfana, nagode kwarai Allah yakara sauki damai jiki ya buga machine nasa yayi gaba Abba yabisa da kallo sai yayi murmushi Tunda yace Ammi bata tare da mutumin abu dayane yazo ransa Alhaji Bashiru babban abokinsa matarsa tarasu 10months kenan yanzu baiyi aure ba, yaga Ammi she s so gently and homely zaiso itada alhaji Bashiru suyi aure, yaransa uku duka maza duk sunyi aure, shi kadaine agida sai Chefs dinsa maza dake masa girki bari zaimai maganan yaga. EPISODE 4 Komawa gida Baffa yayi wannan karan a falon Lami yasamesu gabaki daya, Amirah tayi lamo jikin Ammi tana danna wayan Ammi, yanda take bala in son waya tanason game idan tagama game saita shiga danne danne babu inda bata sani awaya ba tafara danna wayan Ammi kona Miemie sai takusan karan da chajin ko ka amshi shine zaka tsira, doguwan rigane ajikinta na atampa red wani kalan sheki takeyi bana wasa ba, tana glowing ga kamshin datakeyi da turarata da akeyi, karbe wayan hannunta Ammi tayi tace baki iya gaisuwa ba ahankali ta tashi daga jikin Ammi takalli Baffa dake murmushi yana kallonsu murya yar karama tace
Chapter 49 · 0% Book details