← Book details Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 87

Sashe 7

Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

magunguna daga baya ma sun dena zuwa sai yau, dago kansa yayi daidai Ammi na kallonsa tace Doctor dan Allah amana afuwa taki zama dakanta haka takeyi inhar taganta awaje da jama a duk saita fara yan abubuwan nan taki barina sukunu dazaran nai kokarin barinta taita yanka uban ihu Anatse Marwan ya gyadama Ammi kai yace meke damunta? Cikeda dan damuwa Ammi tace gabaki daya tun jiya da rana datai bacci har yanzu bata sake kulle idanunta ba batai bacci ba sannan jikinta yayi zafi sosai Doctor kaman wuta, takicin komi, kuma sai dilalyar da yawu take abinda batayi da, gakuma tari yanzu da bansan daga ina yazo ba rubutu Marwan yayi, yakalli Ammi yace tana iya gayamiki abinda ke mata ciwo? Kota nuna miki ? Girgiza kai Ammi tayi tace ah bata iya fadin abinda ke mata ciwo ba Doctor, sannan bata nunawa, saidai kaga tarasa sukuni, kotaita zufa, kokuma idan ciwo taji taita kallon ciwon Meya sami hannunta? Marwan ya jefoma Ammi tambayan yana rubutu da saida Ammi tai mugun mamaki dan na farko batasan tayaya yaga tafin hannun Amirah ba, kuma kwalban plate data fasa jiyane anan taji ciwon, kafin Ammi tai magana yace is she violent? Tanada fada da dukan mutane? Is she aggressive? Ita ce tama fuskanki rauni? Dasauri Ammi tace rauni ? Cus ta kalli madubi babu wani abu a fuskanta, dukan da Daddy yamata na nunawa a fuskanta ne? Ahankali Marwan yace yes your face, hands is she the one responsible ? Dasauri Ammi tace a ba ita bace ? Ahankali for the second time sounding very professional yace Meya sami hannunta? Jikin Ammi yadanyi sanyi kadan tace makami tadauka jiya yaji mata ciwo, jiya kanwarta na aure akwai jama a gidan sosai Marwan bai sake magana yace gwada kwantar da ita agadon l kokisa ta zauna on her own muga inaso nadubata ahankali Ammi tace ahankali Marwan yamike yadauki sthethoscope yamakama a kunne yazagayo yana tafiya one one. Ammi tacirota daga jikinta tace Amirah na bude idanunta tayi da kyar ahankali daidai akan idanun Marwan, Ammi tace tsaya kwanta anan muga Ammi tai maganan tana share mata pink plumpy lips nata that are so moist sabida saliva, cikin wani kalan siga na shagwaba dakuma rashin lafiya tataho tanaso takoma jikin Ammi, Ammi takai hannunta fuskanta takama habanta tace Amirah kinga inaso kizauna kinji Dr yadubaki saimuje gida ko zauna to, Miemie na jiranmu awaje fa, yauwa kwanta muga Ammi zata kwantar da ita kin kwanciya tayi tasake chukuikuyi Ammi, hakan yasa Ammi ita tazauna gadon takamota dasauri Amirah ta manna fuskanta a hannun Ammi, Dr Marwan yadan dago kansa yakallesu saiya taho ya tsaya gaban gadon yadan sake fuskansa sosai saiya sa hannunsa a aljihun labcoat nasa yaciro wani sabon chocolate na bounty babba yace Hajiya kinashan chocholate ? Murmushi Ammi tayi ganin Dr is good tace ni ai na tsufa banashan chocholate amman daga gani gaskiya zaiyi dadi, kuma kasan Amirah tafison chocolate kan komi aduniyan nan ahankali yana kallon hand movement nata ganin tafara sakin hijab na Ammi yace Ameenah! Wani girrrrrr kan Amirah yayi cus bata tabajin wani arayuwanta yakirata Ameenah ba, ko Ammi Aminatu suke cewa, wani kalan dadi Ammi taji jin tana motsi tace maza tashi ki amsa kafin Dr yafasa baki yaje yaba wasu, maza ungo ahankali ta shiga motsi amman taki ciro fuskanta Ammi ta kamota gentle tafito daga jikin Ammi kaman mai tsoro Marwan ya tsareta da idanu dudda side na fuskanta kadai yake gani, takalli Ammi, Ammi tace maza amsa Dr yana baki Ammi tai maganan tanadan juyoda kanta, ahankali Amirah tajuyo ido da ido tayi da Dr Marwan for the first time ya tsareta dawasu kalan idanu dake cikin glass, wani iri taji a feeling da batasan meba sai kawai takoma jikin Ammi da gudu tai lamoooo tadauke idanunta daga fuskansa tana kallon chocholate din, ahankali Marwan yashiga tahowa dab dasu Amirah ta runtse idanunta da gudu tawani irin kankame Ammi, ijiye chocolate din yayi a gefenta sannan yajuya Ammi tace Iyye Dr yabaki chocholate bakice kin gode ba daukan chocholate din tayi tarike gamgam a hannunta. Komawa seat nasa yayi yazauna ahankali saiya dago kansa ya daura idanunsa akansu kanta fuskanta na kirjin Ammi ga chocholate din tarike gam saiya maida kansa yayi rubutu yadanna wani bell saiga nurse tai knocking tashigo office din yabata wata yar takarda yace I need this test done on her nurse tace sannan yakalli Ammi anatse yace first thing first we will run some test and know why she s running temperature nadaurata kan treatment before we address her main issue, I want you to go with the nurse amata test yakalli nurse din sannan yakalli agogon hannunsa yace ASAP I need to be somewhere dasauri tace yes Dr tashi Ammi tayi tana kamata tace muje Amirah chukuikuye Ammi tayi suka wuce suka fita daga office din Miemie na ganinsu ta taso tace Ammi me Dr yace Ahankali Ammi tace test zamuje ayi mata yanzu Miemie takalli chocolate dake hannun Amirah tace laaa waya baki chocolate dinnan mai tsada Ya Amirah ? Nurse dake jinsu tayi dariya tace haka Dr M ke rabama patient gift, saisa patient sunfi sonsa daidai nan sukakai lab nurse tasa amusu test din tace kawo hannunta Madam Amirah na jikin Ammi, Ammi takama hannunta dake free ta mike tace gashi Miemie dinga mata magana inba hakaba bazata tsaya ba mai deban jinin ya kulla roba a hannunta saiya saka hannunsa yakama hannun nata zai saka allura Amirah tazabura tajuyo da kanta tana ganin allura tawani kurma ihu zata tashi Ammi tace saikun tayani riketa ta tsani allura yarnan dasauri nurse tasaka hannu suka kamata, bawai fuskanta akwai tsoro bane but kawai bataso allura ne da kyar suka riketa akaja jinin aka saki hannun, Ammi tace yakuri yakuri ta bubbuga bayanta Amirah tai lamo ajikin Ammi tana sauke ijiyan zuciya tana kallon chocholate din na hannunta, Ammi najin yanda kirjinta ke bugawa dimdimdim, waje suka fito suka zazzauna Ammi tadauki Fanta daga jakanta tace sha Fanta bakici komiba wlh Amirah gaki bakida lafiya eh turewa tayi zata komar da kanta jikin Ammi, Miemie tace bataso ne Ammi saita kawo fuskanta wajen na Amirah itama ajikin Ammi tana kallonta tace zakici wara na sayo miki ? Dan bude idanunta kadan Amirah tayi tadaurasu akan Miemie kaman mai nazarin fuskan Miemie, Miemie tayi wani murmushin jin dadi ganin yau Amirah ta kalleta wlh inhar Amirah tabari kahada idanu da ita to kanada luck suna wattanni Amirah bata kalli kwayar idanunta ba amman yau ta kalla, dasauri Miemie tace yauwa fadamin kinason wara na sayo miki? Mai yaji da cabbage? Shiru tayi tana kallon Miemie sosai batako kyafta idanu, Miemie tai wani murmushin jin dadi tace Ammi kinga yanda Ya Amirah ke kallona kuwa yau, in sayomiki ? Lumshe mata idanu Amirah tayi ahankali tabude tareda dan motsa kai kadan alamun eh, dawani irin sauri Miemie tace yesss, Ammi bani kudi nasayo mata tace zataci Ammi batai musu ba dan tadamu yanda bataci abinci ba tabata 500 Miemie ta karba tawuce tafita taga masu wara achan waje. Suna zaune awajen Nurse tazo da result na Amirah tace muje ga result dinta, yafito tashi Ammi tayi da Amirah dake jikinta sukai office din har lokacin chocholate din na hannunta, suka shiga office din da sallama, this time babu wanda ya kalla cikinsu, nurse ta taho tabashi result din ya karba, yana duba lab report din, Ammi saita sake zama bakin gadon, Amirah na jikinta ita a tsaye this time taki zamama, gama kallon result din yayi saiyadan sauke ijiyan zuciya ahankali yace I will love to admit her Hajiya dan faduwa gaban Ammi yayi sosai takallesa dasauri tace Dr meya ke damun Aminatu da za a kwantar damu ? Calmly yace calm down Hajiya, bawani babban abu bane amman tanada high malaria da typhoid sosai, which I will zanzo nai admitting nata sabida abata proper treatment dasu antibiotics, high fever awajen yara irinsu dabawai zasu iya bude baki su maka bayanin meke damunsu bane baida kyau kwata kwata, yanada hadari, already ga separate matsalanta zazzabi mai karfi haka yakan damula al amuran kwakwalansu, misali kince tanata dilalar da yawu which on a normal days abune da batayi amman kinga kadan daga cikin abinda zazzabi ke sakasu kenan yi, she s even strong wasu dakeda maleria a level da nata yake can not even stand on feat nasu like this, so can I go ahead and put her on admission sabida mufara mata treatment immediately? Shiru Ammi tayi tana tunani gabanta sai faduwa yake, ance treatment nasu is free but on reality subsidy kawai ake baka ana rage kudi ne but you still get to pay, ko test dinnan da akayi mata saida tabiya amman just 2k tabiya, ina taga kudin biyan na admission? Kuma bata gayama Babansu sun fito ba, atleast su koma gida tabasa hakuri inyaso saisu kawota asibitin tare dudda abune mai wuya amman dai yasan da ita incase kudinta sun gasa sai yakawo nasa kudin, Amirah is strong duk uban zazzabi tanada karfin hali, ahankali Ammi takalli Dr Marwan da tunda yayi maganan ita yake kallo ganin tanata tunani tace ahmmm, ban sanar da mahaifinta muna nan ba ammm Ammi tadanyi shiru chan tace Doctor baza a iya bamu magunguna da allurai sai muje gidaba? Ahankali yamaida kansa kasa yana rubuce rubuce yace a iya, kawai the best treatment is for her to be on admission muyi observing nata, that s my professional advice as her Doctor, but you can choose abinda you feel is best for her and is more comfortable for you, shan magani agida works but in her case putting her on admission is the best dan shiru Ammi tayi tadan dubi Amirah datai lamo ajikinta idanunta a lumshe tana numfashi sama sama, bakinta har nauyi nauyi yake mata tsabagen yanda zuciyanta baya mata dadi tace abamu magani muje gida Doctor na sanar da mahaifinta saimu dawo dan jimm Marwan yayi sai chan ya gyara glasses na idanunsa yace okay yayi rubuce rubuce yadago kansa zai mikamata daganan saiya fasa yataso yazagayo yazo har wajen gadon saiya mikamata yace allura da magunguna idan kin saya zasu mata allura,
Chapter 7 · 0% Book details