← Book details Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 87

Sashe 85

Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

har fitsari saida ya kufce mata, Baffa yatashi yazo wajen yace saketa nace Ammi tasaketa Amirah ta kankame Baffa tana wani kalan ijiyan zuciya kaman zata mutu jikinta bari kawai yake tana kuka, Baffa yace haba so kike yarnan ta mutu gabaki daya kihuta da wanne zataji? Akanki fa taje tai abinda tayi ran Ammi abace tace banki takaba Baffa amman tarbiyan dana bata kenan, yaushe Amirah takoyi fitsara eh? Kallon Babba tamusu rashin kunya, tama Mahaifinsa tama Mamarsa haba an kace karna maketa, tarbiyan dana bata kenan, mijinki zaki cema kanin mata? Mijinki zaki gayama dan uwansa kikeso yanaga jikinki eh? Sabida kinga yana sonki? Naji dadi ai yanuna miki shi dan halak ne daya sakeki, saikisha zaman gida shashasha kawai, shekara nawa yau kikasan halin ubanki, da baki daya zaki sanar da mijinki abinda ke faruwa zasu magance abin nan bagashi yanzu yana police station ba but you decided to use the foolish way, kinma manya fitsara kin kaso aurenki wacce batasan mutunci ba sanda uban naki yadaukeki yakai asibitin mahaukata ya watsar ko biyar bai ijiyewmb wannan bawan Allah data zaga daga kudinsa Yaya kudin aljihunsa yayi admitting nata all her drugs everything was from his pocket ama samin likita haka a duniya? Ko wannan abun kadai baici ki rangwantamai ki kasa kallon idanunsa ki gayamasa wasu maganganun ba, Marwan fa kudi yada uka yaba Miemie wanda ban mamcewa kudin nayi amfani dasu har na kwaso kaya nazo gidan nan dan banda ko sisi a lokacin the only person daya miki wannan adalcin kikama haka I m so embarrassed ace diyata ce tai wannan abun wlh kuwa, Idan Matar dana tamin kalan abinda Amirah tayi saina cewa dana wannan ba Matar aure bace ita da kai har abada, yanzu ai kin huta ki sha zaman gida zawarci kikeso ko, kin dauka ana auren marasa kai ne Allah ya rufa miki asiri amman ke kin tonama kanki shikenan Baffa ya fizgo Ammi yace keeee yakalli Miemie yace dauki Amirah kuje chan dakin Miemie takama Amirah dake kuka suka fita Baffa yakalli Ammi daya dade baiga matan nan tai fushi hakaba yace yakuri yakuri nasan yanda kikeji yakuri kinji yakuri sai alokacin kukan da Ammi keji tarushe tafashe dashi, Allah sarki ashe idan aka saki diyarka sakin yamafi yima uwa ciwo akan diyar, wlh Lami itama saitahau matsar hawaye taji bala in tausayin Ammi, Baffa yace ya isa, kiyakuri, kimata afuwa, duka duka yaushe tasami lafiyan? Yaushe tai hankalin? Meta sani? Dole ta tafka shirme, ayanda Amirah ke sonki kome akace tayi kanki zatayi eh cikin kuka Ammi tace nasani kawai tacima yaron mutunci dayawa ne maganganun data gayamai baisuyi kama da maganganun mara kan gado urinta ba yanda kasan an zaunar da ta an koyamata, kunyan Marwna nakeji, Baffa Amirah bata kyautaba, I can never excuse action nata koda kashenin akayi, she can simply go kobazata fada musu ga abinda ke faruwa ba tayi demanding sakin batare dataci musu mutunci da fuska ba Baffa yace rashin hankalin kenan, amman ya isa, tayi abinda tayi yanzu ne mu manya zamu gyara kuskuren Alhamdulillah saki dayane, inhar matarsa ce zasu dawo su koma su zauna tare, gobe in sha Allah zamu shirya muje gidansu da safe mu uku mu bada hakurin abinda diyarmu tayi hakan zai nuna munsan me mukeyi, kiyakuri go easy on her kar fushinki ya maidata gidan jiya, correct her kinuna mata ga yanda rayuwa yake, ba a wulakanta masoyi, I m sure by now ita kanta tai nadaman actions nata, dan Allah kibita ahankali kinji, saki ba komi bane face kaddara wacce Allah yarubuta maka zai sameka, wani zubin sai bayan an sami matsala anyi saki ake dawowa a kulla soyayya wacce tafi nada so calm down kinji Sosai Baffa da Lami suka dunga bama Ammi baki har fushin datakeyi yaragu sosai. WAYYYOOO AMMI SAKIN NAN YAMATA CIWO WLH EPISODE 9 Miemie da Lami ne suka kula da Amirah sosai tea kawai ta iya sha Baffa yaje pharmacy yasayo mata magungunan zazzabi tasha takara gashin yamma bayan sallan magrib bacci yakwasheta, taba su Miemie tausayi, tashi Miemie tayi ta tafi dakin Ammi, Ammi na zaune kan dadduma tana lazimi tabita da kallo saida tazo wajen ta zauna ahankali Ammi na kallonta tace yaushe zaki tafi? Ahankali tace bayan magrib Ya Umar yace zaizo muwuce Ammi ta gyadamata kai, suna zaune ahaka har aka kira isha sukai ishai. Washegari still Lami tama Amirah komi tabata breakfast tadanci kadan taji sauki sosai wajen yarage mata ciwo kawai rayuwanta baya mata dadi ne, wuraren 10 suka tafi gidansu Baffa akabar Amirah kawai agidan dan bazasu dade ba. Around karfe goma na safe yasauka a garin Netherlands, fitowa yayi anan airport yasai, using WiFi saiya shiga WhatsApp yaturama Mami message. Mami I just arrived, I wanna remove my SIM card, go off social media for a while, when my mind is calm and settled I will call you Mami, take care yana tura maganan yacire Nigerian sim nasa yasauke WhatsApp Wanda daman shine social media app dayake dashi, wani VIP car yashiga aka wuce dashi lafiyayyen 10star hotel dayayi booking ana tafiyan yana kallon hanya yana tunani, Amirah ce azuciyansa but he s trying yadake ya danna duk sanda zatai popping up azuciyansa saiya danne tunaninta he just want to close her chapter baimaso yadinga tunata balle yadinga tuna mai tace masa that s what is hurting him the most kawai saiyayi alkawarin hakan zaiyi. Har gidan sukakai da tsananin farin ciki Mami ta tarbesu while Abba yashiga turama Alhaji Hamza message kan yazo, zama aka yiyyi Mami tace bari akawo breakfast Mami Lami tace ahh mun koshi Mami tace wlh ban yardaba dasauri tawuce kitchen tana kiran Twins dasuka shiga saukowa sukazo suka gaida kowa na dakin sannan suka wuce kitchen saiga Alhaji Hamza yana sanye da manyan kaya milk color yana baza kamshi da sallama yashigo falon yar zuciyanta Ammi taji muryansa amman taki daga kai, Abba yamike yace bismillah shigo shigo yashigo saiya nunama Baffa Alhaji Hamza yace ga babban aminina Alhaji Hamza, tsohon soja ne toh kukan kirasa da general Baffa yabasa hannu suka gaisa anadan raha sai Alhaji Hamza yajuyo yakalli Ammi wani kallo dabaya boye soyayya yace ina kwana Hajiya, dafatan kin tashi lafiya, ya jikin? Akwai abinda ke miki ciwo? Kowa na dakin saida yajuyo yakalli Alhaji Hamza kunya yasa Ammi takasa ko motsi, tamaki magana saiya kalli Lami yace ina kwana dan Allah tasha magani kuwa lami tawani washe baki tana kallon Ammi dataki magana tace eh tasha Alhamdulillah lafiya kalau duk muka kwana anatse yace diyata fa Amirah? Wani sanyi Ammi taji yanda ya tambayi Amirah, Lami tace itama haka tasha shayi munbarta takoma bacci ma gyadamata kai yayi saiya juya yawuce wajen su Abba yazauna Baffa nadan binsa da kallo saiga abinci an shiga kawowa, Lami tadan matso kusada Ammi cikin muryan gulma tace wannan general yakamu fa Maman Amirah yaushe kuka hadu? Dan dago kanta Ammi tayi ta saci kallonsa tadauke idanu dasauri ita kanta batamasan mesa takejin mutumin aranta ba daga ganinsa jiya. EPISODE 1 The last time wani namiji yataba shiga ranta was 22yrs ago tun mahaifin Amirah, that same feelings takeji yanzu akan Hamza tarasa dalili sake dago idanunta tayi karaf suka hada idanu dasauri ta dauke kai Mami tafito tareda yan aikinta dakuma twins aka jera abinci, waina ce da farfesu sai kunu, da shayi dakuma dumamen tuwo da miyan kuka da man shanu da yaji sai ruwa tace dan Allah ku sauko muyi kari babu Wanda yayi musu, duk aka sauko Hamza kaman zai cinye Ammi da idanu babu wanda bai lura a dakinba imagine Ammi na gidan in-laws dinta amman idanun Hamza yahanata sukuni, dumame taci bada wani yawa ba da kunu mazan ko sunci abinci da kyau, Abba ya warware yasaki jikinsa bai daurama kansa damuwan Saleem ba yashiga coma ance shock ne zai dinga zuwa yana dubasa kullum yabisa da addu a shiyasa kansa in this situation he pray Allah have mercy on him. Gama cin abincin akayi tass akai clearing komi aka zazzauna Baffa yayi guaran murya yace toh Alhamdulillah mungode da wannan karamci, zanso na tambaya ina Marwan saikuma shima Saleem din zanzo duk mugansa kafin afara magana dan gyaran murya Abba yayi yace toh with everything that happened jiya konima nan kafin nakoma gida Yayarsa ke sanar dani Marwan yabar kasan! Abba yadanyi shiruuu sai ahankali yace Ahhhh Marwan wani kalan mutum ne mai hakuri mara fushi, koni baimin sallama ba, I m sure yayarsa ma sabida ita tagansa saisa tasan da tafiyan, yatura mana message ya sauka lafiya amman zai sauke komi na wayansa when he s ready zai kiramu, I know he s just hurting me for now, but nasan waye d ana bazai taba rabuwa da Amirah ba aurensu zai dawo let s give him sometime to cool off jikin kowa na dakin yayi sanyiii, Abba yace akwai something daban fada muku ba, sabida bantaba daukan abin hakaba, Saleem kanina ne uwa daya uba daya, while Marwan kanin matana ne wanda tadaukesa tun yana shekara daya sakamakon hatsari da iyayensu sukayi toh a hannunta yataso, Saleem yataso a dayan matata shi yana shekara uku lokacin mahaifiyar mu tarasu, dukansu na daukesu a matsayin yarana dan a hannuna duk sukai girma, Abba yayi shiru yace dukansu sun taso a hannuna as two opposite yara, while Marwan is a calm, nutsasstsen yaro, Saleem is opposite of that, mata, shayeshaye duddai irin abubuwan nan wanda akasan waje abokan banza duk anan ya koya, daidai gwargwado munyi iyakan kokarin mu amman ba riba, rana daya yaje wajen dan uwansa Marwan a asibiti yaga Amirah a office na Marwan, Allah ya doramasa kaunar ta, for the first time saiya fara kokarin ya chanza ya zama mutum na gari, Abba yadanyi shiru yace mukaje muka nemi aurenta amman kash rannan daurin auren wata ta shagaltar dashi jama a sun taru narasa yanda zaiyi sainasa a daura auren da Marwan tunda nasan shi yarone mai hakuri da kawaici nasan bazai taba kunyatani ba Abba yasake yin shiru sai chan yace bamu gansa ba sai bayan wata daya da auren Marwan ma yaganosa ashe yarinyar dayakebi tamai asiri yaje ya karya tom shine
Chapter 85 · 0% Book details