Sashe 56
Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yana zuba uban kamshi mai tashin kai da dadi, idanunsa sanye da farin glasses dinnan dasuke karamai kyau, yafara tafiya zuwa flat din a nutse ya bude kofan falo yashiga da sallama kasa kasa fuskansa looking straight bazaka taba cewa he s happy ba at all, he looks like any other day, Abba ya tsaresa da idanu hakan yasa Marwan yasauke kansa kasa, saiya sami waje yazauna a nutse, ahankali yace ina yini Abba ijiyan zuciya Abba yasauke sai yadanyi gyaran murya yace Marwan due to condition na matarka yasa ban hadaku namuku wa azin tare ba, I know ganin mutane dayawa nadan bata tsoro Abba yayi shiru, chan ya sauke ijiyan zuciya yace yarda da sanin waye kai yasa na aura maka Ameenatu sabida nasan bazaka taba cutar da ita ba, Marwan karike yarinyar nan amana dan girman Allah, batada banbancin da this two children dake gabanka yanuna Farida da Faiza, ahankali Abba yace t hurt her, don t take advantage of condition nata, kariketa tsakani da Allah and trust the process, albarkacin auren nan zakaga ta warke and you will build a very beautiful home da izinin Allah, auren nan na tattare da Alkhairi I feel it, Allah ya maka albarka, yanda kakemin biyayya karufamin asiri ina addu a Allah yabaka yaran dazasu maka abinda yafi haka Marwan, Allah yamaka albarka ahankali kowa na dakin yace Ameen kan Marwan na kasa he just wanna see his wife shine kawai damuwansa, Abba yakalli Mami yace wat were you trying to say? Dan jimmm Mami tayi saita sauke ijiyan zuciya takalli Marwan da kansa ke kasa saita kalli Abba tace Alhaji I was thinking of something, after seeing the girl for just few minutes naga anya is it proper mubar yarinya haka ta tare gidan miji? Wani bugawa kirjin Marwan yayi dummmm! Amman yadaure yadake batare daya nunaba, cikeda kulawa Mami tace I was thinking maisa bazasu zauna anan gabanmu ba, Marwan zai koma aiki, banda haka akwai doguwan fita, yarinyar nan is not in anywhere fits ta zauna agida haka ba iyaye ko wasu dake kallonta, saisa naga zamanta cikinmu kaman is a good idea ko shiru Abba yayi, baiji idea ba, but one thing is yasan komin daren dadewa Saleem can come back to this house, ayanda yake kaman bunsuru yafara neman Matar dan uwansa fa? Dudda bawai lallai yayi hakan ba, amman dai shi yafison yarinyar na tare da mijinta su gina soyayya tukunna, idan basu zauna tare ba yaushe Marwan zai sota? Anatse Abba yace ayanzu wanda can make that decision is Marwan dan matarsa ce! No us Abba yadanyi shiru chan yace suje gidansu su zauna, sanda zai koma aiki yadinga kawota nan ya ijiyeta yatafi aiki, yadawo yazo yadauketa su koma gidansu, with kalan yanda aurensu yazo zamansu tare shine the best sabida Marwan yagane wacece ita soyayyan su ta ginu, ku kawomai matarsa su tashi su tafi dare nayi yakamata ta kwanta ta huta itama Mami taso Abba ya yarda, dan wlh haka kawai Allah yasamata son Amirah, tanaso tarike yarinyar sosai, amman dudda haka bakomi tamike ahankali tawuce sama. Tashi Marwan yayi ahankali yana wani kalan jin kunyan Abba yasan anything dazaisa Amirah tafito tagansa anan she will hug him ne in front of everyone so gwara yaje yajirasu a mota, ahankali yace bari naje mota Abba saida safe Abba yace toh Allah bamu Alkhairi Son yajuya suka hada idanu da Ya Fadila yadauke kai dasauri kafin sumai iskanci yawuce dasauri yabude kiga yafita daga falon. EPISODE 5 Ahankali Mami tabude kofan dakin, Amirah na zaune kan gadon wajen tanashan zobon da straw tana dan wasa da straw din tana ganin Mami ta ijiye zobon Mami tace harya isheki? Gyadama Mami kai tayi asanyaye tamike, ahankali tasauko da kafafuwanta daga gadon, yanayinta da Mami tagani yasa tace menene ? Mikewa tsaye tayi ahankali ta juyama Mami baya tana nuna mata daurin lafayan da aka mata tabaya, da yar muryan nan yar karama chan kasa kuma tace fitsariiiii matsowa dab da ita Mami tayi like a mother saitakai hannuwanta wajen tace to bara na kwance miki kwance mata daurin Mami tayi, Amirah tazare abin gabaki daya daga jikinta yarage wata doguwan riga na atampa mai bala in kyau ne ajikinta ta ijiye akan gadon, Mami tace muje ga bayi kiyi fitsari Mami tawuce dakanta tabude mata kofan bayin, dasauri Amirah ta taho tashige bayin, Mami tarufo mata kofan saita wuce ta linke lafayan, saita bude wardrobe nata taciro wani dogon hijab black, daidai Amirah nabude kofa tafito Mami tabi dogon gashinta da kallo kitson yamata kyau sosai, Mami tace zokisa hijabi muje kasa ahankali tashiga tahowa gaban wardrobe din da Mami ke jiranta, tana zuwa saita mikama Mami kanta yanda takema Ammi alamun asamata hijabin, murmushi kawai Mami tayi wlh she loves the girl sosai ba wasa ba, warware hijabin tayi tasamata ta gyara mata zaman hijabin a wuyanta, Mami tace yauwa toh an gama, maza sa takalmin ki wucewa tayi tasaka takalmin sai Mami tazo tabata hannu dasauri Amirah takama hannun Mami tasa dayan hannunta tadauki zobonta tacigaba da sha tanabin Mami, Mami takalleta sai suka cigaba da tafiya suka fito har stairs kowa na falo, kwata kwata Amirah bata lurama da mutanen ba sabida yanda take wasa da goran zobo da straw gabaki dayan dakin kallonta ake harda Abba, suna gab da saukowa kasa kaman taji ajikinta ana kallonta dago kanta tayi dawani irin sauri tasaki goran kasa kawai takoma bayan Mami gabaki daya taja mayafin Mami tana kare fuskanta dashi tana boyewa, ahaka suka shigo falon Mami saita tsaya ahankali tasa hannu tafito da Amirah daga bayanta tace taho Amirah, gaida Abban ku wani kalan kankame Mami tayi tagaba jikinta har rawa rawa yake ta kifa fuskanta a kirjin Mami da sauri, murya chan kasa yar karama tace ina kwana aka kwashe da dariya a dakin, shi kansa Abba saida ya murmusa yace lafiya lau daughter na, Allah miki albarka kinji dan bude idanunta kadan Amirah tayi takallesa, dan bata tabajin muryan babban namiji daya mata magana da kulawa hakaba banda Baffan ta, saitadan juyo ta kalli Abba kadan saita sake mannewa jikin Mami su Ya Ammah suna kallon da mamakin yanda yarinyar keda shagwaba, anatse Abba yace kaita sutafi she s scared Mami tace okay bari muje sai sukai wajen kofa bude kofan Mami tayi suka fito. Marwan na zaune cikin motan yagansu sun fito ya tsaresu da idanu yana mamakin yanda Amirah ta yarda da Ammi haka she s holding Mami the same way take rike Amminta, abin yabasa mamaki sosai, ahankali yasa hannu yabude motan yafito, Amirah dake nanike da Mami abayanta kamshin turaren Marwan taji saita dakata ta tsaya chak hakan yasa Mami itama ta tsaya tace yaya dai Amirah ? Dago kanta tayi ahankali kaman ance ta kallo gabanta Marwan tagani yana maida kofan mota yana rufewa yana kokarin juyowa towards direction nasu yana sanye da wata faran shadda daidai jikinsa masu kyau, wani hasken sanyi Amirah taji azuciyanta tasaki Mami dasauri, dawani irin gudu ta kwasa daidai Marwan na juyowa ga Mami ga yayyinsa su Ya Ammah duk yagansu ta window, su Farida ma su sun bude kofan falo sun fito Amirah ta taho dagudu, and he knows the next abu dazatayi is tafada jikinsa, tsareta yayi da idanu yahade fuska ba wasa ko zata gane, zuwa tayi gabansa batai wata wata ba tayo luuu zata fado jikinsa cikin dan kakkausan murya yace Tsaresa Amirah tai da idanu saitai raurau da idanu, dasauri Marwan yadauke kai yakalli Mami dake tahowa kaman Amirah bata santaba ganin Marwan saita koma gefensa dasauri tasa hannunta takama hannunsa tarike gam tai lamo a gefensa harda wani kwantar da kanta a muscles nasa Mami data karaso tace abin hakane kinga wanda kika sani an bata dani ne? Kara kankame Marwan Amirah tayi tawani sake kwantar da kanta a hannunsa sosai irin yanda kananun yara masu kiwuya keyi dinnan a jikin Maman su, Mami takallesa yadan sauke kai kasa dasauri, Ammi tace anytime you re going out Marwan bring her here, she s in no condition to stay on her own, it s for her safety and security, banda haka inaso tasaba da yan uwanka, she s part of us, idan she s here she will learn so much gyadama Mami kai yayi wani kunyan Mami yakeji yakasa kallonta wlh, Mami takalli Amirah tace nazuba miki abinci da snacks dazakici anjima ? Mami tai maganan da caring sosai, ahankali Amirah ta gyadamata kai, murya chan kasa yar siriruya tace zoboooo murmushi Mami tayi tace to zan samiki zobo dayawa, shiga mota Mami tai maganan tajuya, kaman jira Marwan yake cikeda so yadan kalleta yanda tai lamo a gefensa kanta duka a hannunsa yace kin iya kwadayi ko ? Tsaresa tayi da idanu kirjinta na dumdumdum, yamata wani irin kyau yau takasa magana, dauke idanunsa yayi daga kanta calmly yace s go dagowa tayi daga jikinsa ahankali tace Ammi? Baiso yace eh yazama kaman yamata karya kuma baiso yace a a ta daga hankalinta hakan yasa saiya wuce, Amirah tabisa dasauri yabude mata kofan motan gaba yakalleta yace get in ahankali ta shiga tana kallonsa, hannunsa yasa ya tattare hijabin tayi yana kallon kafafunta da lallen dasuka sha dayamai kyau sosai sannan yamaida kofan yarufe yazagayo yana jiran Farida da Faiza daya gani niki niki da kula da abubuwa da Mami tahada musu, sukazo bayan mota yabude musu suka ajiye suka juyo, Farida takama hannunsa ashagwabe tace Ya Marwan she doesn t like us, please make her talk to us, wlh we love her tunda Farida takama hannun Marwan tarike kawai kirjin Amirah yadinga bugawa, tarasa dalili sai kallon yanda Farida tarikeshi take mai magana da shagwaba take, itama Faiza tarikemai dayan hannun sunamai magana, suyake kallo ita dake mota baya kallonta, Amirah bata iyajin mesuke cewa dan tana mota amman Marwan yayi dan murmushi, wani iri Amirah taji, zuciyanta namata zafi da nauyi, kawai saita fashe da kuka takai hannunta biyu tadaura kan fuskanta tana kuka sosai harda shesheka, kaman jikinsa yafadamai dago idanunsa Marwan yayi yakallo cikin motan, ganin Amirah tadaura hannu a fuska yasa yakallesu yace good night bari naje, she will talk to you tommorow baijira amsansu