← Book details Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 87

Sashe 53

Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

taci sosai sannan ta kalli Ammi tace Ammi anjima zamu tafi gidan Ya Marwan? Gydamata kai Ammi tayi, murmushi tayi tacigaba da cin abincin sosai taci tana gamawa sai bacci, gyaramata kwanciya Ammi tayi tafito daga dakin tana kallon Miemie dake tareda kawayenta Miemie tayi kyau sosai, tadade tana bacci sai bayan asir ta farka Miemie tagani kusada ita tana kuka tana goge hawaye tashi Amirah tayi zaune ta tsareta da idanu saita matso ahankali tazo kusada ita murya chan kasa like a baby tace menene? Cikin kuka Miemie tace Amirah banson narabu da Ammi dake, banso saita rungume Amirah tana kukan wani iri Amirah tashigaji sai hawaye yashiga cikowa a idanunta, ahankali tadago Miemie saitakai hannunta kan fuskanta ta girgiza mata kai alamun tadena kuka, Miemie tadade tana kallon Amirah saita gyadamata kai, daidai Ammi tabude dakin tashigo takalli Miemie da idanunta sukai jajir anatse tace kuzo ku shirya anzo tafiya daku daidai nan Lami na shigowa dakin tace ina suke muje muje ga motoci sunyi layi a waje ana magrib zaku wuce, muje muje tai wajen Miemie tadagata suka fice, Ammi takalli Amirah tace zomuje tasowa Amirah tayi saitazo dab da Ammi tana kallon fuskan Ammi sosai cikin yar karaman muryan nan tace Ammi ai tare zamuje gidan Yaya Marwan ko ? Tsareta da idanu Ammi tayi saita gyadamata kai kawai, murmushi Amirah tayi ta rungume Ammi suka fito tare tana mammannewa jikin Ammi tana boye fuskanta wanka Ammi takaita tayi dawani ruwan turare sannan tafito da ita sukaje daki Ammi da kanta tashiga shiryata cikin wani lafaya black and red tasata tai salla Ammi bata mata wani kwalliya ba tasa mata kwalli saita zauna gaban Amirah tana kallonta hawaye Ammi taji zasu zubo daga idanunta dasauri tadauke kai dakin aka bude dasauri Amirah ta tashi taboye bayan Ammi tai lamo kaman yar yarinya, Lami dasauran manyan matan wajen suka shigo da Miemie dake kuka sosai an lullubeta sukace ammm Ammi ga Miemie za a tafi da ita tsareta da idanu Ammi tayi saita lumshe idanu bata taba sanin this is how a mother feels when she s saying goodbye to her children ba sai yau, she s feeling kaman ta taya Miemie suyita kuka tare sabida yanda takeji amman saita dake anatse tace Maryama I know daidai gwargwado nabaki tarbiya mai kyau, ke yarinya ce mai hankali da bazaki taba bani kunya ba, baki taba kuntata min ko batamin raiba, I pray Allah yabaki farin ciki irin wanda baki taba tunanin zaki samu ba gidan mijinki Allah ya albarkaci aurenku, go start your new life kinji My Babygirl Miemie rungume Ammi Maryam tayi tama kasa magana sai kuka da kyar tace Ammi banso narabu dake dariya akahau yi adakin itama Ammi tai murmushi tace ai duk diya mace saita rabu da iyayenta mumanan duk hakane maza dena kukan nan Ammi ta dagota, bakin mayafinta Ammi takama ta share mata fuskan tasss saita manna mata kiss a goshi tace go to your home Maryam wasu sababbin hawaye ne suka shiga zubo mata. EPISODE 5 Lami tace muje toh ahankali Miemie ta tashi saita zagayo bayan Ammi tai takalli Amirah dataga idanunta sun ciko da hawaye duk tayi wani irin kaman tasoma gane abin is getting real, ahankali Miemie tace kin haddace number na dana Ya Umar ko? Gyadamata kai Amirah tayi ahankali, Miemie tace toki kirani idan kika sami waya kinji bazan iya rayuwa babu ke ba Ya Amirah, you re my best Sister kuma in sha Allah zaki warke Ya Marwan zai kula dake kinji gyadamata kai Amirah tayi tana kallon yanda Miemie ke kuka saita rungume Miemie ahankali tace kuka bari tadagota tana share mata fuska murmushi Miemie tayi tace tom nadena, Bye Ya Amirah na Lami tazo takama Miemie suka fita da ita daga dakin Amirah tabisu da kallo sai kawai tafado jikin Ammi tana kuka sukaje waje. Ammi tariga tagayama Lami itace zatabi Amirah cus Amirah bata yarda da kowa hakan yasa sai Harira kanwar Lami itane jagoran kai Miemie gidanta, saida Lami ta tabbatar an shiga mota sannan aka tafi yarage saura motocin su Tawagan Marwan, friends nasa guda biyu that are Drs yasanar sai Abba yabada motoci da drivers guda uku, dawowa dakin Lami tayi da kawayen Ammi dakuma makota har lokacin Amirah kuka take, da idanu Lami tama Ammi alamun it s time, dagota Ammi tayi tace dena kukan yanzu tashi kibi Mama Lami kutafi gidan Mijinki Marwan anjima kadan ni sainazo idan na sallami baki na makema Ammi kafada tayi cikeda rigima alamun a a, Ammi tadan hada fuska tace kinason nayi fushi dake ? Ahankali ta girgizama Ammi kai, Ammi tace yauwa yarinyar kirki tashi to kuje, muje nasaki a mota da kaina kasa ma tashi tayi daga jikin Ammi da kanta Ammi tadagata daga jikinta saita gyaramata mayafin saita bata wani flat shoe black na Gucci ya Allah kafafunta sunyi kyau a takalmin tasaka Ammi tai jimmm tana kallonta itama Amirah haka sai kawai Ammi ta rungumeta Amirah ta kankame Ammi kaman jira take tafashe da kuka, Lami ta girgizama Ammi kai alamun kartai kuka da kyar Ammi ta daure saita dago tace ke yarinya ne kike kuka haka, wuce muje Ammi takama hannunta da kanta Ammi tafitar da ita har waje jama a na binsu abaya wata roll Royce Dr Hassan yabude yace motan Amarya ne wannan Ammi da kanta tasa Amirah aciki Lami tashiga ta dayan side din, su biyu kawai zasu zauna a motan sabida yanzu tana ganin jama a saita rikice, Ammi ta dake tai murmushi tana kallon Amirah data rirriketa that looks so scared tace Ammi mutafi Ammi tace eh bari kutafi zan taho uhn yarinyana tayi kyau, Lami bari nai sauri ganinan zuwa Lami tace yauwa kiyi sauri Maman Amirah Ammi tace to cikani sabida nai sauri na biyoku ahankali tasaki Ammi tana kallon fuskan Ammi sosai, Ammi tamata murmushi tace good girl bari naje toh da sauri Ammi tai maza tamaida kofan tarufe tawuce zaure Amirah tabuta da kallo aka kunna mita akaja Ammi na labe azaure tana kallon ana tafiya da Amirah ta gidan miji kawai sai Ammi tafashe da kuka duk yanda zatai bayani bazata iya ba, but she s feeling too many things at a time, her only two daughters leaving her in the same day to start a new life, cikin those 2 imagine the sick one, that s helpless, weak, have zero idea how the world is itama ta tafi gidan miji, Amirah should be by her side, she should be protecting her not ta aurar da ita me Amirah tasani what if Marwan is not a good man ya cutar mata da yarinya eh? Babu abinda Ammi bataji kaman tafita tace adawo mata da yarta tafasa aurar da ita she s feeling so lonely Wayyoo Allah na, idanun Ammi har saida suka kumbura sabida kuka sannan ta lallaba ta tashi tashiga ciki. s calling again Dr Hassan dake tuka motan yafadi yana daukan wayan, Hey Dr ka kirani yafi sau miliyan yau, yes mun daukota she s here we are on our way dan juyowa yayi saiya ba Lami wayan yace mijinta wants to talk to her Lami murmushi tayi ta karbi wayan saitace Amirah ga Mijin naki tabata wayan karban wayan Amirah tayi garin karba tasa a speaker, murya chan kasa Marwan yace Ameenah Kaman yabude abinda ke rike mata kuka kawai saita fashe da kuka sosai harda wani rerawa Marwan yayi shiruuuu yana sauraronta chan saiyace so kike ki kasheni! Dan zaro idanu Lami tayi dasauri ta juyarda kai Dr Hassan yayi murmushi, Amirah da baruwanta da wayan na speaker ta girgizamai kai alamun noo, asanyaye cikin lallashi da tsantsan kauna yace stop crying kinji gyadamai kai tayi asanyaye yace wat do you want me to buy for you ? Ahankali ashagwabe tace wayaaaa ahankali yace mezakiyi da waya? Miemie murya chan kasa yace okay zan sayama matana waya wanda yafi na kowa kyau dazata dinga kiran Miemie, da Ammi, da Ya Mustapa da Baffa aciki ko ? Shiru tayi tana sauraronsa hankalinta nawani kalan kwanciya mamaki yakashe Lami daman Marwan din na magana haka, ahankali Amirah tace dan shiru Marwan yayi duk yanda yaso yadaure yakasa murya chan kasa yace m so happy you ve become my wife Ameenatu, and I m ready to give you not just this world but my entire life, I Love you! Wani bugawa kirjin Amirah yahauyi Dr Hassan ganin kar abokinsa yawuce gona da iri ga iyaye a mota yasa yace yoh Docs you re on speaker wani kunya Marwan yaji dasauri ya katse wayan. Amirah ta ijiye wayan jikin Lami tai shiru kanta sai maimaita mata I love you I love you yake, daga wajensu zuwa bangaren su Marwan it s soo far is like daga area yaku bayi zuwa area masu kudi almost an hour drive sukakai family house nasu Mami inda akai decorating sosai za ayi kamu parking akayi a dankareren compound din ganin mutane a compund din sai Amirah tarike Lami dasauri tana shirin fashewa da kuka ta tsorace tace Ammiiii cikeda hikima Lami tace Ammi na wajen nan muje ki ganta daidai lokacin Mami datasha shigan alfarma dasauran yayin Marwan sunzo wajen ana guda harda su Faiza da Farida da sun kosa suga wacece matan Ya Doc, dudda kan Amirah a lullube but tana ganin kowa ganin fuskokin dabata saniba sai kallonta suke suna murmushi suna guda saita wani koma baya dasauri tashige jikin Lami taja gyalen lami tarufe fuskanta duka tana sakin kuka ahankali kaman zata koma cikinta dan jimmm Mami tayi saita kalli su Ya Ammah tace ku wuce ku tafi babu wanda yayi musu duk suka wuce, ahankali Mami tamika mata hannu calmly tace Amirahhhhh! Dan dago kanta daga jikin Lami tayi Lami tace je mamanki na kiranki hannunwanta Amirah tasa taja mayafin baya ta kalli Mami dake kallonta tanama Mami kallon tsoro idanunta na fitar da hawaye, sosai Mami ke kallon Amirah Ya Subhanallah Allah yayi halitta mai kyau awajen nan yarinya kaman ita tai kanta, and shes so adorable yanda take kukan ashagwabe, anatse Mami tace taho muje bazan bari su kalleki ba kinaso kiga Marwan ? Tsare Mami tayi da idanu kaman bazatai magana ba
Chapter 53 · 0% Book details