← Book details Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 87

Sashe 81

Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

the envelope and ina kiran police Alhaji Hamza dasauri yace bari nakira Abba yace kwarai gwara kai kakirasu general yanzun nan zaka gansu sunzo Alhaji Hamza yashiga kiransu duk suna fita suka shishiga mota, Mami kadai aka bari agidan takasa motsi. Allah yasani tagaji da rigiman Saleem tasan he has something to do with this entire thing amman yanda Marwan yasaki Amirah yamata ciwo kaman taitai kuka, bakin ciki takeji aranta sosai da bacin rai wanda tadade bataji kalansa ba kaman yar cikinta aka saka haka takeji. Shifa Saleem baisan meke faruwa ba so koda yafita motansa yashiga yaja yana gudu a titi amman shima sai tunani yake ina Amirah taje? Zuciyansa na basa Daddy has something to do with it, sai kawai yadaga wayansa yashiga kiran Daddy wanda ringing daya biyu yadaga kai tsaye Saleem yace Yohh Pops kana tareda Babe dina ne ba a ganta ba fa Dan dariya Daddu yayi yana kada kafa yace banace kabani nan dariya 3days ba, but I think I will finish this job today cus right now she s on her way going to gidanta tasa yasaketa Saleem yazaro idanu yana mamaki yace me kayi hakane eh ? Dariya Daddy yayi yace zamuyi magana anjima go and have fun zan kiraka anjima na nuna maka takardan sakinta wani ihun Daddy Saleem yayi yace love you Pops Inlaw Daddy ya fashe da dariya, Saleem ya katse wayan yawani kunna wakan mota yana zuba gudu a titi yana rawa. EPISODE 9 Amirah na fitowa da gudu motan tabude ta shiga bamata tsaya rufe kofan ba kawai ya kwanta ta kifa fuskanta a kujeran bayan datake tafashe da kuka Ya Rabbi! Kuka take with all her heart and soul mai karfi, jikinta na rawa tana shesheka, mazan suka kalleta sai driver yabude motan kawai ya sauko ya kulle kofan bangaren ta yadawo yashiga motan ya kunna yasha motan. Amirah kuka take kaman ranta zai fita bata taba sanin this is the feeling da mace keji idan aka saketa ba, for the first time in her life saitaji inama ta mutu kawai bayan ta ceci Ammi she wants to die, sabida nothing will make sense again, tayaya zata cigaba da rayuwa babu Ya Marwan ciki eh? Saleem she just mentioned that one name sabida yasaketa amman Saleem tama tsani kallon fuskansa haka nan kawai baitama ba at all, kawai Marwan sai dawo mata yake azuciya tana tuna the first day data fara ganinsa a asibiti daya bata chocholate, after Amminta Marwan was the second kind person data taba sani a rayuwanta He takes care of her he protects her he pampers her yanzu shikenan sun rabu? Bazata kara ganinsa ba? Har sukakai gidan kuka take parking akayi, driver yabude mata kofa yace fito tasowa tayi daga kwancen datake saita mike tafito daga motan idanunta sunyi suntum tafito ta tsaya saita daga hannunta ta kalli takardan daya bata that was folded tana hadiye wani abu hawaye na gangarowa daga idanunta, namijin yace s go tafiya tafarayi jikinta ba karfi suka wuce sama azaune taga Ammi bakinta arufe amman idanunta na nuna tashin hankali tana kallon Amirah data kalleta tana g e hawaywn fusknata. Kirjin Ammi yashiga bugawa dum dum dum tadaura idanunta akan envelope dataga Amirah tarike a hannu sai kawai ta runtse idanu da karfi tareda juyar dakanta, Daddy baya dakin hakan yasa Amirah ta taho wajen Ammi dasauri tazauna gefenta tace Ammi nadawo everything will be fine kinji I will save you tai maganan tana tsare Ammi da kallo dataga taki juyowa ta kalleta kawai zuciyanta ya idasa karyewa gabaki daya gane cewa wani kalan mummunan fushi Ammi takeyi da ita bana wasaba kawai saita fashe da kuka sosai har wani kalan shesheka take kaman zata shide wlh hakan baisa Ammi tajuyo ta kalleta ba ayanda take fushi ayanda ranta ke baci, tasan waye Marwan mutum ne mai hakuri da hankali duk abinda zai kaisa daya saki yarnan bakaramin abu Amirah tayi ba maybe taje tamusu rashin hankali. Daddy all this while yana bayi fitowa yayi daga bayin yanda yaga Ammi tajuya ma yarinyar dake kuka sosai baya yasan fushi Ammi take da yarinyar yawani kwashe da dariya yasami kujeransa yazauna yakalli Amirah yace ke zo bani takardan nagani tasowa tayi ahankali tazo wajen saita duka tabasa Daddy yasa hannu ya amsa yana murmushi yadaga wayansa yashiga kiran Saleem yana warware letter yace Hello Saleem yafadi, Daddy yace Na sakeki saki daya! Harda signature da date da sunansa yarubuta Saleem yadanyi shiru yace maisa ba uku ba Daddy yace as long as mun sami dayan ma Alhamdulillah Saleem yace to kuna ina nazo kadaura mana aure ? Dasauri Daddy yace Haba Saleem wani daurin aure, ai saitayi idda ya kake abu kaman bakaje islamiyya ba kusan wata biyu da auren su fa kenan cikin fushi Saleem yace nidai kadauramin aure da ita yau I don t care Daddy shima yace to ai shikenan kaika sani hado balance dina ka kawomin da share dina sai na daura muk everyone raise your hand above your head! Daddy yaji muryan yan sanda, tsabagen rudewa saida yasaki wayan kasa, kwata kwata abinda bai luraba Amirah nabasa envelope din zata yayi tabasa takardan taciro takardan taga dan wani bakin abu dabatasan menene a envelope din ba ta share yan sanda tagani sun shigo falon kusan u goma chan saiga Marwan yashigo yana tafiya kaman zaki wani tsaresa da kallo tayi tana ganin wani haske na binsa tana kallon fuskansa dasauri taga yayi wajen Mami baiyi wata wata ba taga yadaura hannuwansa biyu akan kafadan Ammi cikeda kulawa yace Ammi are you okay? Yashiga kwance igiyan daurin hannuwanta dana kafafunta, saiyakai hannunsa bakinta yashiga cire salatef din ahankali sabida zafi Ammi ta runtse idanu, saiyakai hannunsa yakama hannayen Ammi dayaga shatin bulala banda sign na daurin igiya, daga wajajen guiwan hannunta akwai shatin bulala wani rawa jikinsa yafara saiya kalli shedan bulalan injin dake hannunsa strictly yace who beat you like this Ammi? Murmushi kadan Ammi tayi tace Dan bugewa nayi idanun Marwan na komawa ja yace is that man right? Kafin Ammi tai magana kawai yasa hannu yadauki bulalan yatashi azuciye yawuce inda yan sanda ke kama Daddy dake zuba turenci karaf Marwan yaji an rikesa, saiya juyo Alhaji Hamza ne girgizamai kai yayi yace ba huruminka bane dukansa kana auran diyarsa let me do it with him man to man, inspector ku sakesa yafada with so much command and authority, atare sukace Yes Sir kawai sai suka saki Daddy suka matsa gefe, Daddy ya kallesu da sauri yana mamakin waye mutumin, Alhaji Hamza yashiga nannade hannun rigansa, he was once a soldier retired yayi yafara business bazaka taba cewa yanada shekaru ba, wani kallo Daddy yamai yace and who are you? Yana linke hannun rigansa yace m the man that s is willing to go to any limit to protect that young woman you just tortured, yau zan gwada maka you don t mess with abinda tsohon soja keso! Dago idanunta Ammi tayi takalli Alhaji Hamza dan bata sansa ba bakuma tasan waye ba, Abba yadanyi murmushi yana sunnar dakai kasa ganin Abokinsa na playing hero lines. EPISODE 9 Ammi bata taba ganin Alhaji Hamza ba, amman shi yasha ganinta har unguwansu Abba yakaisa yanuna masa gidan da Ammi take kullum saiyaje ya tsaya a waje just ya ganta, yagayama Abba saita gama idda zai fito ya nemeta amman Allah yadaura masa son Ammi sabida yanda yaga she s so religious shi addini yakeso ajikin mace, Daddy jin abinda yafadi wani kishi yarufe sa yace kar har ka isa? Wayekai har yanzu Matata ce ai ance saki uku a Lokaci daya saki daya ne, kumadai bata gama ba saura 3daya, abamu fili mu fafata Alhaji Hamza yayi wani murmushi yace ai an bamu bakaga sun matsa ba taho yanuna yan sanda Daddy yashiga linke hannun riga Alhaji Hamza yace yau zan maka dukan da bazaka kara kwadayin dukan wata mace ba a tsawon yan shekarun rayuwan dasuka rage cikin kunfan baki Daddy yataho zai naushesa haba kama hannun Alhaji Hamza yayi da hannu daya kawai yajuya Dady Daddy yajuyu kaman muciya yasa kafansa ya kwashesa saiga Daddy akasa on his knees hannunsa twisted sosai yayi wani kara. Wayyyoooo hannuna zaka karyamin hannu har yanzu dorinar I Jin na hannunsa Alhaji Hamza yadage ya zubama Daddy dorinar wani burgima Daddy yayi. Wayyooooo Allah na officer zai kasheni yashiga soda jikinsa kaman zararre yahaukace ashe haka zafin bulalan inji ke zarar da mutum, kunga yanda Alhaji Hamza ke dukan Daddy da wayan Daddy na ihu kowa na dakin kallonsu suke especially Amirah da Ammi, Ammi tunda take bata tabajin abu yamata dadi azucuya kaman yanda taji dadin yanda taga Daddy na ihu in agony ba Hamza na dukansa har Abba babu wanda yace yadena, soja baida imani saida Alhaji Hamza ya farfasamai jiki da bulalan dan kana ganin jini jini a rigansa sannan ya jefar da bulalan yasa hannu ya fizgo Daddy dake nishi kaman zai mutu yajasa keeeee yakaisa gaban Ammi yadagasa yakamo habansa yanunama Ammi shi hancin Daddy har jini yake fita lips dinsa sun kumbura yadaku, Hamza yace bata hakuri Daddy nada rudewa sosai ya tsorata ganin mutumin babba ne kuma kaman Ogan yan anadan ne dan babu wanda yahanasa arude yana magana yace kiyakuri dan Allah kiyakur tasssss! Ammi tadaukesa da mari da saida yaga tauraro Alhaji Hamza yace good yasakesa yana clapping for Ammi yana kallonta, Ammi takara kai hannu tadaurama Daddy mari jikake tassss! Saida bakin Daddy yashiga dalalar da yawu, hawaye zai fito daga idanun Ammi cikeda wani kalan tsantsan kauna Alhaji Hamza yace t cry for him dagayau bazai kara ganin hawaye ki ba, baikai ba sannan bai isaba, he s a nobody kallon Alhaji Hamza Ammi tayi idanunta fal da hawaye amman basu zuboba, gyadamata kai yayi yace s okay, he will never hurt you again or your children, i will make sure he spends the rest of his life in prison, you re a strong woman karki karamai kuka instead trash him nabaki bulalan ? For the first time dan murmushi kadan Ammi tayi ta girgixa kai alamun a a wani sanyi Alhaji Hamza yaji aransa, saiya daga Daddy ya wurgama
Chapter 81 · 0% Book details