← Book details Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 87

Sashe 30

Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

about her condition Yaya, ita nakeso ka auramin! Saleem yafada adan zafafe dan he s damn serious he s not even ready ya saurari duk wani wanda zaice mai mahaukaciya ce, menene menene ko matatta ce ba mahaukaciyaba yanason abinsa, Abba yadade yana kallon Saleem yana nazarinsa, Saleem is a very stubborn yaro tun yana yaro, ayanda take maganan nan idan bai masa abinda yakeso ba tsaf zaiji agari Saleem yaje yayi aure. Ahankali ya juyo yakalli Marwan dake bude bude folder yana cicciro takardu wanda ko ganin takardan bayayi da kyau tsabagen yanda kansa yadauki zafi Abba yace Marwan ijiye takardun Marwan yayi yace am Abba Abba yace wacece yarinyar wani ciwo ke damunta? Abu Marwan yaji aransa yakai kusan 20secs baice komiba chan saiyace ahhmm bata magana ne haka Abba, rashin son mutane da sauransu Abba yayi dan jimmm yana tunani saikuma yakalli Saleem dake kallonsa looking very serious, sai Abba yamaida kansa yakalli Marwan yace yakake ganin za ayi Son? Do you think with condition na yarinyar zata iya aure ? Wannan karan hannu Marwan yasa yaja kujera yazauna danji yayi kaman zai fadi saiya dauki pen yabude wani file kaman yana rubutu dan baiso yakara making eye contact dako Abba ko Saleem zasu iya gane something is going on with him, da yar karaman murya yace I dont know Abba is her parents that can decide that Abba yadanyi jim yana tunani yace kuma hakane, how about kabani number mahaifinta? Ahankali Marwan yace bamu da number mahaifinta Saleem saiya juyo shima ya kalli Marwan din dayake rubuce rubuce kaman da gaske, Abba yace to zaka iya bani address na gidansu yarinyar ? Hannu yasa yadauki file na Amirah dake kan table nasa saiya mika ma Abba batare daya dago kai ba dasauri Saleem yamike yasa hannu ya karbi folder, hannunsa har rawa yake tsabagen kosawa, yabude folder Amirah, the first abu daya gani was sunan Aminatu so is that girl dayaga file nata a dakinsa rannan itace oh what a destiny. Dasauri yawuce address din yace ga address din Yaya ka dauka saikaje ka gayama Babanta karba Abba yayi yana karanta address din yace nasan layin nan sosai ai, zan nemi mahaifinta in sha Allah kam saiya rufe folder yaba Saleem, daidai pager na Marwan na ringing dasauri yamike batare daya hada idanu dasu ba yace Abba bari naje inada patients Abba yace to, to, toh kaje nima bazan wani jimaba zan tafi Dasauri Marwan yayi kofa yabude yafita. Juyowa Abba yayi yakalli Saleem cikeda so yace Saleem kasan abinda kakeyi kuwa? Kasan menene auren wacce batada cikakken lafiyayyan kai kuwa? Don t just think of now? Think about your future kids da sauransu, are you sure ? Ahankali Saleem yace Yaya nizan zauna da ita ba wani ba, yaran kuma nawane, ko gurguwace inasonta ahaka, idan kuma wannan ma bazaka tsayamin ba zan fita na nemi wayanda zasu tayani neman aurenta Saleem yayi maganan cikeda rashin kunya da rashinji, Abba yayi shiru yana kallonsa yazaiyi maraya ne Saleem, kuma amana, dan kallon Abba Saleem yayi jin yayi shiru ganin fuskansa yanuna baiji dadi ba saiyace m sorry Yaya, this days the only thin danakeyi is tunani, mesa zan kamu da son wacce ko sunanta ban sani ba banda yanzu danaga folder ta, soyayya magani ne and she can be fine, I sincerely love her and I will take care of her, Abba she s the most purest girl aduniya, she s like a dewdrop, very clean, fragile and pure Abba yayi shiru yana kallonsa kaman ba Saleem ba ahankali yace shikenan I will meet mahaifinta this weekend, ya jikin naka ? Ahankali yace fine tashi Abba yayi yace bari naje toh. Abba nafita yasake bude file din yana dubawa yana karance karance. Marwan na fita wani Dr daya gani yaje yatayasa duba patient din yafito da sauri yawuce motansa yabude yashiga yarufo thank god motan tinted ne babu mai ganinsa, glasses yacire da sauri yana wani irin nishi kaman mai asthma kirjinshi namai zafi, Allah yasani shi baisan takamaiman meke damunshi ba, is against ethics na profession nasa wato likita ya tsaya yana soyayya da patient nasa, patient dinsa is under his care, why would he harbor love feelings towards yarinyar da bamatasan menene love ba or understand menene so. Shi baisan ko sonta yakeba that s one, menene toh numfashinsa ke nema ya tsaya sabida Saleem ya nuna yana sonta zai aureta ahaka? Why is he feeling kaman zai mutu? Is he truly in love with Amirah? How? Why? And his brother too is inlove with her! Ya runtse idanunsa, daidai wayansa yahau kuka, ciro wayan yayi yana maida glases nasa ganin Ya Ammah ce saiyaki dagawa harya katse, wayan yashiga ringing Mami ce this time hakan yasa yadauka kafin yayi magana Mami tace kana ina Son is time for the meeting dan jim yayi saiya kalli agogon hannunsa, murya chan kasa yace Mami is already time for juma a daga masallaci sainazo ahankali Mami tace toh shikenan Allah kaimu lokacin, meya sameka why is your voice so down ?Ahankali yace kaine kedan ciwo Mami tai shiru kaman bata yarda ba tace kadawo gida kasha magani ka kwanta daga background din yaji muryan Farida tana Mami I want to talk to Uncle M, wayan yacire yasa a speaker ya ijiye kancinyasa Mami tace ga Farida zatai magana dakai ahankali yace okay yanajin muryan Mami tana cewa fitinanniyan yarinya. Farida tai dariya tana daukan wayan ashagwabe sosai tace Uncle M ahankali yace Anty F strictly Marwan da muryansa bata fita da kyau yace m at work banson shirme so what s the matter? Tafiya tashigayi he could feel tafiya take yaji karan tarufe kofa ahankali tace cikina ke ciwo and I took maganin nan is not stopping kawai saita sakin mai kuka yayi shiru, saiyasa hannu yadauki wayan yacire a speaker ya kara a kunnensa ahankali yace ask Faiza to make tea for you I will come back soon saina miki allura okay, stop crying ki kwanta and rest Gyadamai kai tayi tace ohkay katse wayan yayi kansa na sarawa, yakai 10min ahaka sannan ya kunna motan yaja nasallacin juma a yatafi. EPISODE 2 Yaune rana na farko dayake zaune yanajin hudba amman zuciyansa zafi yake masa kaman yayita kuka haka yakeji, sai kawai yafara kiran sunayen Allah hakan yasa yadanji natsuwa, shi baimasan sanda yafara sonta ba? Baisan mesa yakesonta ba? Amman jiyake kaman zai mutu sabida what ever is happening, ahaka akai salla aka idar sannan yafito yana tafiya ahankali yashiga motan sa yaja zuwa gida, horn yayi Musa yabude masa gate yakarasa yayi parking yana kallon motocin dake compound wanda duk na yayyinsa ne he thought by now kowacce ta tafi yanzu zasu damesa. Bude kofan motan yayi ya fito ba labcoat ajikinsa yabarsa a mota, sai yar small Leda asibitin su wanda na alluran dazaima Farida ne a hannunsa yawuce da sallama yabude kofan falon yashiga ciki yana maida kofan yarufe all sisters dinshi suna falon saikuma wata da kallo daya yamata yadauke kai cus baisan wacece ba kuma baiga amfanin kallonta ba, Mami ta tsaresa da idanu tace ya juma an? Ciwon kan ya sauka ? Anutse yace Alhamdulillah Mami, where s Farida? Mami tace suna dakinsu sun kwanta ahankali yaji wata murya tace ina yini Ya Marwan dan tsayawa yayi saiya juyo ya kalleta still baiganeta ba gashi sai kallonsa take, gyadamata kai yayi alamun yauwa yajuya abinsa yayi staircase sai Ya Fadila tabisa yayi sama Mami na kallonsa, Ya Fadila na whispering. Wai is this how you treat girls Doc? Dan juyowa yayi ya kalleta looking confuse yace ? Daidai sun karasa sama kamasa tayi tace didn t you recognize that girl? Marwan yace which girl ? Ya Fadila takama kanta tace Ya Allah wani kalan mutum ne kai Marwan saita juyar da kansa tai masa pointing Ramla tace that girl dake zaune next to kujeran Mami is she not the girl data taimaki Mami a airport, Mami asked her to come here dan muganta tana sonka da yarinyar and she s good kasan mene, she studied accounting as Major a Florida, tanada masters, and she s only 26, very young uhm Marwan lumshe idanu yayi sannan yabude yakalleta yace I have no business with whatever you guys are doing here, I came back for meeting idan kuma bashi zakuyi ba i have plenty patients waiting for me a hospital plus I have headache kafin tai magana yawuce dakin Farida ransa abace abin yaba Ya Fadila mamaki hardly Marwan ke fada haka. Su Mami suka cigaba da hira dan daman bata nunama yarinyar komiba tun jiya sukai magana itane ma tace tanaso tazo ta gaida Mami, Mami tace mata tazo yau juma a, Mami ta lura yarinyar takamu da son Marwan and tanada hankali she just wish Marwan will see the girl. Allura yama Farida yakalli Ya Fadila dake kansa yace m hungry give me food balla masa harara Ya Fadila tayi tace kira Mamanka Mami mara mutunci mai masifa dan murmushi Farida tayi ta yunkura tace Uncle nizan kawo maka dasauri yace no kwanta abinki Ya Fadila tace au iyye hakane yarinya wato I love my uncle I don t love my Aunty zaki kirani ai ina zaman zamana for something Farida baniba boye kanta tayi abayan Ya Marwan tana murmushi, shima Marwan yayi murmushi kadan, Ya Fadila tajuya tafita yajuyo yana kallon Faiza datai bacci yace kema sleep gyadamai kai tayi sai ahankali tace Uncle you don t love that girl right? Tsareta yayi da idanu yace ? The one that s with Mami downstairs, ahankali yace do you love her ? Girgizamai kai tayi tace ahankali yace why? Ahankali tace cus I know she s not the type of girl you will love tsare Farida yayi da idanu yace what type of girl do you think I will love murmushi tayi tace someone like me and Faiza tsareta yayi da idanu saiyaja hancinta baice komiba yamike yanajan bargo yarufe mata yajuya yafita daga dakin daidai Fadila na hayowa sama da abincin sa a tray ya kalleta ta ballamai harara tace Mami tace kagama ci ka sauko katayata sauke Ramla agida kafin kawuce asibiti baice komiba
Chapter 30 · 0% Book details