Sashe 22
Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
running tap ruwan yawani tawarwatsa har fuskan Marwan ya tsareta da idanu ahankali yace wasa da ruwa nace kiyi dasauri tajuyo ta kallesa sai takai hannun data wanke zatasa abaki yace t, clean your mouth goge bakinta tayi, yace wash your hand again wanke hannun tayi, saiya bude kofa yace s go ahankali tafita yafito shima, wani takalmi canvas ne wanda shine general shoes dasuke bama patient nasu fari ya dauko a drawer dakin, sa iya duka ahankali gabanta agaban gadon, Amirah ta kallesa, bude takalmin yayi yace put your leg sa kafanta Amirah tayi saiya samata takalmi da kyau ya kulle igiyan sai kallonsa take kanta trying to put things together, he s just like Ammi, he is her second Ammi sabida yanda yake kula da ita, same thing da dayan kafan yayi ya kulle, yakalli hulanta ya zauna akanta sosai, yace s go saukowa tayi yadan tsaya ya kalleta fully kayan looks free ajikinta sai yajuya kawai yawuce yayi kofa tana biye da shi abaya suka fito, lobby yakaita yau drawing a painting ake koya musu, chair yanuna mata yace zama tayi Malaman na kallonsu da other patients, Malaman takawo mata new board da pen ta ijiye tace here you go anatse Marwan yace I want you to draw anything dakika tuna, stay here I will come back anjima kadan karki biyoni yafada strictly saiya juya binsa Amirah tayi da kallo zuciyanta yashiga rawa sosai har saida tadaina ganinsa sai kawai takifa kanta a table din tai lamo kaman marainiya tareda lumshe idanu. EPISODE 1 Wuraren 1:30PM Saleem yashiga bude idanu shima sabida knocking kofan dakin da Mami tazo tanayi da kanta ne, Saleem maza atashi lokacin sallan zuhur yayi da kyar kaman zaiyi ihu ya juya, sai kawai Mami tashigo dakin labulen windows daki tabude dakin yayi haske abinda baiso kenan yabude idanu yatashi zaune kaman zai mata kuka yace Mamsssss dakuwa Mami tamai tace wuce kaje kayi salla Saleem kafito ina jiranka magana zamuyi dan kallonta yayi kadan saiya tashi ahankali yawuce bayi Mami tawuce tafita daga dakin. Wanka yayi yafito da gangan yakara shiga closet na Marwan yanabin kananun kayansa da kallo, they re to decent for his liking hakanan dai yazaro wani Zara jean blue da farin shirt na H&M yasaka, yadauki p-cap yarike a hannu yafito yana baza kamshi saiya shimfida dadduma yayi salla yawuce gadon yadauki wayansa yana dubawa miss calls ne dayawa kuma duk na abokan sa ne, message din David yaduba a watsapp yace Johnson street yasan abinda abin ke nufi hakan yasa yawuce yafita daga dakin tundaga staircase yake kwalama Mami kira. Mams, Mams Mami dake kitchen tare da masu aiki tace oh ni jama a Saleem gani nan fa fitowa tayi daga kitchen takallesa tace zokai breakfast baiyi musu ba yawuce yazauna kan dinning wayansa na ringing yasa a kunne yana magana Mami na zubamasa abinci, fried rice tasamai da tea da kaji sauke wayan yayi daga kunnensa yace you are the best cook Mams zuwa bayansa Mami tayi kai tsaye yaji hannunta akan kunnuwansa dasauri yakalleta Mami tahararesa tace kace wani abu wlh saina rankwashi kanka bani dan kunnen nan, ko su Faiza naba suna sawa zaka sami lada, these don t belong a kunnenka eh Saleem yanajin nauyin Mami sosai sama da yayan nasa ma, cire an kunnayen tayi takai hannunta ta kwance sarkan shima ta cire kaman zaiyi kuka yace Mamssssss zama kusada shi tayi ta tsaresa da kallo tace Saleem! Kin magana yayi yaturo baki yana jan abincinsa yafara ci, Mami ta tsaresa da kallo, tace Saleem wai bakaga mutuwa ake ba yau mune gobe bamu bane, menene amfanin muna sabama Allah da gangan with the little time we have left? Kayi islamiyya kayi boko, d same school dakayi shi Marwan yayi, amman baka aiki da abinda aka koyar daku a islamiyya, we all love you so much we want the best for you mesa kake haka ? Muryan Mami yadanyi sanyi, saiyadan kalleta yace Mami don t do the sad voice here please just tell me mekikeso ? Shiru Mami tayi tana nazarinsa, all magananganunn data gamayi ko tabasa basuyi ba wlh kawai dan muryan data chanza ne bai so Abinci ma yakeci abinsa, ahankali Mami tace aure nakeso kayi Saleem! Ruwa yakai bakinsa amman saida ya kware yahau tari yana buga kirjinsa yakalli Mami yace wait wat? Mams mene? Aure? Me? Ya yunkura zai mike Mami takamasa ta zaunar tace zauna ban gama magana dakai ba kaman zaiyi kuka mata dan jiransa ake yace Mamii please jirana akeyi fa Mami tace fitanma saina hanaka dasauri yace woh woh woh nooo Mams please my friends are waiting for me Mami tace inaso kafito da mata kai aure kaji Saleem dan dariya yayi yace seriously Mami ? Sai yayi dariya daya lobar da dimples nasa ciki yace Mami I hate marriage aure damuwa ne please banso there s nothing a aure Mami tace okay shikenan zanko bar yayanka ya auro maka kowace mata ne yaga dama zaro idanu Saleem yayi yace wat? Mams what s going on ? Cikeda hikima Mami tace yayanka yace zai samo kowa yaga dama yamaka aure, it took me the whole night to convince him karya maka haka ya banni nizan maka magana kafito da wacce kakeso da kanka dan zaman n nan ba a yima yaro auren dole saisa na kiraka ina maka maganan amman tunda nima baka daukeni serious ba zan barsa yamaka kome yaga dama dasauri Saleem yace no no nooo Mams please, you know how that old man can be trouble ni zaije ya zaboma mata yanda yake jik haushin nan nawama ai wata chan zai dauko a kauye ya auromin Mami tace ashe kasan yayanka dan shiru Saleem yayi yarasa mezaice, Mami ahankali tace baka da budurwa duk yammatan ka Saleem wata yar dariyan iskanci yayi Mami batasan tsakaninsa da su ci bane kawai yace banda shi Mami tace to kafara nema zan rokesa na lallabasa yabaka nan da one month Shiru yayi baitaba sanin zancen aure can make kansa yaji yayi so blank ba sai kawai ya gyadama Mami kai daidai ana sake kiransa yamike da sauri yace bye Mami I m taking your car keys yadauki key motanta yafice harda dan gudu Mami tabisa sa kallo tana karamai addu an shiriya. Motan Mami yashiga duk iskancinsa hakanan yana tsoron Abba yayomai aure dan yasan karamin aikin yayansa ne wlh ayanda yakejin haushin nan nasa, shi kawai akyalesa abarsa yayi rayuwansa abinsa, taka motan yayi da gudu dan sauri yake he needs to make a quick stop before yaje wajensu David Takai kusan 30min ahaka sai tadago ta kalli paper drawing din, saiya dauki pencil tashiga zane, tanatayi ita kadai, Malaman su ne tazo wajen ta tsaya takalli abinda Amirah ke zanawa saitai jim saita wuce cus zata iyama Amirah magana taki cigaba, chan saiga Marwan yataho wajen, kamshinsa kawai Amirah taji saita dakatar da abinda takeyi takai pencil din ahankali bakinta batare data dago kanta ba, kirjinta sai bugawa yake, tahowa yayi wajen kai tsaye yasa hannu yadauki paper datai zane aciki yakai one minute yana kallon abinda ta zana saiya nannade yarike a hannu yace s go dasauri Amirah ta tashi sai yayi gaba tana binsa abaya da sauri kanta akasa da pencil da hannu duka abakinta tana binsa yabude office nasa yajuyo kalleta yace shiga ki zauna ki jirani shiga tayi ahankali ta tsaya yace zauna zama tayi sannan yakulle kofan yawuce Saleem bai tsaya ko inaba sai hospital din su Marwan yawuce yayi parking yanadan gajeren tsaki cus he hates coming to the hospital it always remind him of sanda Babansu ya rasu he dies in the hospital, parking yayi yaciro wayansa yanabin wakan dake tashi a motan na Akon yayi dialing number Marwan yanasa wayan a speaker amman harta gama ringing bai dagaba he knew this might happen sai kawai ya kashe wakan yabude motan yafito yawuce ciki yana zuba kamshi yashiga cikin psychiatric ward din yana tafiya da dan sauri, yawanci nurses ne wajen direct hanyar office na Marwan yayi kai tsaye yabude office din yashiga yana maida kofan yarufe daidai yaji ana rike masa gefen riga gam dawani irin sauri yajuyo yakalli side nasa adan firgice, Amirah ce gefen kofan kanta akasa hannayenta na baki da pencil dayan hannun kuma ta rike masa gefen rigansa dashi, ga pink lips dinta dake motsi sosai tana kallon kasa, at first ya bala in tsorata daga shigansa office out of nowhere wata tarike masa riga saura kadan yayi ihu cus yadauka aljana ce, but sai baiyiba ya tsare fuskanta da kallo especially long eye lashes nata dasuke nan kaman tai fixing da giranta dayake aciki dan idanunta na kasa da pink lips nata dan karami irin na jarirai, ga gashi a goshinta a kwance lublub kaman buzuwa, dan dukawa Saleem yayi yawani leka fuskan Amirah daidai tana tauna fingers nata suka hada idanu, idanuwanta kaman an wanke da madara sabida tsabagen haske baisan sanda gabansa yawani kalan fadi ba rassss! Amirah tadan dakatar da bitting fingers dinta datakeyi ganin fuskan wani daban daba Dr ba but he smells exactly like him dan turaren Marwan Saleem yasaka yafito abinsa, ahankali tasaki gefen rigansa while Saleem cikin wannan care free attitude din nasa yamata wani irin murmushi dayasa dimples dinsa suka lotsa sosai so deep yace Hi, Hey, Hello Pretty! Runtse idanunta Amirah tayi da sauri gabanta na faduwa muryansa zaki and so husky saita shiga komawa baya idanunta a kulle ganin wanda bata saniba at all, daidai ana bude kofan office din dawani irin sauri akuma tsorace Amirah ta juyo tana bude idanunta Marwan ne ya shigo da lab coat a jikinsa stethoscope a hannunsa dan wani patient dake having seizure yaje yaduba, ganin Saleem a office nasa yana kallon Amirah da batada wani tazara dashi sosai saiya tsaya chak itakuma Amirah data rude saitayo kansa kaman zata fado kansa looking confuse, cikin very harsh tone ganin zata shiga jikinsa yace Tsayawa Amirah tayi chak amman dab dashi har iskan numfashin datakeyi yanaji akan fuskansa, hannunta daya na bakinta saitakai na biyun shima tasa a duka bakinta tana taunawa nervously, Saleem dake binta da kallo bayako kyafta idanu yace wowwwww!