Sashe 77
Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kafin yayi magana ahankali Marwan yace Abba kana ina? Dan jimmm Abba yayi jin yanayin muryan Marwan, kai tsaye yace meya faru? I m close ahankali Marwan yace Abba dan Allah kazo gidana yanzu Abba yace menene Marwan ijiyan zuciya ya fuzar zaiyi magana yakasa ya katse wayan kawai ya jefar da wayan ya runtse idanu yana dunkule hannu yana karanto ayyoyin Allah, Allah kabani ikon controlling zuciyata, Allah kabani ikon controlling zuciyata, saiya tashi yawuce yashiga closet yaciro jean yasaka yasaka t-shirt fara kirjinsa kawai dukan uku iku kawai yake yakasa believing baiga Amirah dasuke kwance tare ba, saiya sake fitowa yadauki wayansa number Mami yayi dialing just to be sure kaman Mami bazata dauki wayan ba tadaga tai shiru, cikin muryansa data karkace sosai yace Mami dan Allah Amirah na wurinki ? Muryansa kadai Mami taji tace meya faru? She s not here gabansa bugawa yayi rasss, da kyar ya tattaro kuzari yace t worr Marwan I said what happened? Kaman bazaiyi magana ba ahankali yace banga Amirah bane Mami cikeda tashin hankali Mami tace mene? Bangane bakaga Amirah ba ? Dasauri yace ina zuwa Mami kaman ga Abba nan yazo Mami tace Abba? Kawai tamike tadauki hijabi tazura tafito, saukowa kasa Marwan yayi Abba dake tareda driver nasa dake takasa yabude bayan motan yashigo gidan yana kallon Marwan yace meke faruwa Marwan bai basa amsaba yacigaba da tafiya yashiga falo Abba ya bisa yace meke faruwa? Why did you call me here you look so scattered? Kallon Abba Marwan yayi yabude baki zaiyi magana saiga hawaye hannuwansa biyu yadaura akan idanunsa yarike sAbida yahana hawayen zuba wlh bashi yake kuka ba kawai hawayen zubowa suke daidai Mami na shigowa falon sanye da hijab ta tsaya turus itama tana kallon Marwan yanda Abba ke kallonsa, dasauri ta matsa takai hannu ta kama kafadan Marwan cikeda so tace kai Marwan, menene? Zare hannuwansa yayi dagakan idanun ya goge fuskansa tasss yamaida glasses dinsa yasaka yakalli Mami da Abba yace jiya bayan sallan isha i dana ke dawowa gida i saw Saleem anan kofar g yay shiru bai fadi maganan giyan ba dudda shi Abba dazai shigo gidan yaga kwalban gida daya fashe awajen kuma wlh saida zuciyabsa takawo masa Saleem, ahankali yace we had little disagreement dai nashigo na kulle gidan nashiga falo shima na rufe na kashe komi as usual nawuce sama yayi shiru Abba yace saime yafaru? Ahankali Marwan yace bansan ya akayi ba he got the key na gidan nan yashigo har sama thankfully nasa key a kofarmu na bedroom saisa key dake wajensa couldn t work Abba yace Innalillahi wa innailaihi raji Mami tace I saw him jiya da daddare nafito daga kitchen yana saukowa daga bene I was trying to talk to hi ahankali Marwan yace Mami shiru Mami tayi suka kallesa, ahankali yace this morning mun tashi dagani har Amirah munyi salla mun koma bacci, yanzu na farka ban ganta ba! Atare daga Mami da Abba sukace mene? EPISODE 8 Saiga hawaye yasauke kansa kasa yace babu inda ban dubawa agidan nan ba banganta ba Amirah is not in this house Abba yace Innalillahi wa innailaihi raji Yashiga ciro wayansa Marwan ya goge hawaye yace idan Saleem zaka kira he s still here yana sama Abba yace what! Yana sama? Anan ya kwana? Gyadamai kai Marwan yayi yana lumshe idanu, Abba yawuce yayi sama azuciye Mami tabisa Marwan ya tsaya yabisu da kallo kafin shima yabisu saman. Turus Abba ya tsaya dayakai karshen stairs shi dayaji ance yana sama yadauka yasami wani daki yama shige ya kwana ne but no Saleem na kwance akasa gaban master bedroom gaban dakin ma aurata, kirjin Abba dukan uku iku kawai yake ganin kanninsa na jini ciki daya, uwa daya uba daya yake abun nan, Mami itama just found kanta in a situation da sai tama kasa magana ta tsaya itama, Abba yakai minti daya tsaye awajen saiya yunkura cikeda karfin hali yakarasa gaban dakin hannu yasa yawani fizgo Saleem din zaune shuuu yabiyosa Abba ya kauda kansa sabida wani warin giya dayaji yanayi, saiya dawo da kansa ya kallesa still bacci yake ya bubbuga fuskansa Saleem, Saleem, Saleem amman ina shiru sakinsa Abba yayi yakoma sharap ya kwanta Abba yatashi yashiga kalle kalle nan falon saman ya hango bottle water akan table yatashi dasauri yawuce yaje yadauki daidai Marwan na zuwa saman, Abba yana zuwa yabude ruwan yashiga tsayayawa akan fuskan Saleem da afirgice yatashi dan ruwan sanyi sabida AC ya yunkuro yatashi ya zauna daman tsabagen maye ne yasa since yakasa motsi kaman mai paralyzed idanunsa sunyi jajir ya shiga fuzar da baki yana yatsine fuska yana kakkabe duwan daya kama wanke fuskansa da wuyansa some har kunnensa yana kakkabe kunnensa Abba ya duka gabansa strictly yace Saleem dago jajayen idanunsa Saleem yayi yakalli Abba yahade fuska sosai, strictly Abba yace ina Amirah? Saleem banson tashin hankali? Kokai mayene yakamata ka hakura tunda an daura mata aure dawani bayan ka gudu, Marwan yatashi this morning baiga Amirah ba, she s nowhere to be found, nasan somehow you have something to do with it, kafadamin inda Amirah take ko wlh zan mikama hukuma kai amaka hukuncin daya dace dakai, for the last time Muhammad Saleem ina Amirah? Tunda Abba ke maganan Saleem ke kallonsa Allah yasani baisan ina Amirah take ba amman da Abba yafara maganan yaga damuwa kan idanun Abba wannan da neman Amirah yasa har an kura Abba yasan plan din Daddy yafara aiki ashedai tsohon nan shegen duniya ne, wow ya kwana da bakin ciki but is as if Abba yabasa golden news that just make his morning, kawai saiyaji wani farin ciki ya lullubesa, Abba kawai yaga Saleem na murmushi sosai. Kai Ya Allah! Wannan wani kalan tashin hankali ne wannan? Saleem wani kalan mutum ne wanda baisan mutunci ba da alkhairi? Wani kalan butulu ne Saleem? Wani kalan mara imanine Saleem, Mara Imani kuma da kaddara? Yanda zuciya yakawo ma Abba wuya baisan sanda yakai duka hannayensa gaban wuyan rigan Saleem ba yace ina ka kaima Marwan mata Saleem? Eh? Tell me now Kona maka dan banzan duka ? Kawai Saleem yabushe dawani kalan matsiyacin dariya dayasa azuciye Marwan yataho zai wuce Mami ta taresa tareda girgizamai kai, she knows abinda Marwan keji but ko mutuwa na kunyan mahaifiya, Abba shine yayan Saleem shima yana iyakan kokarin sa akan yaron, cin fuska ne Marwan yahau dukan Saleem agabansa kowani abu, mutunci da karamancin Abba shine Marwan yayi hakuri ya danne zuciyansa yabar yayan da kanninsa suyi magana batare da sun shiga ba, dukan Saleem Abba yashigayi Saleem yana wani kalan dariya na dadi da gidan ke amsawa sosai Abba saima yagaji yadena yana haki gwanin ban tausayi, Saleem dake dariya sosai yace wait harka gaji Yays? Dan Allah cigaba da dukana kaninka ai yazama punching back na kowa, har kasheni aka kusan yi bakace komi ba, kaima yinaka yanzu yamikama Abba kansa, Abba ya tsaresa da idanu, Saleem dake dariya yace kome zakamin yau I promise you bazan taba fushi ba cus I m the happiest man alive today yayi murmushi saiya dena yakalli Abba ido cikin ido yace nine kanninka! Nidakai mun fito daga cikin mace daya, the same blood ajikina shine the same blood ajikinka amman in order ka faranta ma wanda baka hada komi dashi ba ka gwammace nayi rayuwa haka miserably, pathetically ,kana kirana da bunsuru, kana Allah wadai dani, meanwhile kana kyautatama kanin matarka, kana nan nan dashi, kana kiransa danka sabida yayarsa nashan maganin mata tana baka gindi kanaci Saleeeem! EPISODE 8 Abba ya dauramai mummunan mari jikake tassss! Abba na huci yace t you dare disrespect my wife! Saleem yashafa inda Abba ya mare yadan cije lips nasa yanama Abba wani kallon rashin kunya, saiya fashe da dariyan keta sosai, yace you know I finally get wani point na wata karin magana da jama a keyi, wato daka haifi gwanma gwara ka haifi Matar gwamna, look at me kanninka, look at him kannin matarka yanuna Marwan dake kallonsu Mami ta taresa tahanasa komi, Saleem yace you gave him better education than me, yanada masters, harda PHD, a Dr, kasamamai aiki da NGO ana biyansa in dollars, komi ka kawo Marwan, abubuwan ka shi kakesa yana duba maka yana managing maka, nasha ji kana praising nasa wajen abokanan ka kan idan baka raye shikakeso ya jagoranci gidanka da iyalinka, Marwan is your everything while ni kaninka I m just a photo daka tsana, I have just LLB na law shikenan, no masters, no NGO job, nothing, absolutely nothing Abba yadade yana kallonsa cus duka abinda Saleem yake fadi are lies, pure lies, ahankali Abba yace Saleem bantaba banbantaka da Marwan ba, same school kukayi, kun gama same university, he proceeded with his masters kaifa? Kakiyi, kwanakin baya karyama kamin kaje dubai masters nan kana club, your entire life you choose clubbing da bin mata while Marwan is here working his ass off to be a better person to earn his own source of living not depending on my money, he established kansa da kansa, I only recommended him to the NGO tunda psychiatrist Dr suke nema, sunba Marwan aikin base on his merits, sun gansa sunka what he s capable of, sunga resume nasa, i didn t get him this job, he earned it, banda haka bazan iya tuna the last time Marwan yaci 5k tawa ba, he does everything for kansa, kona basa baya karba, kaiko you live and breathe on my money with my credit card nike maka komi, Marwan baida credit card from me ko guda daya, all this things baka gani ba Saleem? Saleem nawani murmushi yace saikuma kayi, karya kake Yaya, you always show me and show the whole world Marwan kakeso, ko baki kayi daga kasashe shi kakeson nunawa not me, abin yakaiga yarinyar danake so nake kauna kadauka ka aura masa just sabida kasa matarka dashi farin ciki ni ina cikin bakin ciki, baka taba tunanin for once how i will feel ba, and you think yau Amirah data bace I will not be happy? Ya kwashe da dariya yace bari nagaya maka wani abu Yays, inhar banda peace of mind kaima bazaka taba samin peace of mind