← Book details Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 87

Sashe 51

Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

manyan kawayen Mami guda biyu sukazo sai kannenta su Yaya Ammah aka tafi kai akwatina Abba yayi magana da Baffa so ansan da zuwansu an basu address. Ammi tasa Miemie ta tafi da Amirah gidan makotansu dasuke shiri da Lami sosai, Ammi tasa wata lace mai kyau tayafa mayafi mai kyau, wlh Ammi is a very very beautiful woman saitaci gayu ka kalleta saika kara kallonta, Sunyi girki, an soya kaji dan Baffa na kiwo, akai fankasau da waina, da alale na gwangwani dasu cincin da danbun nama makota duk sun shigo, wuraren 2 suka iso akai parking, su Ya Ammah suka shigo da farin cikinsu ana ayiririiii suna ina Maman Yarmu Lami na washe baki tanuna Ammi dake murmushi cikeda natsuwa wani irin rungume Ammi sukayi har Ammi saida tafarajin kunya, nan da nan aka shigo da akwatunan, anan tsakar g da aka bubbude ana ayiriri, kafin afara kawo abinci, yanda sukaci abinci ko saida Ammi tai mamaki alalen tasss na kare waina da sinasir har take away sukayi suna tambayan waya dafa Lami tace Maman diyarku ta dafa sun dade sai wajajen four suka tafi suka basu tukuicin 200k suka karba suna godiya sosai duk saida sukai take away na abubuwan da aka musu suka tafi suja murna yau sai Ammi takarajin ta natsu ganin sunada kirki Amirah ta bazata wahala ba. Marwan na sama yaji sun dawo anata hira ana bada labarin abinci babu wanda yayi maganan Amirah har wani gyara kunne yake da laptop jikinsa amman babu wanda yayi maganan Amirah, Farida ne tace Yaya bakuga matan Ya Marwan dinba? Wani ijiyan zuciya Marwan yasauke dasauri jin finally an tambayi Amirah, dariya Ya Fadila tayi tace ai ba a ganin Amarya sai rannan biki wani irin Marwan yaji sai kawai yatashi yawuce yashiga dakinsa karaf a idanun Mami tai wani murmushi batace komiba. Around 10 na dare Mami tai knocking gaban kofansa ahankali yace come in bude kofa tayi ta shiga tana kallonsa yana zaune gaban system yana aiki, Mami ta maida kofan tarufe tace an baka 2months wajen aiki fa Marwan why are you still working ? Batare daya kalli Mami ba yace just small abu nakeyi? Mami tace okay tana wycewa closet nasa tace wai bazaka hada kayanka ka kai gidan ku ba, kamaje ka duba gidan da abubuwan da akayi aciki? Shiru yayi baice komiba Mami tafito saitazo wajen ta tsaya akansa tace Allah idan baka tattara kayan nan ba nizam tattara nabada akai maka gidanka, you have just 5more days agidana kavar gidana kenan kallon Mami yayi ahankali, Mami ta ballamai harara tace nai magana da telenka jibi zai kawo dinkunan ka Abban ku duk yabasa sauke kansa kasa yayi, Mami tai murmushi kawai tace yaushe zakaje kaga matarka kabata kudin kitso da lalle da sauran shirye shiryen Amarya eh? Kasa dago kansa yayi, murya chan kasa yace Mami stopppp! Baki Mami takama tace ni kakejin kunya yau ahh lallai ango da kunya, gobe ka shirya kaje ka kaimata kudin shiryawa ko na cicci maka mutunci I will text you address na gidan Mami tai maganan tana hanyan kofa tace kuma go get hair cut kay gyara gyaran ango this time rufe fuskansa yayi duka Mami ta kwashe da dariya tabude kofa tafita daga dakinsa. He was smiling saikuma ya dakata yana mamakin ina Saleem yayi? He calls him everyday he s fine yana magana dashi yama gayamasa he s married yayi yayi yagaya masa ina yake yaki gayamasa. Kasa zuwa gidan Marwan yayi kuma bakomi ke hanasa ba sai kunya dawani kalan jin nauyin Ammi baisan tayaya zai kalli Ammi ba, he feels like yamata laifi tundaga kan bada address da contact na gidansu da number Daddy, is as if he took advantage na privileged information din dayake dashi na patients so he feels he wronged Ammi sosai. Yana fitowa daga masallaci daga Magrib yana sanye da jumper na milk yadi mai kyau yana kamshi ga glasses idanunsa yaga Abba tsaye gaban gudansu ga mota agaban gidan, zai gaida Abba Abba yamika masa car key yace maza tafi kaga Matarka! Mami tacemin kaki zuwa, akwai kudi a motan jeka bata kudin lalle gobe bikinku inba hakaba zanyi fushi daki karbi makullin motan ahankali yasa hannu ya amsa kansa akasa, yashiga motan ahankali yaciro wayansa zuwa address da Mami tabasa zuwa anguwansu Amirah gabansa sai faduwa yake, yaja yana tuki ahankali, sai Chan yakara gudu wlh he can t wait to see her kusan almost 4weeks bai ganta ba yanabin map harya shigo layin sai yayi parking a kofar gidan gabansa na bugawa kadan kadan yarasa mezaiyi, he s feeling nervous and anxious kaman zaiga wata sarauniyan duniya, baisan ma yaya zaiyi ba, wayansa yadauka ahankali yarasa wanda zai kira saiya kira Ya Fadila wacce yakebi kira daya ta daga tace ya akayi Ango Ango hade fuska yayi yace okay bye dasauri tace yakuri Ang au yakuri Doc dan shiru yayi sai chan yace m in front of their house yazanyi? Dasauri tace wani house? Ban gane maganan ba dan jimm Marwan yayi sai murya chan kasa yace my wife .house yarage murya sosai haba mezaiji sai shewa na muryan duka yayyinsa katse wayan yayi yanaji kaman ya nutse kasa, Mustapha yagani yafito daga gidan somehow duk suna yanayi they re all light skin horn yamasa tareda bude motan yafito dasauri Mustapa yazo wajen yana hada idanu da Marwan yamai wani kwarjini dasauri yace ina yini anatse Marwan yace lafiya lau, please kashiga kace Marwan yazo wajen Ammi zaro idanu Mustapa yayi yace laaa kaine daman Ya Marwan Mijin Amirah! Dr Mustapa yakara basa hannu yana kallonsa kamna zai cinyesa damn! Sai yawani murmushi Marwan ma haka Mustapa yajuya da gudu yayi cikin gida duk suna tsakar gida, Ya Rabbi anma Amirah lalle mai bala in kyau, yanda Mustapa yashigo da gudu yana kwalama Ammi kira, Ammi, Ammi yasa kowa yajuyo harda Amirah dake cin abincin, Lami tace kai lafiya? Wani tsalle yayi yace Ammi Mijin Amirah na waje Yaya Marwan wai yazo wajen ki! Wani zabura Amirah tayi ta kwasa da gudu Ammi na kwala mata kira, ko kalli babu akan nan balle slipas, tace ke! Amirah! Amirah! Amman ina ta falle ta tsere da gudu tai zauren su!!! EPISODE 5 Gidan ba wani babban gida bane, daga nan kofar gidan da Marwan yake tsaye jikin mota yaji yanda Ammi ta kwalama Amirah kira, sai kuma yaji sahu da alamun gudu, gently yadaga kafansa yayi one step closer to kofar gidan, kirjinsa na bugawa yanajin wani kotsawa na ganinta kaman yayi shekara bai gantaba, just 3weeks zuwa 4weeks dinnan dabai gantaba but it feels like forever, daidai Amirah ta bullo daga zauren, wani kamshi da tunda yake arayuwansa baitabajin kalan kamshi dayamai dadi haka ba, kafin ita Amirah ma ta iso yay maza yataho dab gaban kofan cus yasan fitowa zatayi ahaka ba hula, ba takalmi, ya tsaya chak yazuba hannu a aljihun wandonsa yana kallonta, kirjin Amirah wani kara bugawa yake dum, dum, dum, ganinsa tsaye yazuba mata idanu cikin wani farin glasses din nasa, tanajin kamshin turarensa datai kewa kawai saitaji kaman ma bata gudu ayanda takeso tayi dan she feels like the little distance dayarage from inda take takai inda yake feels like forever, kara gudu tayi Marwan yawani lumshe idanu yabude su asanyaye yana sauke ijiyan zuciya bakinsa naso ya furta becareful karta fadi amman yakasa zuwa gabansa Amirah tayi saitaci birki tana kallonsa kirjinta na bugawa tana wani kalan numfashi irin na wayanda sukai game na racing dinnan, takai hannunta tasa abaki ahankali tana tsoro karya sake hanata rungumesa yanda yayi a hospital amman kawai sai jikinta yahau rawa, tana feeling wani mugun urge na hugging nasa, jikinta yayi wani karkarwa, kawai runtse idanunta tayi taciro hannunta daga baki batai wata wata ba kawai tai wani kalan hugging nasa tana daga feets nata sama sabida takai tsayin wuyansa dan Marwan nada tsayi bata wani kai ba amman saita kankamesa ta kwantar da kanta akirjinsa ahankali takai hannayenta duka biyun bayansa ta kulle ta kankamesa tana kara kankamesa kaman zata fasa jikinsa tashige ciki tana sauke ijiyan zuciya fast fast na gudu. Wani kalan bugawa kirjin Marwan keyi kaman zai fito, no one has ever hugged him like this irin real intentional hug dake nuna mutum yayi kewanka, ga kamshin datakeyi gabaki dayanta da wanda gashinta keyi shima yana fizgansa, gashi shifa yana tsaye ne gaban kofan zauren yana daga waje ita tana daga ciki ga jama a and anyone daga gida ayanda ake kiranta dinnan zai iya biyota aka gansu ahaka fa, da kyar ya tattaro duka karfinsa dawani kalan murya da yaune rana na farko da ita kanta Amirah kejin muryan yace cikani! Juya kanta Amirah tayi a kirjinsa alamun no, ta daga takai hannunta tadaura saman kan inda nipples dinsa cikin that baby voice yar karama tace ciwonka ya warke? Ya Rabbil Alameen wani abu Marwan yaji tundaga kafansa zuwa kansa baisan sanda ya gyara muryansa zuwa very strict ba yace fitan mini daga jiki! Ahankali Amirah tafito daga jikinsa dan idan yamata tsawa ko ya maida muryansa so strick tsoronsa da shakkan sa take saitakai hannayenta biyu tasa abaki tasauke kanta kasa tadan turo baki, tundaga kan kafafunta dasuka sha kunshi ja da baki zuwa hannunta dake baki dasuka sha lalle yabi da kallo, yakalli kitson da akamata yaji wani abu a wuyansa, da haka zata fito har waje agama ganeta, strictly yace ina hulanki? Hannunta tadaga takai saman kanta tai wani kwaba kwaba da baki kaman zatai kuka, ashagwaba tace zafi yakemin, Amirah tayi kuka da ana mata kitso lumshe idanu da sauri Marwan yayi saiya dauke kai cus Amirah na neman halakasa, murya ciki ciki yace go back inside kallonsa tayi shirin fashewmai da kuka take strictly yace kikamin kuka ranki zai baci anan turomai baki tayi tajuya ahankali tawuce yabi bayanta da kallo dake juyawa zuwa kitson da aka mata dasuka zubo sosai, sai alokacin Mustapa yafito anatse yace ance ka shigo gyadama Mustapa kai Marwan yayi saiya fara tafiya ya shigao gidan, ko ina looks extremely neat, har falo Mustapa yakaisa falon na kamshin turaren wuta Marwan yazauna. Amirah dake dakinsu Ammi na mata fada tana yafa mata mayafi
Chapter 51 · 0% Book details