← Book details Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 87

Sashe 41

Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da tun yana ganin dishi dishi harya fara washewa idanunsa yana ganinta da kyau da sauran yayinsa Mami cikeda so tashafa fuskansa tace Alhamdulillah, Alhamdulillah Marwan kaganeni ganinan Mamin ka ? Wani kalan sanyi yaji yanaji saiya lumshe idanunsa yabudesu ahankali yajuyar da idanunsa sai ya daura kwayan idanunsa akan Amirah dake tsaye ita kadai wajen kofa kanta akasa hannayenta duka biyun abakinta standing she looks like an angel, ya tsareta da gajiyayyun idanunsa na marasa lafiya dayasa daga Mami dasu Ya Maryam dukansu suka juya dan bin direction na idanunsa suka abinda yake kallo haka, sai sukaga yarinyar data shigone dazu ba sallama nor gaisuwa Marwan ke kallo, ahankali Mami tace bamusan wacece ba kasanta ne? Baiyi magana ba idanunsa still na kanta, wani irin kallo yakema Amirah da tunda Mami tasan Marwan tun yana a year old bata taba ganin yama wata irin wannan kallan kallon ba, dan kallo ne dake muna tsantsan madaran so da matukar kauna, dakuma bege, sai Mami tasake juyawa itama takalli Amirah da kyau from head to toe, she looks like patient na inda Marwan ke aiki, she s wearing uniform na mahaukata and from the way batai magana ba kuma tasa hannaye baki tanaci kasan she s not that okay, sai Mami takalli su Ammah dake kallon Amirah tace ku koma wajenku ku zauna basuyi musu ba dukansu suka koma suka zauna sai Mami ta sauka daga gadon ta matsa gefe tana kallon Amirah tace kinzo duba Dr ne yarinya ? Amirah kaman bada ita ake magana ba ko kanta bata daga ba, ahankali Mami tace zoki gaidasa sai kawai Amirah tashiga tafiya ahankali ahankali kanta akasa tana tahowa still hannunta abaki looking damn adorable, Mami tajuyo tazubama Marwan idanu dake wani kalan kallonta, Marwan is in love with a mad crazy girl? Mami ta tambayi kanta! Zuwa gaban gadon Amirah tayi saita tsaya dab dashi saita dakata da yanda take cizan hannunta amman bata ciro hannun daga bakinta ba saita shiga dago idanunta ahankali kadan kadan tadaura akan Marwan da idanunsa ke kanta bayako kyafta su yana wani irin kallonta kaman yau yafara ganinta, tsaresa Amirah tayi da idanu itama fararen idanunta na kyalli kaman an wanke da madara, wani abu taji yazo mata wuya mara dadi ganin duk ciwo ajikinsa ga waya a hancinsa na oxygen, he looks so sick and not strong, Ammi da Miemie suna rashin lafiya zata tsaya taita kallonsu batajin wani abu aranta, well kotanaji ma bata saniba amman yau seeing Marwan saitaji ciwon data gani a jikinsa tanaji anata jikin, saitaji wani abu kaman tausayi kaman ciwon yadawo jikinta shi ya warke sai kawai tahaujin abubuwa da batasan na meba kuma batasan yaya zatai controlling kanta ba, sai kawai ta duko tana cire hannayenta abaki, tashi daya tai hugging nasa ta kifa kanta a wuyansa takai hannunta mai bala in taushi dayayi zufa and saliva nakai sosai ta ijiye a gefen fuskansa kan sajensa da kunnensa ta kankamesa kawai tashiga rera kuka mai sanyi da zaki dakeda dan sound a kunnensa tana shesheka bana wasaba, tasake kwakumesa ta kankamesa batare data damu da akwai mutane adakin ba. EPISODE 3 Dawani irin sauri Mami tadauke kai daga kallonsu hakama sauran yayinsa like babu wanda ya iya motsi ganin yanda yarinyar ta kankame kaninsu tanamai wani kuka that sounds like kukan shagwaba da damuwa da tsoro, Ammi data kasa shigowa dakin ta tsaya jikin kofa amman tana iya gano komi ta yar karamin glass dake kofan ta tsaya turus itama ganin abinda Amirah tayi kirjinta na bugawa dum dum dum!, Wani abu Marwan yaji tundaga kafafunsa zuwa kwanyan kansa yanda Amirah just hugged him so tight feeling scent of hijabin da Ammi takawo mata dake kamshi mai dadi sosai na turaren wuta, hannunta a gefen fuskansa that is moist zuciyansa kaman zai bude yanaji kaman yakamata yasa a zuciyansa yaji sauki, lumshe idanu yayi yabude kadan, ga yayyinsa awajen duk saiyaji kunya especially yanda babu wanda yayi magana cikinsu, he knows dole Saleem da Abba suna this hospital, danne feelings nasa yayi tunawa da Saleem zata aura, bakinsa da ba karfi dan ko ina na jikinsa yamai nauyi sabida anesthesia, muryansa ba wasa ciki cikin dakewa yace stand up from my body kin motsi Amirah tayi bataso tasakeshi, bataso ta tashi daga jikinsa, murya chan kasa mai bala in dadi Marwan yace Ameenah! Ahankali batare data cire hannunta daga fuskansa ba tadago fuskanta takawo dab da nasa takallesa daidai hawayen dake fuskanta shabe shabe suna diddigowa fuskansa lips dinta sunyi pinkish sosai sabida uban kuka amman tamai bala in kyau kaman ya lallasheta, yana kallon kwayan idanunta sosai yace dagani! Batai musu ba Amirah ta taso still crying tana kallonsa yakalli fuskanta wani iri yaji yasake runtse idanu yabude kadan but this time bai kalleta ba, saida ya dake sosai kaman bai santa ba yace meya kawoki nan? Shiru Amirah tayi batai magana ba tana kuka tana tabe baki yanda yara kanana keyi, sai Marwan yakalleta jin taki magana yadaure fuska sosai, yace Mami kiramin any nurse azo amaidata ward ahankali Mami tace okay Amirah takara rushewa da kuka jin yace azo atafi da ita, daidai Dr dazu tashigo dakin suprisenly tace saida kikasa mamanki takawo ki nan ko Amirah ? Kallonta Dr Marwan yayi, Dr tace yes her Mom come today tadubata ta tambaya ma ko zata iya tafiya da ita nace I have to tell you first juyarda kansa Marwan yayi gefe, ahankali yace discharge them adinga kawota for session weekends Dr tace yayy you can go home now Amirah takalli Amirah dake kallon Marwan sosai hawaye na sauka daga idanunsa, Marwan yace tafi da ita sutafi gida Dr Dr tajuyo takalli Amirah tace s go kin motsi Amirah tayi, hakan yasa Marwan yajuyo yamata wani mugun kallo yace wuce kutafi gyadamai kai Amirah tayi batai musu ba saita juya ahankali, Mami da kowa na dakin na kallonsu daga Amirah har Marwan, tabi Dr ahankali tana tafiya kadan kadan tana juyowa tana kallon Marwan dake kallonta shima da sanyayyun idanunsa har suka fita daga dakin. Ammi was not at door, tunda taga katobaran da Amirah tayi, bataso ma iyayensa su ganta ko shi Marwan din kunya bazai barta ba saita wuce takoma wajen bene, tana wajen bene tsaye tanabin Amirah dake goge fuskanta da bayan hannu still hawaye na sauka biye da likitan, Dr tai murmushi tana kallon Ammi dake bin Amirah da kallo tace yauwa Dr yace zan iya sallaman ku zaku dinga zuwa check up weekends, yanzu tunda cikinta na ciwo zan rubutamuku maganin dazaku saya gyadamata kai kawai Ammi tayi takasa magana saita sa hannu ta kama Amirah suka shiga sauka daga staircase din saiga Saleem da Abba suna dawowa daga mosque ganin Ammi da Amirah dawani kalan sauri Saleem yazube gabanta da guiwa har kasa yace ina yini Mama dan tsayawa Ammi tayi ganin mutum agabansu yaduka har kasa yana kallonta, Amirah dasauri takoma bayan Ammi tai lamo tana manna fuskanta abayan Ammi, Abba yakalli Amirah sosai, ahankali Ammi tace lafiya bawan Allah, tashi dan Allah Saleem yatashi yana murmushi sosai yace Yaya ga Mamana nan, ga Amirah kuma Abba yace ba shakka ina yini Madam ya mai jiki ? Itadai Ammi bata sansu ba amman ganin yanda suke gaidata maybe suma iyayen patients ne sanadin hakan sukasan Amirah sai cikeda girmamawa tace Alhamdulillah Ya Iyali, Amirah bazaki gaisuwa ba ? Wani sake kankame Ammi Amirah tayi abayanta ko fuskanta baka gani Abba yace barta, barta Ammi tai murmushi tace to sai anjiman ku tawuce Saleem yawani bisu da kallo especially Amirah da hijabinta yakama jikinta yabi curvy ass nata da kallo har saida Abba ya tallabe masa kai firgigit Saleem ya kalli Abba yashafa kan yana turo baki Abba yace wuce muje karka cinyeta da idanu suka wuce. Amirah na fita Mami ta zauna awajen tace yaya jikin meke maka ciwo ? Girgixama Mami kai Marwan yayi daidai su Abba na dawowa lumshe idanu Marwan yayi Saleem yafara shigowa cike da farin ciki yace Mami, Mami, Mami Mami ta juyo dasauri Jin yanda Saleem ke kiranta, dasauri yace I saw Amirah tareda wata Dr probably nan sukazo kun ganta? Wata yarinya haka yar fara tana sanye da uniform na hospital da milk hijab kunganta Mami, she s full haka tanada diri, Ya Ammah kunganta? Abba saida yaji kunya yanda Saleem yace diri, gyadamai kai sukayi alamun eh, wani cute smile yayi yace itace Amirah dazan aura! Bugawa kirjin Mami yayi haka ma sauran yayyin Marwan, Saleem yace this Saturday zamu daura aure she s so pretty right Mami ce tai karfin hali tace Masha Allah, Allah yasa albarka Saleem murmushi yayi yazo wajen gadon yana kallon yanda idanun Marwan suke a lumshe yace probably tazo tagaidashi ne but bai tashi ba ko ? Wannan karan Mami batai magana ba amman itama kallon Marwan din tayi dayayi kaman bai tashi ba kuma tasan idanunsa biyu yanajin komi, Abba yace Allah yabasa lpy duk suna zaune a dakin kaman daga bayama baccin daukan Marwan yayi da gaske to dama meya tadasa dazu? Dan lokacin tashi sa baiyiba, da magrib Mami takalli su Ammah tace tashi ku kokkkoma gida kunbar yara Abba yace gaskiya ku tashi, harda kema u Faiza nachan duk sun damu ahankali Mami tace anan nakeso na kwana Alhaji Abba zaiyi magana Saleem yace Mami zan kwana dashi kutafi gida girgixakai Mami tayi tace no Saleem inhar ban kwana anan ba hankalina bazai taba kwanciya ba, dan Allah karku hanani dan Allah Alhaji shiru Abba yayi saiyace to shikenan yanzu medame kike bukata sai muje gida mu kawo miki? Ammi tace kutafi zan kira u Faiza na fada musu zasu hada komi saisu baku Abba yace toh kumuje yatasa su Ammah agaba duk suka tafi dakin yarage just Mami da Marwan dake bacci jikinsa ma harda gajiya baya hutawa she will personally talk to Dr dudda tasan za a basa hutu but abasa mai tsawo ya huta ya warke tai salla tadawo tazauna Doctors suka shigo dubasa hakan yasa tafiya dan kiran su Faiza, una zuwa gida agurguje Saleem yayi wanka anan daki yakara maimaita sallolin dayayi a masallaci dan bazai iya cema Abba yanada najasa ajikiba yagama yayi ishai
Chapter 41 · 0% Book details