Sashe 6
Baccin So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zaizo by 9, ance musai kati achan 5k jakanta Ammi tabata tace ciro kudi kije ki saya 5k Miemie taciro tawuce tabiya tasayo sune number 21 tadawo rike da number, akwai different consultation rooms awajen kusan guda 10, it s all depends on Dr da akai booking dinka zaka gani cus wasu nata shiga ana jiransu sunesai shiru har yanzu. Suna zaune awajen har 10 Dr baizoba jikin Amirah zafi gadan gadan abin haryasa tafara making some wired sounds, gashi tahana Ammi ko motsi dan batason mutane ta chukuikuye Ammi kaman zata koma cikinta. Wuraren 10 wani arnen mota 2025 Tesla dark blue yayi parking awani parking space da musamman akasa UNICEF PHYSICIANS gawasu special securities dake gadin wajen, security ne yazo dasauri yabude masa kofa yana murmushi sosai yace welcome Dr M wani caramel skin color guy ne da zaka iya kiran kalan fatansa fari but ba fari bane and bazaka taba iya kiransa black ba cus he s not, zaune yana sanye da riga da wando dark brown na Ralph Lauren dasukamai wani irin kyau abinka da mai dan hasken fata, yanada saje mai yawa dake a kwance dayazo har gemunsa duka a kwance sai pink lips that her full and meaty irin asalin real masculine mouth garesa that s damn sexy, idanunsa na cikin white glasses wanda madubin jiki are very thick kana gani kasan yanada asalin matsalan idanu cus at a glance zakasan glasses din are medicated, dan ijiyan zuciya yasauke he hates Sundays cus outpatient department is stressful her prefers working a inpatient ward, yanada dogon hanci da gira baki cikake, Ya Allah he s damn cute and skin dinsa is so fresh. Ahankali yafito daga motan yana kallon agogon hannunsa, yanada tsayi da kuma full jiki na d a namiji kakkarfa kuma kosasshe, security yace barka da zuwa Dr gyadamai kai yayi yana janye idanunsa dagakan agogon yabasa car key ahankali, security yayi murmushi, Dr yawuce yana tafiya a nutse, security yashiga motan yayi parking properly sannan yadauki wasu files dake dayan seat din da aka rubuta confidential akai, da sethoscope, saikuma labcoat dinsa da wajen Aljihun akwai rubutun UNESCO Dr Marwan, yafito yamaida kofan yarufe sannan yashiga tafiya dasauri, yana shiga cikin asibitin babban Nurse din tace Dr Marwan yazo? Gyadamata kai security yayi Nurse din tace start coming here according to your number for your vitals, Dr ku yazo tanuna 5rows of chairs wanda harda nasu Ammi cus sune Dr Marwan zai gani. EPISODE 4 Nurse din tawuce tazauna tana shouting number 1 Ahankali security yabude office din ya shiga babu kowa a office din, ba datti dudda wannan is just office dayake shiga every Sunday dan ganin outpatient amman dudda haka office din kamshin sa yake, asalin permanent office dinshi yana cikin physiatrics ward, ijiye komi yayi a inda yakamata, office din yayi kyau kaman ba office na asibitin gwamnati ba ga kujera da table mai kyau ga gadon duba patient gakuma another doors guda biyu wanda daya bathroom ne dayan kuma another door ne na shigowa ciki from outside, yana makala labcoat nasa a hanger aka bude dayan door din security yadago kansa kafin ya shigo har kamshin sa yashigo, anatse yashigo cikin office din yabi ko ina da kallo cus idan yaga datti daya ko kura consultation din dabazaiyi kenan ba yau, ahankali yakaraso wajen hanger security ya matsa masa, hannu yasa yadauki lab coat yana sakawa, security yajuya zai fita batare daya dago kansa ba yana saka boturan rigan cikin muryansa datake murdadda a bit hard, subtle, but still yana nuna masculinity nasa yace ya jikin Mama ? Dasauri yajuyo saiyayi murmushi sosai yace taji sauki sosai kaman ba itaba tace na gaidaka still har lokacin baice komiba sai security ya tsaya yana kallonsa. Any problem with the job ? Dasauri yace no no no, wlh inason aikin nan bazan taba mance alkhairin dakamin b tell the nurse I m seeing 15 patients today I need to be somewhere ya yanke maganan sa cus bayason godiya kwata kwata shi haka yake, dasauri Security yace angama Dr yabude kofa zai fita kaman daga sama ahankali Dr Marwan yace be good Kamal dan jimm yayi saiya juyo yakallesa yaga harya zauna yabude files dayazo dashi, murmushi yayi yace I promise Ya Marwan yabude kofan yafita, Nurse ta kallesa yadan matso sAbida kar patient suji yace yace 15 patients zai gani yau dasauri Nurse takalli wajen gabaki daya patients sunfi 30 wanda suke nasa ba abun ta aikasu wajen wani likita ba cus duk masu matsalan kai ne shine likitan su, inhar bai gansu ba saidai su kara dawowa nextweek Sunday, cikeda takaici tace wlh Dr Marwan sai ahankali sabida yasan abinda yakeyi ne yake yanga haka haba dan Allah, bayan an gama jiransa sai yanzu yake zuwa, kuma yace patients kadan zai gani tai maganan tana kallom jama an tace number one go inside tamike itama tana deban files na patient 15 dayace zai gani ta shiga office din tafito. Ammi duk suna zaune awajen suna kallon kofan office na likitan, Miemie takalli Ammi data damu sosai tace Ammi kallonta Ammi tayi sai ahankali tace bakijin yunwa akwai biscuit ajakana kici murmushi Miemie tayi tace banajin yunwa Ammi kusan 10min number one yadauka yafito nabiyu yashiga duk suna zaune awajen patient number 15 yashiga, lokacin kusan 12:20 Nurse din tamike tazo gaban kujerun su ta tsaya tace ahhhm Dr nada emergency please bazai iya dubaku ba saidai ku dawo next week Sunday wajen ya kaceme da hayaniya kaman za a daki Nurse, ran Miemie yayi matsanancin baci wlh, tace wlh asibitin gwamnati baiyiba ba Ammi especially idan suna dan rage muku kudi ayita muku wulakanci ahankali Ammi data fara tunanin yanda zatayi Amirah taga likita dan jikinta sai uban zafi yake tace Miemie rikemin Amirah ina zuwa, taciro Amirah daga jikinta dako bude idanunta bata iyayi tsabagen zazzabi, Miemie tariketa da sauri Ammi tamike ta tashi dagakan kujeran, one thing is dazaran ba ajikin Ammi takeba tasani, bude idanunta Amirah tashiga yi kadan daidai Ammi takarasa mikewa, azabure tawani yunkuro ta mika hannu zata kama hijabin Ammi tareda kurma wani mugun ihu da saida duka wajen da ake hayaniya kaman za ayi fada yadauka jikake tsit! Kowa yayi shiru! Daidai Marwan yasa hannu zai bude kofa yafita yaji ihu that s very sharp mai ratsa jiki hakan yasa ya tsaya chak, saiya juyo yadubi kofan wajen da patients suke anatse yana duba agogon hannunsa. Dasauri Ammi tajuyo tariketa tace Amirah, ganinan Amirah wani irin numfashi Amirah takeyi kaman zata shide batada one single karfi, Nurse tabar masu rigima da ita tazo wajen su Ammi dasauri hannunta takai ta taba goshin Amirah wanda Ammi da Miemie suka rike saida ta tsorata jin zafin da jikinta yake tace ina zuwa Hajiya ku riketa da kyau saita mike dasauri tawuce office din tai knocking tareda bude kofan, tsaye ta gansa dab da kofan kafin tai magana yace who scream like that? Dasauri tace wata yarinya ce Dr, her condition is really bad, dan Allah kadubata Dr, wlh Mamanta tabani tausayi, yarinyar is running temperature and I think she s non verbal cus Maman and the sister do most of the talking dan shiru Dr Marwan yayi sai yasake kallon agogon sa yace okay dasauri nurse din tawuce tafita tazo wajen Ammi tace kuje ciki mikewa Ammi tayi Amirah ta chukuikuyeta gabaki daya fuskanta na kirjin Ammi ahaka Ammi ke tafiya da ita, Nurse takarbi card dinta daga hannun Miemie tawuce ta dauki folder su tawuce, Ammi tabude kofan ta shiga nurse biye dasu abaya. EPISODE 5 Amirah na sa kafanta office din wani irin sanyi taji akirjinta da kawai saiya koma tare ta tsaya chak tahau tari akirjin Ammi. Rubuce rubuce Marwan yake, yanda Amirah tahau tari yasa anutse yadago kansa yadaura akansu, he can t see the girls face d only thing daya iya gani her fararen white legs nata dake cikin crocs pink bawai masu tsada bane but yanayin yar kafan nata made the crocs looks so damn expensive, saikuma hannayenta suma farare kal masu dogayen yatsu da dogayen kumba dasuke a yanke farare tass ta damdamke hijabin mahaifiyarta dake bubbuga bayanta sabida tarin datakeyi, janye idanunsa yayi daga kansu yakalli nurse data kawo file nata table nasa yace give her water yanuna fridge dake office din nurse tace tajuyo tanuna ma Ammi waje kan gadon duba patient na office din tace kaita ta zauna anan bari na baki ruwa kibata tafiya Ammi tashigayi da Amirah tace muje mu zauna Amirah nurse tabude fridge taciro bottle water takawo musu tana budema Ammi, Ammi ta karba tace nagode nurse Ammi taciro kanta daga kirjinta ahankali tace yauwa Amirah naa ga ruwa to kisha tarin ya tsaya dago kanta Ammi tayi daidai lokacin Marwan dake duba folder nata yasake dago kansa ya kallosu hakanan bugawa kirjinsa yayi, hannu Amirah tasa ta tura hannun Ammi da ruwa alamun bazata sha ba kamar yar baby tasake komar da kanta tai placing a kirjin Ammi tana tarin still amman kadan kadan yaragu, Ammi takalli Marwan dake kallonsu tace bazata sha ruwan ba tun jiya rabonta dasa wani abu abakinta hijabin Ammi yabi da kallo daga sama har kasa duk alamun dakuna saikuma ya tsare fuskan Ammi da kallo na few seconds kafin yadauke kansa maida kan folder dinta yana karancewa A hospital dinnan aka haifeta 2004, 1st August, sunanta Aminatu Adamu, tana around 6yrs suka dawo asibiti Mamanta takawota kan bata magana, taje school bata karatu bata rubutu, she s scared of mutane, she s clingy to mamanta, duk inda Mamanta taje saita bita hatta bayi, bata iya bacci ba Mamanta, bata displaying emotions, the mother complain kan bata gane sanda yarta is happy ko is sad ko is hurt, kotai cracking jokes yarinyar doesn t smile, taji ciwo hardly take kuka ko fuskanta yanuna wani abu saidai taita zufa kotai ta kallon wajen dataji ciwon, idan zataga wani yaji ciwo ko wani abu bazakaga alamun tausayi ba akan fuskanta, saiyaga likitan dasuka gani alokacin yasa yarinyar nada Autism as diagnosis dasauri yakalli sunan Dr sabida yanda yaji ransa yabaci aka bata drugs, tundaga wajen sukanzo asibiti amman gabaki daya akan autism ake mata treatment da